2025-06-15@09:45:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1167
«Kungiyar da ta fi»:
Sannan shi ne ya fi kowanne danwasa yunkurin cin kwallo a gasar, inda ya kai hari (attempt) sau 64, 23 daga cikinsu akwai munana (on target) 23. Ya yi nasarar yanka abokan hamayyarsa har sau 62, sannan ya yi bugun kwana 45. Rapinha Zakakurin danwasan gaba na Barcelona da Brazil, Rapinha, na cikin ‘yanwasan da suka fi bai wa mabiya harkokin wasa mamaki a kakar wasa ta bana baki daya – ba a Champions League ba kawai. Tare da dan wasan kungiyar Borussia Dortmund, Serhou Guirassy, su ne kan gaba a cin mafi yawan kwallaye da 13 kowannensu. Sai dai Rapinha ya zarta shi da yawan bayar da kwallo a zira a raga, inda yake da guda 9, Guirassy...
Wakilin dindindin na kasar Sin a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ko IAEA Li Song, ya ce kasarsa na matukar Allah wadai da harin Isra’ila kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran da ake amfani da su domin ayyukan zaman lafiya. Li Song, ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a, yayin taron manyan jami’an majalisar gudanarwar hukumar ta IAEA, game da batun hare-haren da Isra’ila ta kaddamar kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar Iran. Ya ce, har kullum Sin na mayar da hankali ga zakulo matakan wanzar da zaman lafiya, dangane da batun nukiliyar Iran ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya, tana kuma adawa da kakaba takunkumai ba bisa ka’ida ba daga bangare guda. Har ila yau, Sin za ta ci gaba da...

Za A Watsa Shirin “Bayanan Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Kafofin Watsa Shirye-shiryen Kasashen Tsakiyar Asiya Biyar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Gamsuwa Da Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Yayin da taro na biyu na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya ke kara matsowa, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, sun nuna gamsuwa da hadin gwiwa bisa matsayin koli dake tsakanin Sin da kasashen nan biyar na yankin tsakiyar Asiya, a matsayin wata hadaka ta al’umma mai kyakkyawar makomar bil’Adama, wadda ke kara shigar da sabon kuzari, na daidaito cikin yanayin duniya dake kara shiga yanayin tangal-tangal. Tun dai taro na farko na tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen biyar ya shiga wani sabon zango na ci gaba. Har ma kuri’un na jin ra’ayin jama’a suka nuna yadda kaso 90.4...
Hukumar Kula da Yanayi (NiMet), ta sake fitar da gargaɗi game da yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin a daminar bana. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta bayyana cewa Jihar Akwa Ibom ce ke fuskantar barazana mafi tsanani a halin yanzu. Gwamnan Kaduna ya bai wa sabon Sarkin Moro’a sandar mulki Farashin fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin Isra’ila a Iran Sauran jihohin da abin ka iya shafa sun haɗa da Sakkwato, Zamfara, Filato, Yobe, Bauchi, Bayelsa, Nasarawa, Binuwai, Ogun, Ekiti, Delta da kuma Ribas. NiMet ta shawarci al’umma, musamman waɗanda ke zaune a cikin waɗannan jihohin, da su tabbatar sun yashe magudanan ruwa domin bai wa ruwa hanyar wucewa. Haka kuma...
Aƙalla Mutane biyar sun kwanta dama wasu huɗu kuma sun jiggata sakamakon tsinkewar igiyar lantarki bayan dawo da wutar lantarkin mai ƙarfi a unguwar Tudun Wadan Pantami, ta jihar Gombe. Kamar yadda wani mazaunin yankin Adamu Abubakar Kulani, ya shaidawa manema labarai, mummunan lamarin ya faru ne a daren ranar Juma’a yayin da aka kawo wutar lantarkin bayan sun kwashe kwanaki babu ita. Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Lura Da Yanayin Bala’u Muhimmanci, Tasiri Da Kuma Amfanin Jigida Ga Mata Ya ƙara da cewa sanadiyar wutar ta zo da ƙarfi ne ta haifar da tartsatsi, kana ta tsinka igiyar babban layin lantarkin wanda ta faɗa kan mutanen. Tuni jama’ar yankin aka garzaya da waɗanda suka jiggata Baban Asibitin...
Ba tare da saninmu ba, yawancin al’ummar Afirka musamman ma naYammacin Afirka suna fama da abinda ake kira da suna irin hali ko yanayin da aka shiga sanadiyar lamarin cinikin Bayi.Bayan shekara 100 da aka yi daga shekarar 1801 zuwa 1901, an yi wani kokarin da ake yi ma kallon tamkar wani takune na yadda za’a kubuta daga irin cin fuskar da ake yi kowace rana. Kafin dai a tsunduma sosai cikin lamarin cinikin Bayi, yana da matukar kyau a fara yin bayani kan yadda abin ya fara:Lamarin cinikin Bayi ba manufa bace ta Yammacin Turai.Duk lamarin ya zarce wani hasashen da za’a iya yi ko wani rubutun,da aka yi aka aje.Idan kuma aka duba ta bangaren nahiyar Afirka ita...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bude kofofin wuta a kan haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar mayar da martani kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasarta Iran ta bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya a matsayin mayar da martani ga mummunan zaluncin da suka kaddamar kan lardunan Iran da dama, wanda ya yi sanadiyyar shahadan mutane da dama da jikkata. Bayan da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Wajibi ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta jira mummunan hukunci mai tsanani da kuma makoma mai daci kan abin da aikata, kuma bayan da sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci Manjo Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran za su bude kofofin...
Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kakkausan martanin da Iran ta mayar ya tabbatar da cewa babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani ba Izzat al-Rishq mamba na ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya jaddada cewa: Kakkausan martanin da Iraniyawa suka mayar ya tabbatar da cewa; babu mai girman kai da ba zai fuskanci mayar da martani kan zaluncinsa ba, kuma babu wuce gona da iri ba tare da hukunci ba. Izzat al-Rishq ya yi nuni da cewa: Tabbas makamai masu linzami da jiragen saman yaki marasa matuka ciki na Iran sun yi nasarar kai wa cikin tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila, duk kuwa da kace-nacen da ake yi na girke na’urorin kakkabo makamai...

Taron Koli Na Sin Da Kasashen Yankin Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu Zai Ingiza Manufar Kara Dunkulewar Sassan Yankin
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi karin haske game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta a Kazakhstan, yana mai cewa, Sin na da yakininta hanyar taro, ita da sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya biyar, za su zurfafa dunkulewa, da amincewa da juna, da gina matsaya guda ta fuskar hadin gwiwa, da zurfafa daidaiton dabarun ci gaba, da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da kara kuzarin gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya. Bisa gayyatar da shugaban jamhuriyar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na...
Babu abin da ya rage yanzu, illa babatun zantukan siyasa da ‘yan siyasar ke ta fama yi a kasar, wadanda suka jarabtu da matukar son mulki. Wannan abu da ke faruwa yanzu, ko shakka babu zai canja, zai canja din ne kuwa yayin da ‘yan siyasar ke aiwatar da tsare-tsarensu, sai masu jefa kuri’u a Nijeriya kuma su yanke hukunci. Shekarar 2027, za ta kasance mai ban mamaki tare da kalubale ga ‘yan Nijeriya. A bisa dukkan alamu, jam’iyyar APC ta dukufa wajen kara habaka karfinta ne kawai da ganimar ‘yan adawa. Tana ta faman sa kanta cikin rigingimu, har wadanda ba su shafe ta ba a cikin shekaru biyun da ya rage mata ta yi gaba na kunci da...
Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki. Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban. Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki. “Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya. “Martabar...
A sandiyyar harin da ‘yan sahayoniya su ka kawo wa Iran da asubahin yau, masana fasaahr Nukiliya da dama sun yi shahada. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambaci cewa: Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran; Faridun Abbasi. Shugaban jami’ar Azad, Muhammad Mahdi Dahranji. Shugaban Kwalejin fasahar Nukiliya, Abdulhamid Minochehri. Hakan nan kuma Malamin fasahar Nukiliya Ahmda Riza Zulfiqar, sai mataimakin shugaban hukumar makamashin Nukiliya Amir Husain Fiqhi.
Kwamandan sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa da asubahin yau Juma’a. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar Amir Ali Haji Zadeh.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi da wani dalili da ya wuce a rufe bakin gaskiya wanda yake taimakawa al’ummar Falasdinu a Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, haka nan kuma taimakawa da goyon bayan gwgawarmayar Lebanon da dukkanin wannan yankin. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Wannan harin da wuce gona da irin za iyi tasiri mai girma a cikin wannan yankin, sannan ya kara...
Sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgadiya Muhammad Pakphur ya aike wa da jagoran juyin musulunci na Iran wasika da a ciki ya bayyana cewa: ” Laifukan ta’addanci da HKI ta aikata, wanda ya yi sanadiyyar shahadar manyan kwamandojin da kuma malaman Nukiliya, haka nan mata da kananan yara da ba su ji ba su gani ba, ba zai wuce ba tare da mayar da martani ba.” Bugu da kari sabon kwamandan dakarun kare juyin musuluncin ya ce; Ba da jimawa ba, Za a buwa wa wannan haramtacciyar kasa kofofin jahannama.” Birgeriya Muhamad Pakphur ya kuma kaddamar da ta’aziyya da kuma taya murnar shahadar kwamandojin, ya kuma yi godiya ga jagora da ya gaskata dakarun juyin....
Rundunar ’yan sandan ƙasar Australia ta kama wata ’yar asalin Najeriya da ke ƙasar Australia, Binta Abubakar bisa zarginta da safarar ɗalibai daga ƙasar Papua New Guinea tare da tilasta musu yin aikin da ba a biya a gonaki a faɗin jihar Ƙueensland da sunan bayar da tallafin karatu. Binta mai shekara 56, an kama ta ne a ranar Laraba a filin jirgin saman Brisbane a lokacin da ta isa ƙasar Papua New Guinea, inda take zaune. Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi Kamen nata ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ƙungiyar masu fataucin bil-Adama ta AFP ta...
Gabanin tafiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping birnin Astana na kasar Kazakhstan, inda zai halarci taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, an kaddamar da bikin gabatar da jerin shirye-shiryen shirye-shiryen telebijin da fina-finai, na babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG na shekarar 2025 a birnin Astana. Za a gabatar da shirye-shiryen CMG guda 12, ciki har da alakar dake tsakanin shugaba Xi Jinping da al’adun kasar Sin, da hanyar zamanintar da kasa mai salon kasar Sin na musamman da sauransu, a manyan kafofin watsa labaru na kasashen Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan, da Uzbekistan da dai sauransu. Shugaban gidan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, a ta bakin...
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matsayin cin ribar cikakkiyar dimokuraɗiyya ba, duk da cewa an dawo mulkin farar hula shekaru 26 da suka gabata. Yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, Fayemi ya bayyana cewa duk da cewa ana gudanar da zaɓe a kai a kai a ƙasar, har yanzu an rasa muhimman abubuwan da suka kamata su kasance a tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna “Bai kamata mu rikita gudanar da zaɓe da aiwatar da dimokuraɗiyya ba,” in ji shi. “Abin da muka...
Bayan harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai kasarmu, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sako ga al’ummar Iran. Ga sakon kamar haka Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai Al’ummar Iran masu daraja! Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta hanyar aikata wani laifi da sanyin safiyar yau, ta sake bayyana munanan dabi’arta da fasadi. Ta hanyar kai hari dole ne wannan ya fuskanci hukunci mai tsanani. A wannan harin makiya, kwamandoji da masana kimiyya da dama sun yi shahada. Wadanda suka gaje su kuma da abokan aikinsu za su ci gaba da aiki nan take akan wannan tafarki, godiya ta tabbata ga Allah. Ta hanyar wannan danyen aiki, gwamnatin Sahayoniya ta kaddara akan ta cewa...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada. Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar. “Hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran sun sabawa doka ta 4 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya a matsayin wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma Iran tana da hakki na shari’a na halal ta mayar da martani kan wannan zalunci kamar yadda yake a cikin sashe na 51 na kundin tsarin mulkin majalisar...
Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray a wannan Alhamis din ta sanar da daukar dan wasan Jamus, Leroy Sane daga Bayern Munich. Kungiyar ta Turkiyya ta dauki dan wasan ne kyauta bayan kwantaraginsa ya kare a Munich. Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu Ƙwazo da juriya suka sa na zura ƙwallaye 10 a wasanni 10 – Mane Sane mai shekaru 29 ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru uku inda zai rika daukar albashin Yuro miliyan 9 — kwantankwacin Dala miliyan 10.4 — duk shekara kamar yadda kulob din bayyana. Sane ya buga wa kasarsa ta Jamus wasanni 70, inda kuma ya lashe kofunan Bundesliga guda hudu a Bayern Munich tun bayan raba gari da Manchester...
A yau Alhamis ne aka bude bikin baje kolin hada-hadar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan, taron dake kara jaddada himmar kasar Sin ta fuskar karfafa alaka da nahiyar Afirka, nahiyar dake da mafiya yawan kasashe masu tasowa a duniya baki daya. Kusan kamfanonin Sin da na kasashen Afirka 4,700, da sama da mahalarta 30,000 ne za su halarci bikin na kwanaki hudu, wanda aka yiwa taken “Sin da Afirka: Tunkarar zamanantarwa tare.” Rahotanni daga mashirya bikin na cewa, kwarya-kwaryar darajar ayyukan hadin gwiwa da aka amincewa sun haura dalar Amurka biliyan 11. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin bude baje kolin, inda kuma...
Majiyar tsaron kasar ta Kamaru sanar da cewa, da dama daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da kungiyar Bokoharam ta kai musu ta hanyar amfani da manyan bindigogi da kuma jirgin sama maras matuki akan iyaka da Najeriya. Majiyar ta ce an kai harin ne a yankin Sagami dake kusa da tafkin Chadi a gundumar Logun mai iyaka da kasar Najeriya. Ita dai kungiyar Bokoharam ta addabi kasashen Najeriya, Kamaru da kuma jamhuriyar Nijar. Yankun arewacin kasar ta Kamaru ya fara fuskantar kai hare-hare daga wannan kungiyar ne tun a 2014 wanda kuma har yanzu yana ci gaba da faruwa daga lokaci zuwa lokaci.
Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a yankin Cape ya fada a jiya Laraba cewa; An sami karuwar wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 49. Shugaban tafiyar da sha’anin Mulki a yankin na garin Cape, Oscar Mobyan ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto. Wasu yankuna na kasar ta Afirka Ta Kudu sun fuskanci saukar ruwa kamar da bakin kwarya, haka nan kuma saukar kankara, da hakan ya sa aka shiga cikin yanayin sanyi mai tsanani da kuma yankewar wutar lantarki a wasu yankunan. Ambaliyar ruwan da aka samu a kusa da wata makaranta ya ja motar da take dauke da dalibai 13, da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Tuni...
JMI ta bayyana cewa zata yi amafani da hakkinta wanda doka ya bata na ficewa daga yarjeniyar NPT don sake farfado da takunkuman tattalin arziki na MDD a kan kasar. Jakadan kasar Iran a MDD, Amir Saeid Iravani ne ya bayyana haka a jiya Laraba. Kamfanin dillanbcin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a wata wasika da ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD a jiya. Ya kuma kara da cewa Iran zata yi amfani da dokokin da suka bada damar yin hakan. Kasashen Turai guda Uku jamusa Farana da Burtania suna son su yi amfani da damar da ake kira snap back don sake farfado da takunkuman MDD a kan kasar na yarjeniyar JCPOA. Ya...
Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da ke kawo karshen zaman tankiyar da aka soma tsakanin kasashen biyu tun bayan hawan Donald Trump karagar mulki. Kasashen biyu sun cimma matsaya a kan kan cinikin wani rukini na ma’adinai da Chinar ke fitarwa, wadanda ake kira da sunan Terres Rares, wadanda ake yi amfani da shi wajen samar da lantarki da kuma makamashin da ake sabbintawa. An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m A baya a taron kasar Switzerland, Washington ta amince da rage haraji kan kayayyakin kasar China daga kashi 145 zuwa kashi 30 cikin 100, don musanya makamancin wannan mataki da Beijing ta...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sake kunna ‘hanyar tayar da hankali’ zai gamu da martani mai ƙarfi na Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Fitar da kudiri kan Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta yi ba zai shafi kudurin al’ummar Iran ba ko kuma ci gaban shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Iran a yammacin ranar Talata, Baqa’i ya yi la’akari da dukkanin rahotanni da kudurorin da suka shafi siyasa. Ya kuma kara da cewa Iran ba ta keta hurumin da ya rataya a wuyanta ba, kuma kasashen yammacin turai suna dora barazanarsu ne kan...

He Lifeng Ya Bukaci Amurka Da Ta Warware Takaddamar Cinikayya Da Sin Ta Hanyar Tattaunawa Da Hadin Gwiwa
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari. He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin...
Ana zargin wata mata mai suna Khadija kan zargin kashe ’yarta mai shekaru 11, Fadila, saboda Naira 100 da ta samu a yawon Sallah a unguwar Tukur Tukur da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, inda lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a unguwar har maƙwabta suka ƙi yi wa gawar yarinyar sallah saboda tsoron abin da zai biyo baya. Ranar Dimokuraɗiyya: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Wasu maƙwabta sun bayyana cewa Khadija ta doke Fadila da taɓarya ne saboda ta zargi yarinyar da satar Naira 100. Sun ce irin wannan ɗabi’a na duka da tsangwama...
Cherki ya buga wasansa na farko a Lyon yana da shekara 16 a watan Oktoban 2019 kuma ya bar kungiyar inda ya ci kwallaye 29 sannan ya taimaka aka jefa 45 a wasanni 185 da ya bugawa kungiyar ta Faransa. Cherki ya wakilci kasar Faransa kuma ya lashe lambar azurfa a gasar Olympics da aka gudanar a birnin Paris na kasar Faransa a bara. Daraktan kwallon kafa na Manchester City, Hugo Viana ya ce, “Babu shakka a yanzu Cherki yazo inda ya dace kuma zai cigaba a karkashin jagorancin Guardiola, kuma na yi imani zai iya zama babban dan wasa a duniya tare da goyon bayan abokan wasa da masu horarwa”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Neja kan mummunar barnar da ambaliyar ruwan ta yi, na salwantar da rayuka da barnata dukiya da dama. Gwamna Umar Bago na jihar Neja, ya yabawa takwaransa na Borno bisa wannan ziyarar da kuma bayar da gudunmawar, inda ya ce lokaci ya yi da za a nuna soyayya ga juna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iran ta ce za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a Muscat, babban birnin kasar Oman. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai a wata sanarwa da ya fitar ya ce “An shirya zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Muscat.” Tun a watan Afrilu, Tehran da Washington ke gudanar da shawarwarin kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. An yi shawarwari guda uku a tsakanin kasashen biyu a birnin Muscat, yayin da sauran biyun suka gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Tehran da Washington sun gudanar da wadannan zagaye biyar na shawarwarin a shiga tsakanin kasar Oman, kan batun maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar...
Gidauniyar Hind Rajab (HRF), mai rajin kare hakkin Falasdinawa, ta shigar da kara kan laifukan yaki bayan farmakin da sojojin ruwan Isra’ila suka kai kan jirgin ruwan agaji na Birtaniya Madleen a ruwan kasa da kasa a yammacin Lahadi. Koken dai ya shafi rundunar sojin ruwa ta Isra’ila Shaytet 13 da kwamandan ta, Vice Admiral David Saar Salama. Gidauniyar ta HRF ta yi kira da a gaggauta sakin masu fafutuka 12 da ake tsare da su, ciki har da mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg, dan wasan kwaikwayo Liam Cunningham, da Rima Hassan ta faransa, wadanda ke hannun Isra’ila. Jirgin ruwan na Madleen, na kungiyar Freedom Flotilla Coalition, na dauke da kayayyakin jinya, da abinci, da madarar jarirai, da sauran...
Iran ta bayyana cewa: Tace sinadarin Uranium wani bangare ne na bunkasa masana’antar nukiliya kuma ba zata amince kan tattaunawa ko yin sulhu kansa ba Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Sarrafa sinadarin Uranium wani bangare ne na masana’antar nukiliya, kuma batu ne da ba za a tattaunawa kansa ko yin sulhu kansa ba, kasancewarsa masana’antar cikin gida ne kuma an shefe tsawon shekaru da dama ana sarrafa shi a cikin kasa, sakamakon kokarin da masana kimiyya suka yi. babu wata kasa da ke da ikon bayyana ra’ayi kan wannan hakkin. A cikin taron manema labarai na mako-mako, Baqa’i ya yi ishara da abubuwan da ke faruwa a duniya a halin yanzu, yana mai jaddada...

Jami’in Makamashin Nukiyar Iran Ya Ce; Zarge-Zargen Da Ake Yi Kan Shirin Makmashin Nukiliyar Iran Siyasa Ce Kawai
Jami’in makamashin nukiliyar Iran ya jaddada cewa: Zarge-zargen da ake yi wa Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, siyasa ne tsantsa Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: Zargin da ake yi wa Iran game da batun Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya, tsagwaron siyasa ne, ba bisa ka’ida ko na fasaha ba. Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya kara da cewa: Kudurorin da suka biyo baya da kuma kara matsin lamba a kan Iran suna share fagen fuskantar al’amura a nan gaba. Yayin da yake ishara da cikas iri-iri da ke kawo sarkakiya ga ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran, Behrouz Kamalvandi ya bayyana cewa: Wadannan kalubalen da suka kara ta’azzara a cikin ‘yan shekarun...

Iran Ta Yi Kakkausar Suka Kan Babban Darektan Hukumar IAEA Saboda Yadda Yake Mika Wuya Ga Bakar Siyasa
Babban darektan hukumar IAEA ya zama tamkar wata yar tsana ce a hannun kasashen Yamma don dakile shirin nukiliyar Iran An fara taron kwata-kwata na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a birnin Vienna, wanda ya samu halartar wakilan kasashe 35 mambobi hukumar Bisa la’akari da rahoton da babban daraktan ya fitar game da sa ido da tabbatar da shirin nukiliyar Iran karkashin yarjejeniyar kare kai da kuma tsarin aiwatar da ayyukan hadin gwiwa ta (JCPOA) na daya daga cikin batutuwan da za a tattauna. Babban darektan hukumar ta IAEA Rafa’el Grossi ya sanar a wani rahoto da ya fitar a makon da ya gabata cewa; Yawan sinadarin uranium da Iran ke da shi ya ninka har...

Al’ummomi Daga Sassan Duniya Suna Yin Tofin Allah Tsine Kan Sace Masu Fafatuka A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Gaza
Al’ummu daga dukkan sassan duniya suna mayar da martaninsu cikin fushi bayan sace jirgin ruwa Madeleine mai dauke kayayyakin jin kai zuwa Gaza Kwamandojin sojojin mamayar Isra’ila sun yi garkuwa da jirgin ruwan farare hula Madeleine, wanda ke yunkurin karya killace yankin Zirin Gaza da aka yi a kokarinsu na shigar da kayan agaji ga al’ummar yankin da suka rage. Sojojin mamaya sun garkuwa da masu fafutuka tare da kai su tashar ruwan Ashdod. Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin sun yi tir da laifin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata. Kungiyar Hamas ta bayyana shi a matsayin ta’addancin kasa da kasa. A wani sabon laifin da ya saba wa dukkanin ka’idojin kasa da kasa da na jin kai, sojojin...
Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.” Sanarwar ta...
Fadar mulkin Rasha ” Kremlin” ta sanar da cewa; Kasar Rasha tana fadada fafagen yin aiki da kasashen Afirka da su ka hada da fagage masu muhimmanci na soja da tsaro. Kakakin fadar ta “Kremlin” Dmitry Viskov da yake amsa tambaya akan tasirin shigar Rasha cikin nahiyar Afirka, ya ce; Sannu a hankali Rasha tana kara shiga cikin nahiyar ta Afirka’ sannan kuma ya yi ishara da azamar da Rashan ta yi na ganin wannan alakar ta bunkasa tare da mayar da hankali akan tattalin arziki da kuma zuba hannun jari.”
“Mun bi tsarin mulki kuma mun ƙi rashin adalci. Da PDP ta yi haka, ba za ta fuskanci wannan matsala ba.” Taron ya haɗa da tsoffin gwamnonin jihohi Samuel Ortom (Benue) da Okezie Ikpeazu (Abia), da sauran shugabannin jam’iyyar. Wike ya soki shugabannin PDP saboda sanya son rai fiye da haɗin kan jam’iyyar. Ya ce jam’iyyar sai ta koma tubalinta na asali don samun ci gaba. “Wasu shugabanni suna karkatar da dokoki don amfanin kansu,” in ji Wike, yana ambaton yadda gwamnan Taraba ya tsaya takarar gwamna ba tare da ya yi murabus a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ba. “Dole ne a daina wannan.” Tsohon Gwamna Ortom ya yarda da maganar Wike, ya amince cewa PDP ta yi manyan kurakurai....
Ma’aikatar kiwon lafiya na kasar Iran ta bayyana cewa kasar a halin ayanzu tana daga cikin kasashe uku na gaba a kan abinda ya shafi samun isasshen abinci mai lafiya da kuma wadatacce a cikin kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan kiwon lafiya Muhammad Reza Zafarkandi yana fadar haka a jiya litinin a taron raya ranar abinci da duniya wanda aka gudanar a dakin taro na hukumar gidajen radio da talabijin a nan birnin Tehran. Ministan ya kara da cewa, samun abinci mai gina jiki da kuma bada sinadaran da jiki yake bukata yana daga cikin abubuwan da suke bada lafiya ga jiki. Har’ila yau wannan yana kwantar da hankalin mutanen ko wace kasa wacce...
Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan birnin Hudaidah na bakin ruwa a kasar Yemen a safiyar yau Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto tashoshin talabijin ta Almasirahtv ta kasar Yemen, da kuma Aljazeerah ta kasar Qatar suna bada wannan labarin. Sun kuma kara da cewa tun fara yaki a Gaza a shekara ta 2023 sojojin kasar Yemen suka hana jiragen kasuwanci na HKI wucewa ta babul Mandab na kasar Yemen wanda ya jawowa HKI asarori masu yawa, ya kuma gurgurta ayyukan tashoshin jiragen Ruwa na ummu Rashrash ko Ilat da kuma Haifa. Sannan suna kaiwa hki hare-hare ne da makamai masu linzami kan tashar jiragen sama na Bengerion da kuma wuraren soje na kasar tun...
Sojojin Isra’ila sun ƙwace wani jirgi da ke ɗauke da kayan tallafi mai suna Madleen wanda ke kan hanyara a zuwa Gaza, sannan suka karkata akalar shi zuwa Isra’ila. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ilan ta fitar da tsakar daren Lahadi ta bayyana cewa za a mayar da masu fafutukar da ke cikin jirgin zuwa ƙasashensu. Sojoji sun kashe wani kwamandan ’yan ta’adda a Yobe Zai fi kyau Tinubu ya mayar da hankali kan ’yan Nijeriya ba Zaɓen 2027 ba — ACF Sanarwa da aka wallafa a X, ma’aikatar ta ce jirgin yana “kan hanyarsa zuwa gaɓar tekun Isra’ila” kuma “ana sa ran fasinjojin za su koma ƙasashensu.” Ƙungiyar Freedom Flotilla Coalition ta ce sojojin Isra’ila sun “yi...
Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya ACF ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su daina gaggawar shige-da-fice wajen neman tazarce a Zaɓen 2027. ACF ta ce zai fi dacewa gwamnatin Tiinubun ta mayar da hankali wajen ganin ta kyautata rayuwar ’yan Nijeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓensa a 2027, lamarin da ƙungiyar cewa hakan ya yi wuri. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba Ɓarawon waya ya kashe babban jami’in soja da wuƙa a Kaduna Wannan kira dai na kunshe cikin wata sanarwar yi wa musulmi barka da Sallah Babba da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar. Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da...
Tare da cewa giwaye suna cikin dabbobin da masu yawon bude ido suke son gani, said ai gwamantin kasar Zimbabwe ta yanke hukunci yanka 50 daga cikinsu domin rabawa mutanen karkara namansu. Wannan matakin na gwamnatin Zimbabwe ya zo ne saboda yadda giwayen suke kara yawa sosai a cikin shekarun bayannan. Haka nan kuma wuraren da ake killace su, sun yi kadan. Majiyar dake kula da gandun dajin kasar ta ce; adadin giwayen ya rubanya har sau uku, wannan ne ya sa mahukuntar kasar su ka yanke shawarar yanka 50 daga cikinsu saboda a rabawa mutanen karkara. A baya gwamnatin na Zimbabwe ya yi kokarin warware matsalar karuwar dabbobin ta hanyar sauya musu gandun daji da wuraren da aka killace...
A daidai lokacin da kungiyar kasashen tsakiyar Afirka ta tattalin arziki ( ECCAS) take yin taro, kasar Rwanda ta sanar da ficewa daga cikinta. Bayanin da gwamnatin kasar ta Rwanda ta fitar ya kunshi cewa; Kasar Rwanda tana nuna takaicinta akan yadda kasar DRC take amfani da kungiyar tattalin arziki ta tsakiyar Afirka a matsayin wani makamin a hannunta.” Bayanin gwamnatin ta Rwanda ya kara da cewa: Yadda DRC take amfani da wannan kungiyar ya sake fitowa fili a yayin taron kungiyar karo na 26 a Malabo, ta yadda aka kau da kai akan hakkin Rwanda na shugabancin karba-karba,kamar yadda yake a cikin doka ta shida ta kundin kungiyar. Hakan kuma ya faru ne sanadiyyar shiftar DRC ga kungiyar.” A...

He Lifeng Zai Ziyarci Birtaniya Tare Da Halartar Taron Farko Na Tattauna Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Sin Da Amurka
Ma’aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ta sanar a jiya Asabar cewa bisa gayyatar da gwamnatin Birtaniya ta yi masa, memba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, zai ziyarci Birtaniya tun daga yau Lahadi har zuwa Juma’a 13 ga watan nan na Yuni. Ana sa ran yayin ziyarar tasa a Birtaniya, He Lifeng zai halarci taron farko na tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Kafofin yada labarai daga Isra’ila na tabbatar da kutsen da akayi wa kasar akan wasu takardun bayyanan sirrin shirinta na nukiliya. Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da Iran ta ce ta samu tarin takardun sirri da suka shafi ayyukan nukiliyar Isra’ila. Ministan leken asirin kasar Iran Esmail Khatib ya ce tarin takardun sirri na Isra’ila da kasar ta samu na da alaka da makaman nukiliyar gwamnatin kuma za su kara karfi ga tsarin garkuwa daga hare-haren sama na Iran. “Takardun da muka samu na da alaka da bayanai game da cibiyoyin nukiliyar su,” kamar yadda Khatib ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na IRIB. Kafafen yada labaran Isra’ila sun tabbatar da hakan, tare da bayyana shi a matsayin “babban...
Gwamnatin kasar Ruwanda ta sanar da janyewa daga kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen tsakiyar nahiyar Afirka wato CEEAC, bayan ta zargi jamhuriyyar demokuradiyyar Congo da hada kai da wasu kasashe membobin kungiyar, wajen amfani da kungiyar don neman cimma bukatunsu. Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Ruwanda ta fitar, an ce, a gun taron koli na kungiyar ta CEEAC da aka gudanar a birnin Malabo dake kasar Equatorial Guinea, jamhuriyyar demokuradiyyar Congo ta hada kai da sauran kasashe membobin kungiyar, don hana Ruwanda damar karbar ragamar shugabancin kungiyar a wannan karo. Ma’aikatar ta bayyana cewa an ware Rwanda daga taron koli na 22 na ECCAS da aka gudanar a Kinshasa a...
Tashar talabijin din ‘almayadin” ta ambato wata majiya ta Iran tana cewa; Jami’an leken asirin kasar sun sami muhimman byanai akan Shirin Nukiliyar HKI. Majiyar ta kara da cewa; Jami’an leken asirin Iran sun iya isa ga wadannan muhimman bayanan masu yawan gaske tare da yin jigilarsu zuwa cikin kasar Iran. Daga cikin bayanan da akwai wadanda su ka shafi shirye-shiryen da ‘yan sahayoniyar suke aiwatarwa na Nukiliya da kuma cibiyoyin Nukiliyar. Majiyar ta kara da cewa; jami’an leken asirin na Iran sun iya kai wa ga wadannan bayanan tun shekarun da su ka gabata, kuma saboda yawan bayanan da kuma hanyoyin shigo da su cikin Iran ne ya sa ba a bayyana shi ba sai yanzu. Haka nan kuma...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa kasar Iran tana gudanar da ayukanta na bincike a cibiyoyin Nukliyar kasar tare amincewa da bincike kuma a bayyana take hakan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto shugaban yana fadar haja a jiya Asabar a lokacinda yake ganawa da mataimakin firay minister kuma ministan harkokin wajen kasar Kazakistan Murat Abugaliuly wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran. Shugaban ya kara da cewa tun lokacinda kasar ta fara tache sinadarin Uranium hukumar makamacin Nukliya ta duniya IAEA na sanya ido a ayyukanta, sannan tun lokacin bata bada rahoton cewa shirin nata ba ta zaman lafiya ba. Daga karshe shugaban ya kara da cewa bayan wannan kuma ba zamu taba amincewa...
Daya daga cikin shuwagabannin Falasdinawa ya yi shahada sanadiyyar hare-haren da sojojin HKI suka kai kan zirin gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Asa’d Abu Sharia shi ne baban sakataren kungiyar ‘Dakarun Palastinewa”. Wacce aka kafa a shekara ta 2001 M. Kungiyar kanta ta tabbatar da wannan labarin ta kuma bayyana cewa ya dade yana shugabantar wannan kungiyar sannan a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya shiga cikin yakin da aka fara kan HKI kuma dakarunsa sun kama yahudawa da dama suka shigo da su su gaza. Banda haka shi ne yake jagorantar bangaren soje na kungiyarsa. Sau da dama ya jagoranci Falasdinawa a yaki da yahudawan a Gaza. Sannan kungiyar tana...
Kasar Ghana ta kawo karshen goyon bayan da take bawa kungiyar Polisario, sannan ta dawo tana goyon bayan kasar Morocco a kan wannan rikicin. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa, an kafa kungiyar Polisario ne a shekara 1979. Sannan rikicin Polisario yana komawa zuwa shekara 1975 a lokacinda turawan Espania yan mulkin mallaka suka fice daga yankin sai suka hadda fada tsakanin Polisario da kasashen Morocco da kuma Mauritania. Kungiyar dai tana samun goyon bayan kasashe kimani 80 a duniya, amma kuma a hankali-a hankali tana rasa goyon bayan da take da samu a duniya, na karshensu it ace kasar Ghana.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta wallafa tsokacinta kan rahoton babban darartan Hukumar IAEA ga kwamitin gwamnonin hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da ra’ayoyinta da tsokacinta kan sabon rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) ya gabatar ga kwamitin gwamnonin hukumar ta IAEA a ranar 24- wannan shekara ta 2025. A cewar cibiyar diflomasiyya da ta yada labarai ta hukumar makamashin nukiliya ta Iran, an fitar da bayanin mai taken “Sa ido da Tabbatarwa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da kudurin kwamitin tsaro mai lamba 2231 (2015)” a ranar 31 ga Mayu, 2025. Bayanin ya fayyace cewa: Rahoton da babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa...

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Na Ganin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa A Matsayin Hanyar Warware Takaddamar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka
CGTN ta wallafa nazarin ne a dandamalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci. Kuma mutane 5610 ne suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 12. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
vvddxfKungiyar bada agaji ta Red Cross ta nbada sanarwan cewa ta rufe ofishinta a Nijer kuma ta fidda dukkan ma’aikatanta na kasashen waje daga kasar. Ta kuma kara da cewa, gwamnatin kasar ta bukacin kungiyar ta fice daga Nijer tun watanni 4 da suka gabata, amma bata yi hakan bas ai yanzu. ICRC ta tabbatar da hakan a ranar Alhamis da ta gabata Sannan Patric Yousuf daraktan kungiyar a Nahiyar Afirka ya bayyana cewa sun janye ma’aikatansu a Nijer sannan suna tattaunawa da gwamnatin kasar don sake dawowa kasar da kuma ci gaba da ayyukansu na bada agaji. A cikin watan Fabrayrun wannan shekara ne ministan harkokin wajen kasar ya bada wannan umrnin ba tare da bayyana dalilan yin haka...
Abu Ubaida kakakn dakarun Ezzuddeen Al-Qassam reshen soje na kungiyar Hamasa ya bayyana cewa dakarunsa zasu ci gaba da Yakar sojojin yahudawa har zuwa korarsu daga yankin zirin Gaza. Abu Ubaida ya kara nda cewa, dakarun Hamas suna a madaka ga sojojin HKI babu jada baya babu janyewa daga matsayinsu. Kafin haka dai a jiya Jumma’a dakarun na Hamas tare da hadin guiwa da na Saraya Qudus sun aiwatar da wani shiri ko tarko kan sojojin yahudawan wanda ya sami nasara halaka sojojin yahudawa da dam. Majiyar yahudawan sun tabbatar da aukuwar hare-haren na Khan Yunus dake kudancin Gaza, wanda kuma ya halaka yahufawa da dama., Abu ubaida ya kammala da cewa aikin soje da suka yi a Khan Yunus...
Ministan harkokin wajen Faransa ya jaddada aniyar birnin Paris na amincewa da kasar Falasdinu Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya tabbatar da aniyar Faransa na amincewa da kasar Falasdinu, yana mai jaddada cewa wannan amincewa ba zai kasance na bai daya ba, sai dai a matsayin wani bangare na kokarin hadin gwiwa da sauran kasashe. Hakan ya zo ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo kasa makonni biyu gabanin taron hadin gwiwa tsakanin Faransa da Saudiyya a Majalisar Dinkin Duniya. Barrot ya bayyana cewa, makasudin taron shi ne hada kasashe da masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da hukumar Falasdinawa da kasashen Larabawa don ciyar da shirin zaman lafiya gaba. Ya...
Ya ce an samu yawan mace-macen ne saboda rashin bin umarnin gargadin ambaliyar ruwa daga mutane a jihar. Ya bukaci jihohi su dauki matakai don hana mummunar ambaliyar ruwa da ka iya lalata rayuka da kadarori, ministan ya ce, “Ma’aikatar Tarayya ta Albarkatun Ruwa da Tsabtace Muhalli tana mika ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar Jihar Neja, musamman ga al’ummomin da lamarin ya shafa a Mokwa, wadanda suka fuskanci asara, mutuwa da canjin wuri sakamakon wannan bala’i na ambaliyar ruwa. “Ina jaddada cewa ambaliyan da aka samu ba ta kasance saboda sakin ruwa daga dam din Kainji ko Jebba ba ne, domin duka dam din suna cikin tsaro. “Mun yaba da kokarin gaggawa na gwamnatin Jihar Neja da hukumomin yankin, da...
Shugabannin nahiyar Afirka sun tattauna hanyoyin samar da maganin kwalara a cikin nahiyar. An tattauna wannan batun ne dai a yayin taron da aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa akan hanyoyin magance cutuka mabanbanta da su ka hada da riga-kafi. Wadanda su ka halarci tattaunawar ta bidiyo sun hada shugabannin kasashen Angola, Namibia, Malawi da kuma DRC. Shugaban kasar Zambia Hakayinde Hichilema ya bayyana cewa; Da akwai bukatar nahiyar Afirka ta fara samar da magunguna cikin gaggawa tare da dogaro da nahiyar wajen samar da kudaden da ake bukata domin yin hakan, saboda kaucewa dogaro da waje.” Haka nan kuma shugaban kasar ta Zambia ya ce: Saboda kwalara idan ta barke ba ta san iyakar kasashe ba, ya kamata...
Gidauniyar ta kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammed Aliyu Shaaba, inda wakilan fadar suka yi maraba da tawagar wakilan gidauniyar tare da jinjina taimako da goyon bayan da aka nuna musu a wannan hali da suke ciki na ibtila’i. Kamar yadda Babban daraktan yankin, Musa Aliyu ya bayyana, gidauniyar Dr. Abubakar Bukola Saraki ta kai taimakon kuɗi domin tallafawa waɗanda suka tsira da masu taimaka musu. Sannan ya yi kira ga ƙungiyoyi masu zaman kansu da ɗaiɗaikun mutane da su taimakawa al’ummar garin Mokwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qolibof ya bayyana cewa kungiyar BRICS wata dama ce ta kaucewa danniya da babakeren da Amurka take kudaden sauran kasashen duniya. Qolibof yana bayyana haka ne a lokacin ganawarsa da shugaban majalisar dokokin kasar Brazil Dowi Alku-Lomubre a gefen taron shuwagabannin majalisun dokokin kungiyar BRICS wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Brazia na kasar Brazil. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban majalisar dokokin Iran yana fadar cewa kasashen Iran da Brazil suna da fahinta iri guda dangane da yenci da kuma zama yentacciyar kasa. Don haka tare da wannan ana iya gina dangantaka ta bunkasar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu tare da wannan fahintar. Qolibof ya kara...
Lamarin ya ƙara tsananta ne bayan fitowar wani littafi mai taken Original Sin da ya zargi wani na kusa da Biden da ɓoye yadda jikinsa ya gaza yayin yaƙin neman zaɓen 2024, wanda daga ƙarshe ya janye. Wannan ya ƙara sanya tambayoyi kan ko an san da cutar sankarar da ya kamu da ita tun da wuri, musamman ganin yadda aka ce ta bazu zuwa ƙasusuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan filin jirgin saman Lod da ke Jaffa da aka mamaya da jiragen sama biyu marasa matuka ciki Sojojin Yemen sun sanar da kai wani farmakin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma nuna tsananin Rashin amincewa da kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan uwansu a zirin Gaza. Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, inda ta ce farmakin da rundunar sojin saman Yemen ta kai da jiragen saman yaki marasa matuka ciki kirar Yaffa guda biyu, ya samu nasarar cimma burin da ake bukata. Rundunar...
Babban jami’in diflomasiyyar Iran ya sake tabbatar da cewa Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba kan ‘yancinta na tace Uranium, yana mai cewa ci gaban da kasar ta samu a fannin makamashin nukiliya ya samo asali ne sakamakon sadaukarwa da kuma saka hannun jari na kasa. A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya ce, ba batun inganta makamashin Uranium a duk wata yarjejeniyar nukiliya da za a yi nan gaba. “Iran ta saka kudi da yawa domin kai wag a wannan mataki, sannan kuma ba zai sa mu yi watsi da sadaukarwar da ‘yan kishin kasa sukayi don tabbatar da burinmu. Araghchi ya bayyana tace...
Wasu daga cikin mazauna yankin Mokwa da ambaliyar ruwa ta lalata wa gidaje a Jihar Neja, yanzu na zaune a sansanin ’yan gudun hijira. Ambaliyar, wadda ta kashe sama da mutum 100, ta jawo asarar dukiya da lalacewar gidaje da dama a yankin. Direbobi sun toshe babbar hanyar Kogi sakamakon harbe abokan aikinsu Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji Aminiya ta kai ziyara sansanin a ranar Talata, inda ta ɗauki wasu hotuna da ke nuna halin da waɗanda abin ya shafa ke ciki da yadda suke rayuwa a sabon wajen da suka koma. Ga hotunan a ƙasa:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wata al’ada da ta zama gama gari a tsakanin matasa, ita ce yankewa da fige kaji a unguwanni, musamman a lokutan bukukuwan Sallah. A da, ana da wurare na musamman da ake yin irin wannan abu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa Sai dai masana sun ce wannan abu na iya haifar da matsaloli ga lafiya da kuma gurɓata muhalli. Wannan shi ne abin da shirin Najeriya A Yau zai tattauna a kai, yayin da ake Bikin Ranar Muhalli ta Duniya kwana ɗaya kafin Babbar Sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
Wasu direbobin manyan motoci sun rufe hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta da ke Jihar Kogi domin nuna fushinsu bayan jami’an tsaro sun harbi ɗaya daga cikinsu da kuma mataimakinsa. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’an tsaro suka harbi mutanen biyu saboda sun ƙi tsayawa a wajen binciken da aka tsayar da su. Ambaliyar Mokwa: An gano gawar yara 7, jama’a na neman agaji Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Sai dai, babu wanda ya mutu sakamakon harbin. An garzaya da su asibiti domin ba su kulawar gaggawa. Hakan ne, ya sa sauran direbobin suka fusata, suka toshe bakin gadar Ganaja da ke babbar hanyar Lokoja zuwa Ajaokuta. Sun ƙi...
DSP Alabo, ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Filato, CP Emmanuel Olugbemiga Adesina, ya jaddada ƙudirin rundunar wajen yaƙi da laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a jihar. Ya kuma roƙi jama’a da su riƙa bai wa ‘yansanda ingantattun bayanai a kan lokaci domin taimaka musu wajen gudanar da aikinsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An gano gawar yara bakwai a yankin Mokwa, da ke Jihar Neja, bayan ambaliyar ruwa da ta afka wa garin mako guda da ya wuce. Yawan adadin waɗanda suka rasu kawo yanzu ya kai mutum 160, amma wasu jami’ai sun ce za a iya gano gawar sama da mutum 200. Kotu ta aike da ɗan Tiktok gidan yari kan yin shigar mata a Kano Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda Ambaliyar ta kuma tafi da motar haya mai kujeru 18 ɗauke da fasinjoji. Kawo yanzu, bayan kwana shida da faruwar ambaliyar, ba a ga motar ko wani daga cikin fasinjojin ba. Wani mazaunin garin, Baba Abu, ya ce: “Direban bai nemi ƙetare ruwan ba. Ya...
Wata kotu da ke unguwar Noman’s Land a Jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare fitaccen ɗan TikTok, Abubakar Kilina, a gidan gyaran hali har zuwa ranar 17 ga Yuni, 2025. Wannan hukunci ya biyo bayan tuhumar da Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta shigar da ke zargin sa da aikata halaye da suka saɓa wa tarbiyya da al’adu Hausawa. Sallah: Mun shirya samar da tsaro a Yobe — ’Yan Sanda Ba zan yi musayar yawu da yara ba — Martanin Amaechi ga Wike Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na yunƙurin hukumar na daƙile yaɗuwar rashin ɗa’a a kafafen sada zumunta, musamman TikTok. “Mun ƙudiri aniyar daƙile duk wani abin...
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Nain Qasim da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi sun gana a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran siyasa da yankin kudancin Asiya tare da kasar Lebanon. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto aragchi yana cewa dangantaka tsakanin Iran da kungiyar Hizbullah dangane ce wacce ta shafi yankin kudancin Asiya gaba daya. A nashi bangaren shugaban kungiyar Hizbullah sheikh Naem Kassem ya godewa JMI ta irin tallafin da take bayarwa ga kungiyoyi da kasashen kawancen masu gwagwarmaya a yankin wadanda suka hada da Falasdinawa da Lebanon da sauransu. Aragchi ya kara da cewa Iran a shirye take ta taimakawa kasar Lebanon a...
Jami’an Yansanda masu kula da ayyukan ta’addanci da kuma hana aukuwarsu a nan Iran sun sami nasarar kama wasu yan kungiyar ISIS 13 a duk fadin kasar daga ciki har da shugabansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Saeed Montazer al-Mahdi kakakin rundunar FARAJA mai kula da fada da yan ta’adda yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa yan ta’addan su 13 daga cikin har da shugabansu, sun kuduri anniyar kai hare-hare a cikin Jama’a su kuma kashe mutane a wasu tarurrukan da aka gudanar a kasar nan. Labarin ya kara da cewa an kama yan ta’addan na ISIS a biranen Tehran, Qum, Esfahan da kuma Albus. Kuma an kama tare da su kayakin...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama daya daga cikin masu kamfanin Microsoft, Bill Gates, da lambar girmamawa ta kasa — Commander of the Order of the Federal Republic (CFR), inda ya jaddada cewa Gates ya kasance abin koyi ga shugabanni a fadin duniya saboda yadda yake taimaka wa talakawa da masu bukata ta musamman. Shugaban ya kuma bayyana cewa Mista Gates, wanda shi ne Shugaban Gidauniyar Melinda da Gates, ya bada gudummawa a fannonin kiwon lafiyar mata, noma da bincike kan cututtuka masu yaduwa. Ya gode wa Bill Gates bisa gudummawar da yake bayarwa a duniya, musamman wajen saukaka rayuwa da kare lafiyar masu rauni da wadanda ke cikin bukata. Ministan Lafiya da Ci gaban Jama’a, Farfesa Ali Pate,...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Zata mayar da martani mai gauni kan yadda ake siyasantar da batun nukiliya a cikin kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya jaddada cewa: Idan aka mayar da batun Iran na nukiliya siyasa a taron kwamitin gwamnonin cibiyar IAEA, bai kamata daya bangaren ya sa ran Iran za ta ci gaba da yin aiki da cikakken kamun kai ba tare da mayar da martani ba. Maimakon haka, Iran za ta gudanar da mu’amalarta da siyasarta daidai da halayensu da manufofinsu. A cikin wata sanarwa da ya fitar ta gidan talabijin na Iran a yammacin jiya Talata, dangane...

Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa: Amurka Da Isra’ila Suna Da Mugun Nufi Kan Iran Da Kasashen Musulmi
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suna da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da mugun nufi kan Iran da kasashen musulmi. A yayin wani jawabi da ta gabatar a wajen juyayin tunawa da rasuwar Imam Khumaini {r.a}, Pezeshkian ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba za ta iya aikata wani aiki hauka da wauta ba, idan kasashen musulmi suka hada kansu. Pezeshkian ya kara da cewa: Wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama suna kare “haramtacciyar kasar Isra’ila” mai laifi, kuma suna ci gaba da adawa da shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Ya ci gaba da cewa: “Babu mutum...
Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2. Hari ya gudana daidai inda aka tsara shi, kuma ya haifar da firgici da ya kai ga miliyoyin yahudawan sahayoniyya gudu tare da shigewa maboyar karkashin kasa kamar burage. Har ila yau, harin ya dakatar da dukkan ayyukan filin jirgin, tare da hana wani jirgin dakon kaya na sojan Amurka sauka a filin jirgin sama na Ben Gurium a rana ta biyu a jere. A cikin wannan yanayi ne...
Irin manufar bude kofa da gyare-gyare ta kasar Sin duniya da jama’arta suka fi bukata, domin ita ce za ta bada damar samun dunkulewar duniya da ci gabanta kamar yadda ake fata, har ma da kai wa gina duniya mai kyakkyawar makoma ga dukkannin dan adam. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”. Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, a yau Talata ya yi watsi da ikirarin da Amurka ta yi na cewa kasar ta Sin na karya yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin kasashen biyu a tattaunawar tattalin arziki da kasuwanci da aka yi a Geneva, inda ya bukaci Amurka da ta daina yada labarun kanzon kurege. A yayin taron manema labarai na yau da kullum, Lin ya bayyana cewa, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace, tare da daukar yarjejeniyar da aka cimma a shawarwarin Geneva da muhimmanci, tare da aiwatarwa yadda ya kamata. Yanzu-yanzu: JUSUN Ta Dakatar Da Yajin Aikin Da Fara A Faɗin Ƙasa Baki Ɗaya Sallah: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Naira Miliyan...
A cikin sanarwar da dukkan bangarorin da suka halarci taron suka sanya wa hannu, an amince da cewa, kungiyar za ta ba da wata guda domin tattauna bukatun JUSUN. Wani bangare na yarjejeniyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta saki kudaden da suka wajaba ga bangaren ma’aikatan shari’a a cikin wannan watan. Sanarwar ta jaddada cewa, da zarar an fitar da kudaden, dole ne a aiwatar da duk wasu bukatu da kungiyar ta JUSUN ta gabatar ba tare da bata lokaci ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranar Laraba da ta gabata da daddare. Ɗaruruwan gidaje sun lalace, inda mutane da yawa suka rasa matsugunansu. Kafar yaɗa Labarai ta BBC ta ruwaito a ranar Litinin cewa yawan mutanen da suka mutu ya ƙaru zuwa sama da 200, kuma an dakatar da ayyukan ceto saboda hukumomi sun yanke ƙauna daga samun wasu da rai. Babbar Sallah: Farashin kayan miya ya yi tashin...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaro da muradun kasar a cikin tsibiran guda uku. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya jaddada matsayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da yin watsi da ikirarin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron ministocin harkokin wajen kasashen yankin tekun Fasha karo na...
Rikici tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar yana ci gaba da habaka a wurare da dama na kasar Kasar Sudan dai na fuskantar tabarbarewar harkokin tsaro cikin hanzari, a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF), a cikin sarkakkiyar yanayin jin kai da na siyasa da kuma fadadan rikici a jihohi daban-daban. Fadace-fadace a Sudan suna ci gaba da karuwa, inda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan kungiyar Rapid Support Forces, inda sojojin saman Sudan suka zafafa kai hare-hare ta sama ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki, kuma suka yi luguden wuta kan wasu muhimman...
Hukumar ta buƙaci jama’a da su kasance cikin shiri tare da bibiyar sabbin rahotannin yanayi da ta ke fitarwa. Ta kuma ja hankalin hukumomin da ke kula da madatsun ruwa da su saka ido kan matakin ruwa domin gujewa cike-ciken da ka iya haddasa ambaliya. Rahoton ya ƙara da cewa jihohin kudancin Nijeriya da kuma na Arewa ta Tsakiya za su riƙa samun ruwan sama da iska a kai a kai. Sai dai NiMet ta ce jihohin Kwara, Kogi, Neja, Nasarawa, Benuwe, Taraba, Adamawa, Kaduna, Kano, Katsina, Sakkwato, Edo, Delta da Abuja ba za su samu ruwan sama da yawa kamar yadda aka saba ba. Hukumar ta buƙaci manoma da su yi amfani da dabarun zamani da ilimin kimiyya wajen...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata hajiyar Najeriya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya. Hajiya Jamila Muhammad ta rasu ne a yayin da alhazai ke shirin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan. Sakataren Hukumar Kin Dadin Alhazai ta Jirage Filato, Daiyabu Dauda, ya sanar a ranar Litinin cewa Hajiya Jamila ta rasu ne a asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah, sakamakon tashin cutar suga. Ya ce Amirul Hajj na jihar da wasu manyan jami’ai sun halarci jana’izar marigayiyar, kamar yadda Musulunci ta tanada. Yadda magidanci ya kuɓuta bayan wata 7 a hannun ’yan bindiga NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Hajji ta bayan fage: Saudiyya ta hana mahajjata 269,000 shiga Makka Da rayuwarta, yawan alhazan Najeriya da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ambaliyar ruwa na ci gaba da raba dubban mutane da matsugunansu, tare da lalata dukiyoyi a faɗin Najeriya. Ko a makon da ya gabata, wasu al’ummomi a Karamar Hukumar Mokwa da ke Jihar Neja sun fuskanci irin wannan ambaliya da ta yi sanadiyyar rasa ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi masu yawa. NAJERIYA A YAU: Mokwa: Tsakanin Taraddadin Rashin Matsuguni Da Jimamin Rashin ’Yan-Uwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada” Ko waɗanne hanyoyi za a bi domin kauce wa ɓarnar ambaliya a Najeriya? Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a kungiyar Shangai. Muhammad Riza Farzin ya isa kasar ta China ne domin halartar taron gwamnonin manyan bankunan kasashen da suke mambobi a cikin wanann kungiya, domin yin nazarin hanyoyin aiki tare a tsakaninsu da kuma musayar kudade. Muhammad Riza Farzin ya kuma kara da cewa; Daga cikin ajandar taron kungiyar a China, akwai tattauna batun kafa bankin hadin gwiwa wanda daga cikin ayyukansa a akwai aiwatar da hada-hadar kudade da mu’amala a tsakanin Bankuna.” Gwamnan babban bankin na Iran ya bayyana cewa, wannan kungiyar tana da matukar muhimmanci, domin tana kunshe da kasashe goma daga...
Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu muhimman wurare a yankunan Jaffa, Ashdod da Umm al-Rashrash a cikin Palasdinu da aka mamaye. Rundunar sojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Rundunarta ta kai wasu hare-haren soji masu inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami. Dakarun sojin sun tabbatar da cewa: wannan...
Ya buƙaci shugabannin haɗakar su fara tsarin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta kasance mai suna ɗaya, falsafa ɗaya, da tsarin shugabancin da zai haɗa kan kowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministocin shari’a na Burkina Faso, Mali da Nijar sun amince da kafa kotun hukunta laif uka da kare hakkin bil’adama ta kungiyar tarayyar kasashen Sahel. Haka kuma za a gina wani gidan yari mai cikakken tsaro a yankin, mai alaka da wannan kotun, domin karfafa hanyoyin yaki da ta’addanci da aikata laifuka a yankin. Sun bayyana hakan ne bayan taron da suka gudanar a birnin Bamako a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu. Kotun hukunta manyan laifuka da kare hakkin bil’adama a yankin Sahel A cewar shafin labarai na APANews, za ta dauki nauyin “duba laifukan cin zarafin bil’adama, laifuffukan yaki, kisan kiyashi da ta’addanci, halatta kudaden haram da kuma cin zarafi mai tsanani na ‘yancin dan adam da...