Aminiya:
2025-09-17@23:15:18 GMT

Yau ake cika shekaru 10 da ƙirƙirar Ranar Hausa

Published: 26th, August 2025 GMT

A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya.

An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta.

An ɓullo da ranar ce domin haɗa kan masu magana da harshen Hausa a faɗin duniya da nufin magance matsalolin da ke ci musu tuwo a ƙwarya.

Da farko dai, an fara bikin wannan rana ce kamar wasa a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta amfani da kalmar #RanarHausa. Zuwa shekara ta 2018 kuma aka fara yin bikin a zahiri tare da gudanar da tarurruka da shagulgula a garuruwa a faɗin Najeriya da ma wasu ƙasashen irinsu Ghana.

NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 PDP ta miƙa wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027

Masu shirya bikin ranar suna ƙoƙarin ganin sun bayyana mahimmancin harshen Hausa da yadda za a ci gaba da yaɗa shi. Haka kuma a kan tattaro masana da masu bincike domin yin nazari kan wasu sabbin abubuwa da ya kamata a sani da Hausa.

A shekaru biyu da suka shuɗe, an yi bikin Ranar Hausa ta Duniya a ƙasashe sama da 20, ciki har da Faransa da Saudiyya.

Masu fafutukar wannan rana suna fatan cewa nan gaba za a amince da yaren Hausa a hukumance a ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da kuma ƙungiyar raya ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS).

Wane ci-gaba aka samu?

A wannan shekarar dai za a yi gagarumin bikin wannan rana a garin Daura da ke Jihar Katsina, wajen da ake kallo a matsayin tushen Hausa da al’ummar Hausawa. 

Za a yi tattaunawa da kuma nuna al’adu tare da mahalarta daga ƙasashe daban-daban a yammacin Afirka da kewaye.

Abdulbaƙi Aliyu Jari, wanda shi ne jagoran wannan taro na Ranar Hausa ta Duniya, ya shaida wa Aminiya cewa, a yanzu haka bincike ya ayyana harshen Hausa a matsayin yare na 11 da ake aka fi amfani da shi a faɗin duniya, kuma ana sa ran nan da shekarar 2050 zai zama na biyar a duniya. 

“Hausa ba kamar sauran yaruka ba ne da suke ɓacewa, Hausa na ƙara bunƙasa. Ana magana da yaren a nahiyar Afirka tsakanin mutane fiye da miliyan 170,” in ji shi.

Ya bayyana cewa, Hausa ya riga da ya samu gurbi na musamman a Jamhuriyar Nijar, inda kaso sama da 80 na al’ummarsu ƙasar suke magana da yaren, haka ma a ƙasar Ghana. Kafofin yaɗa labarai ma tuni suka rungumi harshen Hausa domin isar da saƙonninsu ga ɗimbin mabiya a faɗin duniya.

Jari ya ce, sun faro wannan lamari ne kamar wasa a shekarar 2015, amma sai ga shi yanzu duk duniya ana maganar sa. “Abu ne da aka faro a shafukan sada zumunta, sai ga shi yanzu ana bikin a ƙasashe kusan 25”.

A cewar Jari, Ranar Hausa ta Duniya, “Ba wai biki ba ce kawai, a’a, wata hanya ce da masu magana da harshen Hausa a duk faɗin Najeriya, Afirka ta Yamma da sauran ƙasashen duniya za su haɗa kai, su tattauna ƙalubalen da ke damun su da kuma samar da zaman lafiya.”

Da yake tsokaci kan nasarorin da aka samu a cikin shekaru goma da suka gabata, ya bayyana cewa a halin yanzu bikin ranar Hausa ya samu wani gurbi  a kalandar masu magana da harshen Hausa a duk duniya.

Jari ya yi kira ga gwamnatocin Afirka, musamman a Najeriya da Afirka ta Yamma, da su amince da Hausa a matsayin harshen ƙasa ko na yanki a hukumance, ta hanyar yin koyi da Jamhuriyar Nijar inda ake magana da Hausa a hukumance.

Hakan a cewarsa zai yara al’adu taro da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

Su wane ne Hausawa?

Ana kallon al’ummar Hausawa a matsayin ɗaya daga cikin ƙabilu masu muhimmanci a yammacin Afirka, da al’adunsu na musamman a faɗin nahiyar da ma sauran ƙasashen duniya. Yayin da wasu alƙaluma suka ce adadin Hausawa ya kai kimanin miliyan 150, Farfesa Muhammad Bunza na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sakkwato na ganin cewa adadin zai iya haura miliyan 500 idan aka haɗa da masu magana da yare biyu.

Ba a iya Najeriya ake samun al’ummar Hausawa ba, baya ga Nijar akwai ƙasashe irin su Saudiyya, Sudan, Maroko, Libya, da Mali, inda suke zuwa kasuwanci, ko kuma a kan haɗu ta dalilin auratayya.

A wata hira da BBC Hausa a shekarar 2023, Farfesa Bunza ya  bayyana cewa tsawon shekaru aru-aru, auratayya tsakanin ƙabilu da Hausawa ta sa su rikiɗewa zuwa ƙabila guda.

A yanzu dai, harshen Hausa yana cikin jerin harsunan da ake magana da su a duniya, inda wasu suka ce na bakwai a duniya, kuma yana ci gaba da samun karɓuwa. Amma duk da haka, Farfesa Bunza ya yi gargaɗin cewa harshen yana fuskantar ƙalubale, ciki har da ƙarancin koyar da shi a makarantu da rashin malamansa.

Ya buƙaci gwamnatocin Afirka da su haɓaka amfani da harshen, yana mai cewa, “Baya ga Swahili, babu wani yare na Afirka da zai iya yin gogayya da Hausa.

Yadda yaren Hausa ya bunƙasa

Masana harshe da dama na yi wa harshen Hausa kallon wani harshe mai yaɗuwa a faɗin duniya, inda yanzu haka nazarce-nazarce ke nuna cewa Hausa ne harshe na 11 a fadin duniya wajen yawan masu amfani da shi, kuma na ɗaya a Afirka ta yamma.

Sai dai akwai jayayya tsakanin manazarta kan girman Hausa a nahiyar Afirka, inda wasu ke ganin harshen Swahili da ake yi a ƙasashe da dama na yankin Afirka maso Gabas ya ɗara na Hausa wanda ake yi a yankin Afirka ta yamma da Afirka ta Tsakiya da ma kusurwar Afirka.

Sai dai nazarce-nazarce sun nuna harshen Hausa yana gaba da na Swahili ta fannin yawan masu yin amfani da shi inda shi kuma Swahili ke gaba wajen yawan ƙasashen da ake yin yaren.

Tuni dai manyan kafafe irin su Facebook da Google suke amfani da harshen Hausa inda tuni manhajar amfani ta Android da IOS suka shigar da shi cikin harsunan da suke amfani da su.

Ko a baya-bayan nan sai da hukumar Lafiya ta Duniya ta sanya Hausa a cikin harsuna guda uku da ta zaɓa domin yaki da annobar korona a Afirka.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hausawa Najeriya Ranar Hausa ta Duniya Ranar Hausa ta Duniya da harshen Hausa a faɗin duniya harshen Hausa a ranar Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa

Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.

 

A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwara ETF Ya Dauki Nauyin Karatun Fitattun Dalibai A Matakin Sakandare
  • Yawan Kadarorin Kamfanoni Mallakar Gwamnatin Sin Ya Wuce Yuan Triliyan 90 a Lokacin Shirin Raya Kasa Na 14 Na Shekaru 5 
  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara