Isra’ila ta sake kai hare-hare ta sama kan kasar Siriya
Published: 4th, April 2025 GMT
Jiragen yakin Isra’ila sun kai karin hare-hare ta sama kan kasar Siriya, inda suka bijirewa gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da hadassa asarar fararen hula yayin da suke ci gaba da kai wa kasar ta Larabawa hare-hare.
Rahotanni sun ce a ranar alhamis, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare a kalla sau biyu a kan wuraren da sojoji a kusa da birnin Damascus, inda bayanai suka ce sun kai hari a yankunan Al-Kiswah da Al-Muqaylibah.
Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.
Hare-haren sun zo ne kasa da kwana guda bayan hare-haren da Isra’ila ta kai makamancin haka inda ta kashe mutane 13.
Fararen hula 9 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a lardin Dara’a da ke kudu maso yammacin kasar Siriya a yammacin ranar Laraba.
Isra’ila dai ta tsananta kai hare-hare kan Siriya tun bayan da ‘yan tawayen HTS suka karbe iko daga hannun gwamnatin Bashar Al’Assad a watan Disambar bara.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Geir Pedersen a ranar Alhamis ya yi Allah wadai da karuwar hare-haren soji da gwamnatin Isra’ila ke yi, yana mai gargadin cewa suna yin zagon kasa ga yunkurin sake gina kasar Syria da kuma kara jefa kasar cikin mawuyacin hali.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce “Irin wadannan ayyuka na kawo cikas ga kokarin samar da sabuwar kasar Siriya mai zaman lafiya da yankin, da kuma jefa Siriya a cikin wani mawuyacin hali.”
Tun bayan rugujewar gwamnatin Bashar al-Assad, sojojin Isra’ila ke kai hare-hare ta sama a kan cibiyoyin da suke bayyanawa da na soji, da kuma rumbun adana kayan yaki na sojojin Siriya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kai hare hare kasar Siriya
এছাড়াও পড়ুন:
Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp