HausaTv:
2025-11-02@20:54:36 GMT

 Iran  Ce Ta Farko A Duniya Wajen Dashen Koda

Published: 1st, June 2025 GMT

Mataimakin shugaban kungiyar Iraniyawa masu bayar da kyautar gabban jikinsu ga mabukata, Umid Qabadi, ya bayyana cewa; A cikin shekaru 25 da su ka gabata, yadda ake kyautar gabban jiki domin yin dashe a duniya ya karu da kaso 70%, kuma Iran ce ta farko wajen yin dashen koda, har ma ana yi ma ta kirari da; Sarauniyar dashen koda.

A yayin wani taro na girmama masu bayar da kyautar gabban jikin nasu domin yi dashe ga mabukata a gundunar Qazwin, mataimakin shugaban kungiyar Umid Qabadi ya ce; Iran ce ta farko a duniya wajen yin dashen gabobi ga marasa lafiya mabukata.

Qabadi ya yi ishara da wajabci ganin an bunkasa wannan al’ada ta bayar da gabobin jiki domin yin dashe saboda a ceto da rayukar mutane, yana mai kara da cewa; A gundumar Qazawin a shekarar da ta gabata, mutane 12 sun bayar da kyautar gabobin jikinsu ga mabukata. Amma a cikin watanni biyu na wannan shekarar kadai, an sami mutane bakwai da su ka bayar da kyautar gabobin jikin nasu ga mabukata.”

Har ila yau, mataimakin shugaban kungiyar masu bayar da gabobin jikin nasu ga mabukata ya ambaci cewa; An kafa wani tsari a Iran na yin jigila ta sama ta marasa lafiya da suke da bukatar a yi musu dashe, zuwa wasu gundumomi na kasar.

Qabadi ya ambaci cewa; A shekarar 1989 ne wanda ya assasa jamhuriyar musulunci ta Iran, Imam Khumaini ( QS) ya bayar da fatawar halarta bayar da gabobin jiki domin ceto da marasa lafiya mabukata, daga wadanda su ka rasu ta hanyar bugun kwakwalwa.” Qabani ya bayyana wanann fatawar a matsayin daya daga cikin muhimman ci gaban da juyin musulunci ya samar.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: bayar da kyautar

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.

Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen  tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti