Amurka Na Shirin Rufe Ofisoshin Jakadancinta Kimani 30 A Duniya
Published: 18th, April 2025 GMT
Gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancinta har kimani 30 a kasashen duniya, amma mafi yawansu a kasashen Afirka.
Shafin yanar gizo na labarai Afrika News ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurkan na fadar cewa gwamnatin shugaban Trump tana son ta rage yawan kashe kudade a ma’aikatar don amfani da su a cikin gida.
Labarin ya kara da cewa gwamnatin tana son rage kudaden da ma’aikatar take kashewa a kan ofisoshin jakadunsu da kasha 50% da kuma rage tallafin da take bawa wasu kungiyoyi a wadan nan kasashe har da kasha 75%.
Labarin ya kara da cewa kasashen da shirin ya shafa dai akwai Lesotho, Eritrea, Afrika ta tsakiya, Congo Brazavile, Gambia, Sudan ta kudu,. Banda wadannan za’a rufe kananan ofisoshin jakadanci da ke birnin Durban na Afrika ta kudu, da kuma na Douala, da ke kasar Cameroon. Labarin yace ayyukan wadannan ofisoshin jakadanci zasu kuma ga kasashe makobta.
A kasahen turai da Asiya kuma Amurka zata rufe ofisoshin jakadancinta a tsibirin Malta, Luxembourg, da kuma wasu kananan ofisoshin jakadancin kasar a tarayyar Turai da Asiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba.
A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”
Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”
Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.
Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.
A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.