HausaTv:
2025-11-03@07:20:55 GMT

Makami Mai Linzami Daga Yemen Ya Tashi Jiniyar Gargadi A Garuruwa 300 Na HKI

Published: 1st, June 2025 GMT

Sa’oi kadai da su ka gabata jiniyar gargadi ta kada a cikin garuruwa da sansanonin ‘yan share wuri zauna 300 a HKI saboda  makami mai linzami da mutane Yemen su ka harba.

 Kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniya sun ambaci cewa; an rufe filin saukar jiragen saman a “Ben Gorion” da kuma dakatar da kai da komowar jiragen sama.

Kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa; Miliyoyin mutane ne su ka gudu zuwa Mabuya.

Wannan sabon harin dai na sojojin Yemen yana zuwa ne a karkashin abinda sojojin na Yemen su ka kira, kakaba takunkumi na sama da ruwa akan HKI, tare da yin kira ga kamfanonin jiragen sama da na ruwa da su kauracewa zuwa wannan haramtacciyar kasa.

Filin saukar jiragen sama na Ben Gorion’ da tashoshin  jiragen ruwa ta Haifa da Eiliat su ne wadanda takunkumin na sojojin Yamen ya fi shafa.

 Kwanaki kadan da su ka gabata jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya sanar da cewa, ba za su daina kai wa HKI hare-hare, har sai idan sun kawo karshen yakin Gaza da kuma killace yankin da aka yi.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: jiragen sama

এছাড়াও পড়ুন:

Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC

Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.

A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.

Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”

Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.

Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.

Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.

Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.

Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”

“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”

Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.

Daniel Karlmax

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC
  • NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi