Leadership News Hausa:
2025-09-17@20:28:32 GMT

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

Published: 13th, September 2025 GMT

Kasar Sin Za Ta Kare Hakkin Kamfanoninta Ciki Har Da Tiktok

Ma’aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta yi karin haske kan shirin tattauna batun kamfanin TikTok a ganawar da tawagogin Sin da Amurka za su yi a kasar Sifaniya a gobe Lahadi, 14 ga wata.

Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, matsayin kasar Sin kan batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma bai taba canzawa ba.

Ta ce kasar Sin tana da cikakkiyar niyyar kare hakkin kamfanoninta, kuma za ta tantance batun kamfanin TikTok bisa doka. Ban da haka, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan ikon kebanta bayanai da tabbatar da tsaronsu, ba za ta taba bukatar wani kamfani ya tattara bayanai a sauran kasashe ta wata haramtacciyar hanya ba.

Sanarwar ta kara da cewa, bisa la’akari da yadda tawagogin kasashen Sin da Amurka za su tattauna maganar TikTok da sauran batutuwa, kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya hada hannu da bangaren Sin, don nemo bakin zaren warware matsalar da ake fuskanta, da samar da muhalli mai adalci ga kamfanonin Sin dake gudanar da harkokinsu a kasar Amurka, ciki har da TikTok, ta yadda za a tabbatar da ci gaban huldar cinikayya a tsakanin kasashen 2, cikin wani yanayi mai inganci da dorewa. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai

Shugaban kasar Iran yana mai jaddada cewa wajibi ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan, inda ya ce: Wajibi ne kasashen musulmi su tsaya tsayin daka tare da daukar matakai na zahiri a fagen tattalin arziki, al’adu da zamantakewa, yanke alakarsu da gwamnatin sahyoniyawan.

Masoud Pezeshkian shugaban kasar Iran a jiya litinin kafin ya tashi zuwa kasar Qatar domin halartar taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da kungiyar hadin kan kasashen larabawa dangane da harin da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa birnin Doha, ya bayyana cewa: “Gwamnatin yahudawan sahyoniya ba ta amince da wani iyaka ga kanta ba, kuma tare da goyon bayan Amurka, ta kai hare-hare kan kasashen musulmi da dama da suka hada da Qatar, Lebanon, Iraq, Iran, Yemen da kuma kasashen turai suna goyon bayan wadannan kasashen duniya. ayyuka.”

Shugaban na Iran ya kara da cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, tare da la’antar mata da yara da tsoffi, abin takaicin shi ne kasashen yammacin turai, ta hanyar goyon bayansu da kuma tanade-tanaden da suke baiwa gwamnatin wariyar launin fata ta sahyoniyawa, sun halasta wadannan ayyukan.

Pezeshkian, yayin da yake bayyana fatan sakamakon taron gaggawa na OIC da shugabannin kungiyar kasashen Larabawa, ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su karfafa hadin kai da hadin kai don mayar da martani ga ayyukan gwamnatin sahyoniyawan da kuma kokarin tabbatar da cewa ana aiwatar da laifuffukan wannan gwamnati a dandalin kasa da kasa da na shari’a, ya kamata kasashen musulmi su tsaya tsayin daka, ta hanyar daukar matakai masu amfani a fannin tattalin arziki, al’adu, da zamantakewar al’ummar Sahayoniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Pars Today cewa, a yammacin ranar Talata 9 ga watan Satumba, jiragen kasar Isra’ila sun keta sararin samaniyar kasar Qatar, inda suka yi ruwan bama-bamai a yankin Katara na birnin Doha, babban birnin kasar, inda wata babbar tawaga ta Hamas karkashin jagorancin Khalil al-Hayya ke ganawa.

A mayar da martani, an gudanar da taron ministocin harkokin wajen kungiyar OIC a jiya Lahadi a birnin Doha, wanda ya samu halartar ministan harkokin wajen kasar Iran, domin tinkarar matsalar wuce gona da iri da sojojin gwamnatin sahyoniyawan suke kaiwa kasar Qatar. Wannan taron dai ya kasance share fage ga taron kasashen musulmi da na larabawa, wanda aka shirya gudanarwa a yau litinin tare da halartar Masoud Pezeshkian shugaban jamhuriyar musulinci ta Iran.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan:  Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya
  • Har Kullum Burin Sin Shi Ne Wanzar Da Daidaito Da Cimma Moriya Tare Da Amurka
  • Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
  • Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
  • Ministan Tsaron Kasar venezuela Ya Gargadi Amurka Dangane Da Kokarin Juyin Mulki A Kasar
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
  • Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Dakatar Da Shuka Kiyayya Da Tashin-Tashina A Tekun Kudancin Sin
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar