Yadda Hukuncin Kotun Koli Ya Kara Dagula Rikicin Shugabanci A PDP Da LP
Published: 19th, April 2025 GMT
Wata majiya ta ce PDP na cikin mawuyacin hali da kuma rashin tabbas a harkokinta wanda ya tilasta jinkirta taron shiyya da aka shirya gudanarwa a karshen makon da ya gabata.
Wata majiya ta ce hukuncin da kotun koli ta zartar akwai rikitarwa saboda an gwama siyasa a ciki.
Amma sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fada a wata hira kan cewa hukuncin kotun koli a bayyane yake kuma yana da fa’ida ga gudanar da jam’iyyar a kasar, ya kara da cewa an ba da ikon magance matsalolin da ke tattare da rikice-rikicen da za su iya shafi masu rike da mukaman jam’iyyar.
Ya ce abin da kotun ta yanke hukunci shi ne cewa dole ne a warware duk wani abu da ya shafi matsayi na jam’iyya ta hanyar tsarin cikin gida na jam’iyya, sannan kotun ta ce ba za ta yi katsalandan ga al’amuran jam’iyyu ba kamar yadda dokoki da ka’idoji suka bayyana.
Ya ce PDP ba ta cikin wani mawuyacin hali game da hukuncin, ya kara da cewa tsarin cikin gida na jam’iyyar zai yanke shawara tare da samar da mafita.
Yayin da PDP tana cikin mawuyacin hali saboda jinkirin warware matsayin sakataren jam’iyyar na kasa, al’amura na kara tabarbarewa a LP. A makon da ya gabata ne bangare uku suke ikirarin zama shugabannin jam’iyyar na kasa.
Julius Abure, Nenadi Usman da Lamidi Apapa sun ci gaba ikirarinsu na zama a matsayin shugabancin jam’iyyar, duk da cewa sakataren yada labarai na kasa, Obiora Ifoh, ya bayyana cewa wadanda ke fafatawa da Abure suna yin was an kwaikoyo ne kawai.
A cewarsa, a yayin da kotun koli ta fadi karara cewa ba ta da iko a kan lamarin da ya shafi rikicin cikin gida na jam’iyya kuma ta mayar da iko ga tsarin jam’iyyar, wasu mambobin jam’iyyar suna yin wasan kwaikwayo ta hanyar zuwa ofishin hukumar zabe ta kasa, lamarin da ya ce ba shi da tasiri.
Ya ce hukuncin kotun koli ya yi watsi da batun shugabancin jam’iyyar tare da soke hukuncin kotun daukaka kara, har ma ba ta tabbatar da wani mutum a matsayin shugaban jam’iyyar ba.
“Abin da wannan ke nufi shi ne, an mayar da jam’iyyar zuwa matsayi na farko. Kuma Abure ya kasance shugaban jam’iyyar na kasa har tsawon lokacin da wa’adinsa ya kare,” in ji Ifoh.
Mai magana da yawun jam’iyyar ya gargadin Sanata Nenadi Usman da sauran masu adawa da Abure cewa kar su yaudari ‘yan Nijeriya da fassarar da ba daidai ba game da hukuncin kotun koli.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Dan Takarar Gwamnan PDP
এছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da aniyar ta ta bunƙasa harkar kiwon dabbobi a Nijeriya a matsayin wata muhimmiyar hanya ta magance rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, tare da amfani da damar tattalin arzikin da ke cikin ɓangaren.
Ɗaya daga cikin Shugabannin Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Harkar Kiwo, Farfesa Attahiru Jega, shi ne ya bayyana hakan a wurin taron tattaunawa tsakanin gwamnati da ‘yan ƙasa, wanda Gidauniyar Sa Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna, a ranar Laraba.
Wasan Kwallon Mutum-Mutumi Ya Nuna Yadda Sin Ta Shirya Wa Karbar Bakuncin Wasanninsu Na Duniya Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyarJega ya bayyana cewa sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo tana ɗaya daga cikin ginshiƙan da ke cikin shirin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na sauya fasalin ɓangaren kiwon dabbobi.
Ya jaddada cewa ana aiwatar da hangen nesa na Shugaban Ƙasa ba tare da son rai na siyasa ba, tare da mayar da hankali kan haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnatocin jihohi, sarakunan gargajiya, al’ummomin makiyaya da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp