Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Gudanar Da Hidima Ga Al’umma Daga Kowane Dan Kasa
Published: 25th, August 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Gudanar da hidima wa mutane aikin kowa ne
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa yi wa al’umma hidima aiki ne na kowa da kowa, yana mai bayanin cewa hadin kai da fahimtar juna kan kasa suna samun nasarar gudanar da mulki da tsayin daka wajen tunkarar makiya.
A yayin jawabin da ya gabatar a wajen bikin sabunta mubaya’ar Imam Khumaini (r.a) a hubbarensa mai tsarki da ke birnin Tehran, shugaban kasar Masar Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: “Aikin hadin kan jama’ar kasa ne yi wa al’umma hidima da nuna musu kauna, idan har za a iya tabbatar da adalci a cikin halayen al’umma, za a yi nasara wajen hidimtawa al’umma, kuma dukkan jami’ai za su zama bayin mutane.”
Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa yi wa jama’a hidima da sauraron muryoyinsu wani aiki ne na kowa da kowa. Ya yi imanin cewa, abin da zai iya cimma nasara shi ne hadin kai da fahimtar juna kan kasa, kuma duk wani abu da zai cutar da wannan hadin kan ba za a amince da shi ba. Ya bayyana cewa, idan aka samu hadin kai, makiya Amurka da gwamnatin sahayoniyya ba za su kuskura su kai hari ko wuce gona da iri kan kasar Iran ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Na Wurga Makiya Cikin Nadama August 25, 2025 Kafofin Watsa Labaran Isra’ila Sun Ce: Ba Za A Iya Hana Sojojin Yemen Kai Hare-Hare Kan Isra’ila Ba August 25, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Kai Hari Kan Kungiyar Red Crecent A Kasar Sudan August 25, 2025 Hamas: Da gangan Netanyahu ya dakatar da tattaunawar zaman lafiya August 25, 2025 Iran: Pezeshkian ya yaba da kalaman Jagora Kan hadin kan al’umma August 25, 2025 Isra’ila ta kai hari kan ababen more rayuwa na fararen hula a Yemen August 25, 2025 Araqchi ya isa Saudiyya don halartar taron gaggawa na OIC a kan Gaza August 25, 2025 Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Zama Mai Biyayya Ga Amurka Ba August 24, 2025 An Gudanar Da Tarukan Makoki Shahadar Imam Ridha (AS) A Hubbarensa Da Ke Mashhad August 24, 2025 Aragchi: Batun ‘Isra’ila Babba” Mafarki ne Kuma Barazana Ce Ga Zaman Lafiya A Duniya August 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin fara amfani da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa da Allah SWT ya hore ma ta da nufin haɓaka tattalin arzikinta tare da samarwa al’umma aikin yi.
A yayin ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na Jihar da aka yi a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu, Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya ce kamfanin haɓaka ma’adanai ta Yobe Limited ita ce kawai hukumar da aka bai wa izini don gudanar da duk ayyukan bincike da haƙar ma’adinai a faɗin jihar.
Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFAYana mai cewa, kamfanin haƙar ma’adinai na Yobe a halin yanzu shi ne, ƙashin bayan da zai samarwa Jihar hanyoyin dogaro.
“Jihar Yobe tana da wadataccen albarkatun ma’adinai kamar: Limestone, gypsum, kaolin, granite, Quartz, silica da sauran su duk da haka, tsawon shekaru da yawa, waɗannan ma’adinai sun kasance ba a amfani da su sosai kuma a yanzu lokaci ya yi da za a mayar da waɗannan ma’adinai da aka ɓoye zuwa kadarorin da za su samar da ayyukan yi, samar da wadata da kuma ciyar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na mutanenmu gaba ɗaya.”
“Manufarmu ita ce tsara wani tsari don ci gaban fannin haƙar ma’adinai a Jihar Yobe ta hanyar da ta dace da manufofin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da haɗa kan al’umma, jawo hankalin masu zuba jari masu aminci da kuma tabbatar da alhakin gyara muhalli.
“kuma mun yi imanin cewa haƙar ma’adinai idan aka sarrafa shi yadda ya kamata, zai iya zama babban abin da ke haifar da juriyar tattalin arzikin jiharmu, samar da aikin yi ga matasa da kuma samar da kuɗaɗen shiga.”
“Muna hasashen samar da fannin haƙar ma’adinai wanda zai iya aiki a cikin tsarin dokoki, wanda ke tabbatar da ɗorewar muhalli da fa’idar al’umma; wanda ke haɗaka da haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu waɗanda aka amince da riƙon amana; wanda ke jawo hankalin masu zuba jari na ƙasashen waje.” Cewar Gwamna Buni.