Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka
Published: 23rd, April 2025 GMT
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025.
Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da ya jagoranci membobin hukumar ta NAHCON domin gabatar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025.
Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ke sa ido kan ayyukan NAHCON, kuma Hukumar ta shaida wa Sanata Kashim Shettima cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin fara aikin Hajjin 2025 da jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 9 ga Mayu, 2025.
A nasa jawabin bayan ganawar, Kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka, Prince Anofi Elegushi ya bayyana cewa an riga an kammala shirye-shirye a Makka, Madina da sauran wurare domin gudanar da aikin Hajji cikin sauki.
Ya ce, “Mun tanadi masaukai a Makka, da Madina da sauran wurare, an kuma shirya su domin tarɓar mahajjatanmu, inda muka samu isassun gadajen, tare da biyan kuɗin abinci mai kyau kuma isasshe ga dukkan mahajjata. Mun zaɓi ranar 9 ga watan Mayu domin tashin jirgin farko zuwa Madina, muna kuma fatan kammala jigilar zuwa Saudiyya kafin ranar 24 ga watan Mayu, kuma mu fara dawo da mahajjata daga ranar 13 ga Yuni har zuwa 2 ga Yuli.”
A jawabinsa tun da farko, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bukaci Hukumar da ta tabbatar da cewa kowa yana bakin kokarinsa domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana.
“Ya zama wajibi a dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin 2025. Wannan nauyi ne a kanmu ga ‘yan Najeriya da mahajjata, domin mu tabbatar da aikin Hajji mai inganci.” In ji shi
Safiyah Abdulkadir
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Mataimakin Shugaban Ƙasa shirye shirye tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Ware Yuan Biliyan 10 Don Shirye-Shiryen Ba Da Tallafin Aiki
A yau Talata, hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC) ta sanar da cewa, ta ware karin kudi yuan biliyan 10, kimanin dalar Amurka biliyan 1.4, a cikin asusun kasafin kudi na gwamnatin tsakiya, don karfafa rawar da shirye-shiryen ba da tallafin ayyukan yi ke takawa wajen bunkasa daukar aiki da karuwar kudin shiga ga manyan kamfanoni.
Kudaden za su tallafa wa yankuna na lardi 26, da kungiyar masana’antu da gine-gine ta Xinjiang wajen aiwatar da ayyuka 1,975, wadanda ake sa ran za su samar da jimillar kudi yuan biliyan 4.59 a matsayin albashin ma’aikata, tare da taimaka wa muhimman mutane 310,000 wajen daidaita ayyukansu da kuma kara samun kudin shiga. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp