Aminiya:
2025-04-30@23:08:43 GMT

Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan

Published: 20th, March 2025 GMT

A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma.

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:

Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah.

Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan ibada, musamman a dararen mara a goman karshen watan Ramadan. Sallah: Musamman Sallar Tarawihi da Tahajjud, baya ga yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma yin nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin na farilla. Karatun Al-Kur’ani: A dage a yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi, a daren Lailatul Kadar, cikin kwana goman karshe. Addu’o’i: A dage da addu’o’in neman garafa da rahamar Allah da aljannah da kuma dacewa da alherin duniya da lahira da kuma neman tsari daga wuta da kuma sharrin duniya da na lahira. Mutum na iya yin addu’a a lokutan da ake amsa addu’o’i kamar lokacin Sahur ko bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin da cikin sujada ko a cikin sulusin karshe da dare da sauransu. Umrah: Hadisi ya nuna wanda ya yi Umra a cikin goman karshe na Ramadan zai samu ladar yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW). Zakka: Ana so duk Musulmi mai hali ya fitar da Zakkar Kono ya ba wa mabukata. Magidanci da da da hali zai fitar da sa’i daya (Mudun Nabi hudu) na hatsi, haka kuma zai fitar wa iyalansa da duk wanda yake ciyarwa. Ana iya fitarwa a bayar daga ranar 28 ga Ramadan har zuwa lokacin tafiya masallacin idi ranar Karamar Sallah. Kabbarori: Ana yin kabbarori daga bayan faduwar ranar jajibirin Karamar Sallah, har zuwa lokacin da za a idar da sallar idin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Goman Karshe kwana 10 Ramadan

এছাড়াও পড়ুন:

Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu

A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.

 

Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.

 

Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu gobe Alhamis
  • Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  • Yadda ta kaya a wasannin kusa da na ƙarshe na Gasar Zakarun Turai
  • Abubuwan Da Na Gani A Yankin ‘Hero Bay’ Da Ke Cikin Kasar China
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi
  • Sarkin Musulmi Ya Ayyana Ranar Talata 1 Ga Watan Zulki’ida
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
  • Lebanon:  Isra’ila Ta Kai Hari Akan Unguwar Dhahiya A Birnin Beirut