Tsofaffin Ma’aikatan FRCN Za Su Gudanar da Zanga-zanga Kan Jinkirin Biyan Hakkokin Su
Published: 8th, April 2025 GMT
Kungiyar Tsofaffin Ma’aikatan Hukumar Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) ta Umarci Mambobinta a Fadin Kasa da Su Gudanar da Zanga-zanga Kan Jinkirin Biyan Kudin Fansa da Aka Yi Alkawari Tsawon Shekaru.
A cikin wata sanarwa, kungiyar ta bayyana cewa zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba na da nufin jawo hankalin hukumomi masu ruwa da tsaki kan kalubalen da tsofaffin ma’aikata ke fuskanta.
Ana sa ran zanga-zangar za ta fara ne a hedikwatar Gidan Rediyon Najeriya da ke Abuja da misalin karfe goma na safe, sannan ta ci gaba zuwa wasu wurare cikin lumana, yayin da masu shirya zanga-zangar suka bukaci a tabbatar da cikakken daukar rahoton al’amarin daga kafafen yada labarai.
Jagororin zanga-zangar sun nuna rashin jin dadinsu kan zargin gaza biyan kudaden fansa daga Hukumar Tsare-tsaren Biyan Fansho (PTAD), duk da cewa an ce an amince da biliyoyin naira domin biyan su.
Wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan da suka nuna goyon baya ga zanga-zangar sun bayyana mamaki kan irin shiru da kungiyar FRCN na kasa ke yi game da wannan batu mai matukar muhimmanci, wanda bai kamata a ci gaba da dauka da wasa ba, musamman ganin halin kuncin da masu ritaya ke ciki.
Suleiman Kaura
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp