SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (3)
Published: 1st, June 2025 GMT
Yanzu haka, akalla ana iya karbar sama da Naira miliyan 100 daga wannan PAYE a kowane wata. Wasu hanyoyin samun kudaden shiga, sun hada da haya na kasa (ground rent), harajin haya (tenement rate), da harajin wuraren kasuwanci. Har ma da noma, ana sa wa haraji a Suleja, duk da cewa; gwamnan jihar manomi ne.
Idan har gwamnatin tarayya ba ta yaba da sadaukarwar da Suleja ta yi ba, to akalla Gwamnatin Jihar Neja; ya kamata ta fi mayar da hankali wajen samar da ci gaba a Suleja, domin karrama gudunmawar da garin ke bayarwa wajen samun kudaden shiga ga jihar. Har ila yau, adalci ne a dawo da abin da aka karba ta hanyar ayyuka ga al’umma.
Tsohon Gwamna, Babangida Aliyu ya ce; gwamnatinsa ta gina titin cikin gari na kilomita 10 a kowace karamar hukuma. Amma ba a kai wa Suleja kilomita uku ba. Titin Gwazunu da aka ce an gyara, bai kai shekara biyu ba ya lalace. Aliyu kuma ya zo da burin aikin Twin City, ciki har da aikin titin Madalla mai layi biyu, a cikin bashi da aka fito da shi. Amma aikin da bashin duk sun bace bat kamar iska.
Gwamnatin yanzu ta sanar da shirin samar da tituna na tsawon kilomita 50 a kowanne daga cikin garuruwa uku: Bida, Kontagora da kuma Suleja. An kaddamar da aikin a sauran wuraren amma ban da Suleja ba.
Watakila aikin titin da aka fara shi ne, wanda ake gina magudanan ruwa marasa inganci a gefen titin Maje zuwa Madalla da kuma hanyar Kaduna. Wannan abin takaici ne. Abu mafi muni shi ne, tsoffin magudanan ruwa da Gwamna Kure ya gina fiye da shekaru 20 da suka wuce, wadanda yanzu ake maye gurbinsu, sun fi wadanda ake ginawa yanzu inganci.
Titin Maje zuwa Madalla na daga cikin manyan titunan tarayya, ‘Trunk A-124’. Ma’ana, gwamnatin jiha, na sa ran gwamnatin tarayya za ta biya su bayan shekara 10. Amma ta yaya aiki marar inganci irin haka zai cancanci a biya kudinsa? Idan har gwamnatin yanzu ta ki gyarawa, ta ci gaba da biyan kwangilar wanda ko sunansa ba a so a sani, duk da gurbataccen aikin da korafi masu yawa, hakan yana nuna cewa; abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne kudi, ba aiki ko jin dadin jama’a ba. haka zalika kuma, wannan gwamnatin ba ta damu da matsalolin da za su bar wa gwamnati mai zuwa ba.
Masu gidaje, yawancinsu ‘yan asalin garin wadanda aikin ke shirin shafar su ne, don haka dole ne a biya su diyya tare da sake musu matsugunai. Amma har yanzu, babu wani shiri na sake matsugunan ko kididdigar diyya da aka sanar a Suleja. Amma an gudanar da hakan a wasu al’ummomi a cikin jihar.
Babu shakka, ikon gwamnati ya shafi dukkanin Jihar Neja, ba Suleja kadai ba. Amma Hassan da Hussaini duka suna da hakkin da ya caccanta a ba su. Sai dai, ba dai-dai ba ne a tauye hakkin Hassan don a amfanar da Hussaini. A bayyane yake karara, inda ake samun kudin shiga a Jihar Neja, ba can ake yi da su ba. A gaggauta gyara tunda lokaci bai kure ba.
Alhamdulillah!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
Ya ce ya dinga ƙorafi ne domin gwamnatin Buhari ba ta ɗauki matakin da ya dace ba game da kashe-kashen da ake yi a Benuwe.
“Ba zan iya zama na yi shiru ina ci gaba da binne mutane ba. Dole ne na faɗi gaskiya,” in ji shi.
“Amma ban tsaya a magana kawai ba, gwamnatina ta kawo hanyoyin magance matsalar da muka ga za su taimaka.”
Ortom ya ƙara da cewa da gwamnatin Buhari ta karɓi shawararsa kuma ta yi aiki da ita, da matsalar tsaro a Benuwe ta ƙare.
Ya ce ya sha kokawa a lokacin, kuma shirye-shiryen da gwamnati ta kawo kamar Ruga ba su da amfani.
Ya ce ba wai rikici ne tsakanin makiyaya da manoma kawai ba, wasu daga cikin makiyaya suna kai wa ƙauyuka hari, suna kashe mutane, lalata gonaki, yi wa mata fyaɗe da aikata wasu laifuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp