ECOWAS na shirin kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dakaru 260,000
Published: 26th, August 2025 GMT
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaki da ta’addanci mai dauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke kara ta’azzara a yankin.
Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin dakile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
“Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin ci-gaba,” in ji Musah.
ECOWAS ta ce za ta bukaci dala biliyan 2.5 a kowace shekara domin tallafa wa rundunar da kayan aiki da kudaden gudanarwa. Ana sa ran Ministocin kudi da na tsaro za su gana a ranar Juma’a domin kammala tsarin yadda za a samar da kudaden.
Touray ya ce yankin Sahel ya fi kowanne yanki fama da ta’addanci, inda ya ce kashi 51 cikin 100 na mutanen da suka mutu sakamakon ta’addanci a duniya a shekarar 2024 sun fito ne daga yankin.
A yayin da ECOWAS ke ci gaba da kokarin kafa rundunar sojoji 5,000 karkashin tsarin tsaro na Afirka, ana sa ran sabuwar rundunar za ta taimaka wajen kara karfin yaki da ta’addanci.
Nijar ta halarta, Mali da Burkina Faso sun kauraceSai dai ba dukkan kasashen da aka gayyata suka halarci taron ba. Daga cikin kasashe 54 da aka gayyata, 36 ne suka samu wakilci.
Ko da yake Jamhuriyar Nijar ta halarta, Mali da Burkina Faso ba su halarta ba — lamarin da ba zai rasa nasaba da rikicin siyasa da ke tsakaninsu da ECOWAS ba.
Tsohon Firaministan Guinea, Lansana Kouyaté, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na hadin gwiwar tsaro a Afirka.
“Karon farko ne shugabannin rundunonin tsaro na dukkan kasashen Afirka suka hadu. Wannan ya nuna muhimmancin batun — ba za a samu ci gaba ba sai da zaman lafiya,” in ji shi.
Kouyaté ya bukaci shugabannin Afirka da su hada kai wajen samar da tsaro, yana mai jaddada cewa Afirka ba kasa daya ba ce, illa dai hadin gwiwar kasashe masu bambancin tarihi da al’adu. Ya ce zai gabatar da shawarwari kan yadda za a samar da kudaden tsaro ta hanyar hadin gwiwa da masu zaman kansu.
Afirka ke da alhalin kula da tsaronta —MDDA nata bangaren, Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta bukaci shugabannin Afirka da su dauki nauyin tsaron nahiyar.
Ta yi gargadin cewa ta’addanci, yaki ta kafar intanet da sauyin yanayi na barazana ga zaman lafiyar Afirka. Ta kara da cewa, “Afirka ta zama cibiyar mutuwar mutane sakamakon ta’addanci. A cikin shekaru biyu kacal, hare-hare a kasashen gabar tekun yammacin Afirka sun karu da kashi 250 cikin 100.”
Ta ce fiye da makarantu 14,000 sun rufe a yankin Sahel saboda rikici, sannan ta yi gargadi kan barazanar fasahar zamani da sauyin yanayi, ciki har da faduwar ruwan tafkin Chadi da ta raba fiye da mutane miliyan uku da muhallinsu.
Tinubu ya bukaci sabuwar dokar tsaron AfirkaShugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya bukaci a samar da sabuwar dokar tsaro ta nahiyar Afirka da za ta dogara da amincewa, musayar bayanan sirri da hadin gwiwa.
“Wannan taro bai kamata ya kare da tafi ba kawai watse. Ya zama ginshikin sabuwar tsarin tsaro na Afirka,” in ji shi.
Ya bukaci a kafa taron dindindin na shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da kuma zuba jari a fannin kirkire-kirkire na tsaro da fasahar zamani.
A karshe, tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana cewa akwai fiye da kungiyoyin ’yan tada kayar baya 1,000 a nahiyar Afirka, yana mai kira da a kara karfafa masana’antar tsaro da kirkirar fasahohin gida.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tsaro yaki da ta addanci tsaro na Afirka
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci.
“Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA