Girgizar ƙasa ta hallaka fiye da mutum 800 a Afghanistan
Published: 2nd, September 2025 GMT
Mutum sama da 800 sun mutu, yayin da wasu fiye da 2,500 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6 da ta auku a lardin Kunar da ke gabashin Afghanistan, kusa da iyakar Pakistan.
Girgizar ƙasar wadda ta auku da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi ta rusa gidaje da dama da aka gina da laka da duwatsu, lamarin da ya sanya dubban mazauna kwana a waje.
Rahotanni sun ce yara da mata na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu, kuma tuni an yi jana’izarsu.
Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya bayyana fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu ko jikkata na iya ƙaruwa domin akwai da dama da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzan gine-gine.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa wasu ƙauyukan da abin ya fi shafa ba za a iya kai musu agaji ba saboda hanyoyin da suka toshe.
Shugaban MDD, Antonio Guterres, ya miƙa ta’aziyarsa ga al’ummar Afghanistan cikin wata sanarwa da ya ce “ina goyon bayan da ƙara wa al’ummar Afghanistan ƙwarin gwiwa a wannan lokaci mai tsanani.”
Shi ma shugaban cocin Katolika na Vatican, Fafaroma Leo XIV, ya bayyana a wata sanarwa cewa ya “yana matuƙar baƙin ciki da rayukan da suka salwanta a sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a gabashin Afghanistan.”
A daren nan ne, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Afghanistan da UAE suka yi shiru na minti ɗaya domin girmama waɗanda suka rasa rayukansu, kafin fara wasan ƙetaren ƙasa a Sharjah.
Girgizar ƙasar ba ita farau baAfghanistan dai na cikin ƙasashen da ke yawan fuskantar girgizar ƙasa, musamman a yankin tsaunukan Hindu Kush.
Tun daga shekarar 1900, an samu girgizar ƙasa guda 12 da ƙarfinta ya haura maki 7 a yankin arewa maso gabas na ƙasar, a cewar Brian Baptie, wani masani a Birtaniya.
“Wannan irin girgiza, haɗe da haɗarin bala’o’i da kuma irin ginin da ke yankin, na iya haddasa asarar rayuka masu yawa,” in ji shi.
A watan Oktoba na 2023, girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.3 ta girgiza lardin Herat da ke yammacin ƙasar, inda mutane sama da 1,500 suka mutu, kuma gidaje sama da 63,000 suka lalace ko rushe.
A watan Yuni na 2022, girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.9 da ta auku a lardin Paktika, an rasa rayuka fiye da 1,000 kuma dubban mutane suka rasa matsuguni.
Bayan shafe shekaru 40 tana yaƙi, Afghanistan na fuskantar manyan ƙalubalen jin ƙai.
Tun bayan dawowar Taliban a shekarar 2021, tallafin ƙasashen waje ya ragu sosai, lamarin da ya sa ƙasar ke samun cikas wajen ɗaukar matakan gaggawa idan bala’i ya auku.
A halin yanzu dai Afghanistan na daga cikin ƙasashe mafi talauci a duniya, tana fama da mummunan rikicin jin ƙai, yayin da dubban ‘yan Afghanistan da aka mayar daga Pakistan da Iran suka koma gida cikin wannan shekara.
Kimanin kashi 85 cikin ɗari na al’ummar Afghanistan na rayuwa da ƙasa da dala ɗaya a rana, a cewar Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP).
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Girgizar ƙasa girgizar ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur.
Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki.
Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya.
“Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama. Ko da Atiku da magoya bayansa ba su yadda ba, ’yan Nijeriya suna ganin sauyin,” in ji Onanuga.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma zargi Atiku da jam’iyyar PDP da yaɗa maganganun da za su kawo tashin hankali.
Ya bayyana cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta sun samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci tun a lokacin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp