An gano shanu 25 da suka ɓace a dajin Sakkwato
Published: 3rd, May 2025 GMT
Hedikwatar ’yan sandan Gada da ke Jihar Sakkwato ta gano wasu shanu 25 da ake zargin an sace ko kuma sun ɓace daga hannun masu su.
An gano dabbobin ne a wani dajin da ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar a ranar Alhamis, bayan da hukumomin yankin suka samu labarin.
’Yan kungiyar asiri: Mutum 95 sun shiga hannu a Edo Shettima zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar GabonJami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmad Rufa’i ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, inda ya ce an gano dabbobin ne bayan da Alhaji Muhammad Kyari ya bayar da rahoton cewa akwai shanun da suka ɓace.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hakimin Gada, Alhaji Idi ‘M, tsohon Hakimin garin Gidan Rabami da ke ƙaramar Hukumar Gada, a baya ya sanar da hukuma game da wasu baƙin shanu a wani dajin da ke kusa.
“An gano dabbobin ne a wani dajin da ke da iyaka da ƙaramar hukumar Sabon Birni, yankin da ya shahara da sarƙaƙiya da kuma ƙalubalen tsaro a wasu lokuta.
“Rundunar ’yan sanda ta Gada ta mayar da martani cikin gaggawa, inda ta tura jami’anta zuwa wurin da aka yi nasarar ƙwato shanu 25 ba tare da wata matsala ba.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, bayan kuɓutar da su an kai shanun zuwa hedikwatar Gada, inda ake tsare da su cikin ƙoshin lafiya.
Rundunar ’yan sandan ta yi kira ga masu dabbobin da suka rasa shanunsu da su ziyarci hedikwatar tare da ingantacciyar hujjar mallakar su domin tantancewa tare karɓarsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Barayin Shanu jihar Sokoto
এছাড়াও পড়ুন:
Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn N70.4bn domin inganta kiwon lafiya
Bankin Raya Ci-gaban Afirka (AfDB) ya amince da ba wa Gwamnatin Jihar Sakkwato bashin Naira biliyan 70.4 domin inganta fannin kiwon lafiya.
Wannan shiri na da nufin bunƙasa fannin kiwon lafiya da ingancinsa, da kuma cike giɓin da ake da shi a ɓangaren a Jihar Sakkwato, a cewar AfDB ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.
Rahotanni na nuni da cewa, yaro ɗaya cikin kowane yara 20 ne akale yi wa allurar rigakafi cikakke a Jihar Sakkwato a, a yayin da adadin mutuwar jarirai ya kai 104 daga cikin 1,000 a Jihar.
Ƙasa da kashi 14 cikin 100 na cibiyoyin lafiya a jihar ne suke da kayan aiki masu aiki, kuma likita ɗaya ne kawai ke kula da mutum 8,285, wanda ya gaza abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar na likita 1 ga 1,000 mutum.
Har yanzu ana fama da cutar kwalara a Najeriya – UNICEF PDP ta mutu murus a Kano — Shugaban NNPPKuɗaɗen da bankin ya ware za su tallafa wa samar kayan aikin kula da lafiya masu inganci a matakai uku na kula da lafiya a Jihar Sakkwato.
Wannan ya haɗa da gina sabon asibitin koyarwa mai gado 1,000, da manyan asibitoci na yankuna uku masu jimillar gadaje 450, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya guda shida da aka tsara a domin kuka da al’ummomin karkara.
Aikin ya kuma haɗa da gyaran cibiyoyin horar da ma’aikatan lafiya da ƙirƙirar sabon ma’ajiyar magunguna ta zamani.
Darakta-Janar na Ofishin AfDB a Najeriya, Abdul Kamara, ya ce, “Wannan rancen na nuna yadda muke jajircewa wajen aiki tare da gwamnati don magance giɓin kayan kiwon lafiya a Najeriya, tare da gina cibiyoyin kula da lafiya masu ƙarfi da suka dace da tsari na yanayi.
“Ta hanyar ƙarfafa kayan aikin lafiya a Jihar Sakkwato, muna gina fata da hanyoyin samun kyakkyawan sakamako ga miliyoyin ’yan Najeriya.”