Aminiya:
2025-07-04@00:21:34 GMT

’Yan adawa sun zama kyanwar Lami duk da rinjayensu a Majalisa

Published: 13th, April 2025 GMT

Nan da wata biyu Majalisar Dokoki ta Kasa ta 10 za ta cika shekara biyu, rabin wa’adinta, da fara aiki a matsayin ɓangaren da ke kafa dokoki da kuma saita ɓangaren zartarwa domin yin daidai a bisa tsarin dimokuradiyyar Nijeriya.

’Yan kasar da dama na ganin wannan muhimmin ɓangare ya zama dan amshin shata ga ɓangaren zantarwa na Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu.

Amurka ta janye harajin kayan laturoni da ake shiga da su ƙasar Mutum ɗaya ya mutu a faɗan ƙungiyar asiri a Maiduguri

Hakan dai ya ci karo da yadda aka yi hasashe a lokacin da aka kaddamar da ’yan majalisar su sama da 460 domin fara aikinsu na wakilcin ’yan Nijeriya sama da miliyan 230 a zaurukanta biyu.

Bisa la’akari da yawa da kuma rinjayen da ’yan adawa ke da shi a kan ’yan jami’iyya mai mulki a zauren majalisun biyu, na dattawa da na wakilai, a lokacin, ’yan Najeriya sun sa ran ganin zafafan mahawarori da sauran nau’ukan adawa da za su sa bangaren gwamnati da jam’iyya mai mulki yin kaffa-kaffa a duk wani motsi da tsare-tsarensu.

Wannan kuwa na faruwa ne duk da cewa a wannan karon jimillar ’yan adawa sun kafa tarihin samun rinjaye a zauruka biyu na majalisar, Wakilai da Dattawa, idan aka kwatanta da ’yan jam’iyya mai mulki ta APC.

A lokacin da majalisar ta fara aiki a watan Mayu na shekara ta 2023, ’yan adawa da ke rinjaye a Majalisar Wakilai da jimillar mambobi 182, adadin da ya dara na jam’iyya mai mulki ta APC mai mutum 175.

Babbar jam’iyyar adawa, PDP, kadai a lokacin tana da mutum 118, sai Jamiyyar Labour da ke bin ta da wakilai 35, sai NNPP mai mutum da 19, a yayin da ragowar kananan jam’iyyun adawa da ke da wakilai 10.

Koda yake har yanzu Jam’iyyar APC mai mulki ce ke da rinjaye a Majalisar Dattawa da mabobi 59, amma jam’iyyun adawa na da jimillar sanatoci 50.

’Yan Nijeriya da dama sun yi zaton cewa wannan adadi na ’yan jam’iyyun adawa a Majalisar Dokoki ta Kasa, zai samar da hamayya mai zafi da kuma ma’ana, ta yadda za su rika taka wa gwamnati burki tare da tilasta mata yin abin da ya dace, a maimakon barin ta tana yin kama karya ko yadda ga dama.

Sai dai tun ba a je ko’in ba, ’yan adawan suka fara nuna gazawa inda suka kasa samar da shugabannin zaurukan majalisun biyu daga cikinsu, alhali da farko sun lashi takobin amfani da rinjayen nasu domin cim ma wannan buri.

Gabanin zaɓen shugabannnin, ’yan majalisar daga bangaren jam’iyyun adawa sun yi ta gudanar da taruka karkashin wata kungiyarsu da suka sa wa suna “Greater Majority” inda masu neman shugabancin daga bangarensu da ma na jam’iyya mai mulki suka rika zawarcin goyon bayansu.

Amma a ƙarshe bayan kammala zaɓen jagorori a zaurukan biyu, ’yan takarar da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu yake goyon bayan daga APC ne suka kai bantensu, inda Sanata Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattijai, shi kuma Honorabul Abbas Tajudden ya zama Shugaban Majalisar Wakilai.

Saunyin shekar ’yan adawa zuwa APC

Daga wancan lokacin zuwa yanzu kuma adadin ’yan jam’iyyun adawan ya rika raguwa, sakamakon sauya sheka da wasusu suka rika yi zuwa APC, lamarin da ya sa zuwa yanzu PDP kadai ta rasa mamobi 30 da suka tsallaka suka koma APC a Majalisar Wakilai, Jam’iyyar Labour kuma ta rasa mambobi shida.

Zuwa yanzu dai, babu wani dan Jam’yyar NNNPP da ya sauya sheka, sai dai rabuwar kai da aka samu a babbar cibiyarta, wato Jihar Kano inda jam’iyyar ta sanar da korar daya daga cikin ’ya’yanta, shi kuma ya ce bai koru ba.

A Majalisar Dattawa, Jam’iyyar PDP ta rasa daya daga cikin fitattun ’ya’yanta, Sanata Ned Nwoko ga APC.

Wadannan sauye-sauyen sheƙa da jam’iyyun adawa suka fuskanta ya raunata karfinsu kataɓus ɗinsu.

Majalisa ta 10: ’Yan adawa sun zama kyanwar Lami

Sai dai masu hasashe na ganin cewa kimanin shekara biyu da farawar majalisar ta goma, amma ta rasa muryata ta zama ’yar sa ido tare da tabbatar da cewa gwamnati mai ci tana yi abin da ya dace ga al’ummar Nijeriya.

Amma ana gabin abubuwa da dama da suka faru musamman a baya-bayan a matsayin alamar da ke nuna ’yan adawa a Majalisar sun gaza yin abin da ya dace.

Na karshe-karshen shi ne yadda ’yan majalisar suka amince da da ayyana dokar ta-baci da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a Jihar Ribas.

Ganin yananin rudanin da ya dabaibaye matakin, ’yan Nijeriya da dama sun yi zaton cewa musamman ’yan hamayyar za su yi amfani da rinjayensu su taka wa Tinubu burki, kan yadda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa da kuma ’yan majlisar dokokin jihar Ribas na tsawon wata shida, waɗanda ’yan jam’iyyar PDP ne, alhali dokar kasa ce ta zabe su.

Amma sai ga shi ’yan majalisar sun yi amfani da tsarin kuri’a na murya suka tabbatar da matakin na shugaban kasa da ke bukatar kashi biyu bisa ukun ’yan majalisa a dokance.

A ɓangaren Majalisar Wakilai dai an ruwaito cewa wasu mambobi biyu sun yi yunkurin hana lamarin, inda suka dage cewa adadin ’yan majalisar da suka samu halartar zaman bai kai kashi biyu bisa uku ba, kamar yadda tsarin zauren ya amince, amma ba su kai labari ba.

Rashin katabus da ’yan majalisar suka yi a kan lamarin ya bar al’umma da dama cike da mamaki.

A Majalisar Dattawa kuma sanatoci uku ne suka nuna adawarsu a kan lamarin a lokacin kada kuri’ar muryar — Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Seriaki Dickson da Sanata Eyinnaya Abaribe —, ko da yake kokarin nasu bai yi tasiri ba, aka yi watsi da matsayarsu.

A ƙarshe Sanata Dickson ya fice daga zauren majalisar don nuna bacin rai a kan matakin, lamarin shi ma ya tabbatar da cewa ’yan adawan sun koma abin nan da ake cewa ‘magen Lami’.

Baya ga badakalar amincewa da dokar-ta-bacin, an kuma zargi ’yan majalisar adawan da rikidewa da zama ’yan amshin shata wajen amincewa da duk bukatun da bangaren zartarwa ya bijiro wa majalisar ba tare da kwakkaran bincike a kai ba.

Misali, shi ne yadda ’yan majisar ke amincewa da bukatar karbo bashi da gwamnati ke gabatar masu, sai kuma kwaryakwaryan kasafi da kuma kashe-kashen kudi da kuma dokokin da aka hakikance da cewa ba su da nasaba da bukatun al’ummar kasa.

Tambayar da ake ta yi ita ce, shin ina adawar ’yan jam’iyyun adawa a Majalisar Dokoki ta Kasa karo na 10?

Siyasa jari hujja ta kashe adawa a Majalisa — Rafsanjani

Ɗan Rajin Kare Hakkin Jama’a kuma Shugaban Kungiyar CISLAC a Nijeriya, Malam Auwal Musa Rafsanjani ya danganta dakushewar adawa a Majalisar Dattawa ta 10 da hali na jari hujja a tsakanin yawancin ’yan siyasa.

Ya bayyana cewa hakan ne ya sa suke fifita buƙatar abin da za su sama wa aljihunsu fiye da kare manufofin da suka dace.

Rafsanjani ya ce, ’yan majalisa daga ɓangaren adawa sun zama tamkar ’yan amshin shata saboda burace-burace na kuɗi a maimakon tsayawa kan gaskiya.

“Jamiyyun siyasa da ke mulki ko bangaren adawa sun rasa ikonsu na yin aiki bisa ka’ida ta jam’iyya. Za ka samu ko dai ana musu zagon kasa, ko kuma su ke yi wa kansu zagon kasan,” in ji shi.

Shugaban na CISLAC ya ce, tun daga wajen zaben tsayar da ’yan takara ake kauce layi inda ake tsayar da dan takara bisa nauyin aljihunsa, a maimakon lura da cancanta ta kwarewar aiki ko halin nagarta, da kuma girman sha’awarsa ga yin aiki wa al’umma.”

Ya kuma ce aikin majalisa na fuskantar cikas a sakamakon yadda ya koma tamkar na kashemu-raba, inda bangaren zartarwa ke ba da kudi a kan wani kuduri da ake bukatar ’yan majalisar su amince da shi bisa halin ko kaka.

“Ya kamata ’yan adawa su rika sa ido wajen gudanar da aikin gwamnati, amma sabanin haka duk abin da gwamnati mai ci ta gabatar, ’yan adawa amincewa kawai suke yi,” in ji Rafsanjani.

Ya bukaci samar da sauyi a tsarin gudanar da siyasar kasar nan tare da bukatar fifita cancanta da kuma kyawawan manufofi a kan yawan kudi na dan takara a yayin zaben fidda gwani.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Adawa Majalisar Dattawa Majalisar Dokokin Tarayya Majalisar Wakilai A Majalisar Dattawa a Majalisar Dattawa jam iyya mai mulki adawa a Majalisar Majalisar Wakilai majalisar Wakilai yan majalisar su majalisar da yan adawa su A ɓangaren

এছাড়াও পড়ুন:

David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya fice daga jam’iyyar adawa ta PDP.

A cikin wata wasiƙar da Aminiya ta gani, David Mark ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda rikice-rikicen shugabanci da aka gaza magancewa.

Najeriya ta kammala dawo da alhazan da suka yi Aikin Hajjin bana Kotu ta yanke hukuncin rataya ga dalibin da ya kashe malaminsa a Jos

Ya ce waɗannan matsalolin sun kawo wa jam’iyyar naƙaso kuma sun jawo mata abun kunya a idon jama’a.

A daren ranar Talata, an naɗa David Mark da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugabannin riƙon kwarya (Shugaba da Sakatare) na wata sabuwar jam’iyyar ADC.

Wannan jam’iyya wadda ta haɗa manyan ’yan adawa na da niyyar ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

A wasiƙarsa, Mark ya ce: “Na tsaya tsayin daka a PDP tun daɗewa, har lokacin da wasu suka bar jam’iyyar bayan faɗuwa zaɓen 2015.

“Amma yanzu jam’iyyar ta lalace, ba ta da tasiri ko haɗin kai. Bayan yanke shawara da iyalina da abokan siyasa, na yanke shawarar shiga sabuwar haɗakar siyasa domin ceto dimokuraɗiyya.”

Sabuwar haɗakar siyasar ta ce za ta ƙalubalanci Tinubu a zaɓe mai zuwa domin ƙwace mulki daga hannunsa.

Amma jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba ta jin tsoron haɗakar da manyan ’yan adawa ke yi.

Muƙaddashin Shugaban jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya shaida wa BBC cewa babu wanda ke yin magana a kan wannan haɗaka sai a Abuja.

Ya ce: “Ba mu damu da wannan haɗaka ba. APC jam’iyya ce da mutane ke so. Sabuwar haɗaka ba ta da abin da za ta bai wa jama’a.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Jigawa Ta Isa Roni A Ci Gaba Da Rangadin Kananan Hukumomi
  • Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa ‘Yan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa Yahudawan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • ’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC
  • ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’
  • Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
  • David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu
  • Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma
  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila