Kasar Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje Kan Wasu Ma’adinan Da Ba Kasafai Ake Samun Su Ba
Published: 4th, April 2025 GMT
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin tare da hadin gwiwar babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta sanar a yau Juma’a cewa, za ta fara aiwatar da matakan kiyaye fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kan nau’o’in ma’adinai bakwai matsakaita da masu nauyi da ba kasafai ake samun su, wadanda suka hada da samarium, gadolinium, terbium, dysprosium, lutetium, scandium da yttrium.
Har ila yau, ma’aikatar ta sanar cewa, ta yanke shawarar kara wasu kamfanonin Amurka 16 da ke barazana ga tsaron kasa da moriyarta a cikin jerin sunayen kamfanonin da ta dauki matakin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kansu, tare da sanya kamfanonin Amurka 11 cikin jerin sunayen kamfanonin da ba su da tabbas, yayin da ta sanar da kaddamar da wani binciken yaki da shigo da kayayyaki fiye da kima kan shigo da wasu na’urorin daukar hoton CT na x-ray wadanda suka samo asali daga Amurka da Indiya.
Kazalika, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin a yau Juma’a har ila yau, ta dakatar da takardun cancantar shigo da kayayyakin wasu kamfanoni shida na Amurka sakamakon batutuwan da suka shafi bincike da kuma kandagarkin kayayyakinsu. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp