2025-06-30@21:26:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2134
«karanta Alƙur ani»:
Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.” Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.
Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo. Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro. “Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai,” in ji Ahmad Manga. “Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu,” in ji Manga. Ya bayyana cewa Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa-kai na Gwamnatin...
Ya ce a tare da shi a cikin tawagar, akwai Ministan shari’a, Antoni-janar na tarayya, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin Minista a ma’aikatar gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata. Tawagar ta kuma haɗa da wasu manyan Malamai, waɗanda suka ƙunshi, Dr Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Limamin masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad. Daga nan ma’aikatan ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jidda, ƙarƙashin Jakada Mu’azzim Ibrahim Nayaya, wanda da ma shi ke kai-kawo wajen shirya yadda jana’iazar za ta gudana, duk sun haɗu da tawagar don gudanar da ita a yau Litini. Alhaji Ɗantata dai ya rasu ne a Abu Dhabi ta Haɗaɗɗiyar Ɗaular Larabawa...
Sojojin HKI sun kai falasdinawa akalla 72 ga shahada a safiyar yau Litinin, daga cikinsu har da yara kanana da kuma wadanda suke jiraran a basu taimakon abinci a cibiyoyinsu a cikin Gazzar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau litinin a Gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa a wurare da dama a gaza. Labarin ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka ji ciwo zuwa asbitin Al-Ahli. Bayan haka yahudawan kai kai hare-hare a yankin Zaitun da kuma kasuwar zawiyya. Labarin ya kara da cewa baba gadaje a Asbitin don haka zaka ga wadanda suka ji ciwon kwance a kasa. Har’ila yau labaran sun bayyana cewa mafi yawan wadanda sojojin yahudawa suka kashe...
Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula. Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile yakin duniya na uku. A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taba dauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da karfin kokarinmu. A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban dan’Adam shi ma yana da tasiri a MDD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban karni, wanda kasashe...
Rahotannin da suke fitowa daga Amurkan sun ce, wani mutum mai dauke da bindiga yankin Cotinai dake jihar Idaho ya bude wuta akan ma’aikatan kashe gobara a lokacin da suke kan aikinsu na kashe wutar da ta tashi a dajin Kootenai. Jami’an tafiyar da sha’anin Mulki a yankin ya bayyana cewa; har yanzu ba a yi nasarar kama maharin ba,kuma yana ci gaba da kai wa jami’an tsaro hari, saboda babbar bindiga yake amfani da ita. Bude wuta akan mai uwa da wani a kasar Amurka wata halayya ce wacce ta dade ana fama da ita saboda yaduwar makamai a hannun mutane. Kungiyar da take kare wadanda suka makamai a cikin Amurka tana da karfin tasiri a cikin harkokin siyasar...
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Uwargida Oluremi Tinubu wacce ta ba da Naira miliyan 110 ga iyalan marigaya. An kuma yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ɗauki nauyin ilimin yaran waɗanda suka rasu da kuma taimaka wa matansu da iyayensu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa...
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Alhaji Kabir Husaini, wanda ke jagorantar aikin, ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da Mangal ke bayar da irin wannan taimako ga marasa lafiya masu ƙaramin ƙarfi. Ya ce a baya, Mangal ya taimaka wajen yi wa masu lalurar gwaiwa...
Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni. Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar. Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne...
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a gaban sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ministar harkokin wajen Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, Teresa Kayumba, da na Rwanda Olivier Nduhungirehe. Yarjejeniyar da Amurka da Qatar suka wakilci shiga Tsakani ta hada da tanade-tanade kan mutunta yankunan kasa, haramta ayyukan soji, kwance damarar makamai da hadewar kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma samar da wani tsari na hadin gwiwa don daidaita...
Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kasarsa na adawa da duk wata yarjejeniyar yafe haraji da Amurka za ta kulla da wata kasa, wadda ka iya illata moriyar Sin, tare da baiwa kasar da aka kulla yarjejeniyar damar samun yafiyar haraji daga Amurka. Kakakin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, lokacin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da tattaunawar cinikayya da Amurka ta yi tare da wasu kasashe, ya ce, idan an samu aukuwar irin wannan yanayi, kasar Sin ba za nade hannu ba, za ta dauki matakai na martani domin kare halastattun hakkoki da moriyarta. Jami’in ya kara da cewa, tun watan Afrilun da ya gabata, Amurka ke ta ingiza matakan...
Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin farashin abubuwa da dama da zai hau sama. A cewar masana, Gabas ta Tsakiya da ke samar da akalla kashi 34 na mai a duniya da kashi 18 na gas, gumurzun kasashen biyu ya haddasa farashin danyen mai tashi da kashi 10, yayin da gas ya kara da kashi 7. Haka ma akwai fargabar Isra’ila na iya illata harkokin mai da jigilarsa a mashigar Hormuz...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce zai iya yin komai muddin hakan zai kawo zaman lafiya da ci gaba a jiharsa. Fubara, ya faɗi haka ne a garin Fatakwal a ranar Asabar, yayin da yake magana da magoya bayansa. An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina Van Nistelrooy ya ajiye aikin horas da Leicester City Ya tabbatar musu cewa ya sasanta da Tsohon Gwamnan jihar, wanda a yanzu Ministan Abuja ne, Nyesom Wike. Ya ce ya san wasu daga cikin magoya bayansa ba za su ji daɗin sasancin da aka yi ba, amma ya roƙe su da su yi haƙuri. Ya ce: “Wani lokaci sai an ɗauki matakai masu wahala domin a samu gyara.” Ya ƙara da...
Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu. Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin...
“Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan. “A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60, Awakai sama da miliyan 1.4”, in ji shi. Kazalika, Minstan ya kara da cewa; burin shi ne ganin an kara bunkasa tattalin arzikin kasar tare da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar. “Ina son fayyace cewa, ba wai batu ne kawai na yawan Shanun da ake da su a kasar nan ba, batu ne na jama’a da samar da ayyukan yi, habaka...
Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...

Faransa Tace Za’a Maida Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Iran Idan Taki Yarda Da Yarjeniyar da Trump Yake
Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta ki ta rattaba hannu kan yarjeniyar da gwamnatin shugaba Trump yake so kan shirinta na makamashin Nukliya ba, abinda muke buklata kawai shi ne mu aika da wasika kan a dawoda takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, wadanda suka hada da na makamai, kudade, da kuma fasaha wadanda aka dagesu shekaru 10 da suka gabata. Bayanda Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA a shekara 2018...
Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”. Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji. Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne. “Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga. Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Monaco ta ƙulla yarjejeniyar kaka biyu da tsohon ɗan wasan Manchester United da kuma Juventus, Paul Pogba. Pogba mai shekara 32 ya koma a matakin wanda bai da kwantiragi tun daga watan Nuwamba, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu. Nijeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a duniya — IMF Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan A watan Maris ɗin bara ne aka dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan ƙara kuzarin jiki. Amma yanzu zai koma taka leda bayan da aka rage hukuncin zuwa wata, sakamakon ɗaukaka kara a watan Oktoba. Ya fara taka leda a Manchester United daga nan ya...

An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin
Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin fadakar da al’umma na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen jihar Xizang mai cin gashin kai ta kasar, da gidan rediyo da talabijin na jihar, da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na Qinghai-Xizang na kasar Sin, inda aka gayyaci manyan ’yan jaridu gami da shahararrun masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet guda 20, don watsa labarai game da jihar ta Xizang. A...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Da Isra’ila Kanta
Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka yi kan cibiyoyin makamashin nukiliya, da kafofin yada labarai, da cibiyoyin kiwon lafiya na Iran, da kuma wuraren zama, gidajen yari da birane da kauyuka, a matsayin misali karara na keta dokokin kasa da kasa da hakkokin bil’adama. A cikin wata wasika da ya aike wa kwamishinan kare hakkin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türk Nasser Seraj mataimakin shugaban hukumar...
Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran tana kera makamin nukiliya ba. Grossi dai ya fuskanci tambayoyi da kalubale da dama daga mai gabatar da Shirin, kan ko Iran na daf da kera makamin nukiliya? Ya amsa a cikin halin shakku, yana mai cewa a cikin rahoton ya nisanci zargin Iran da kokwarin kera makamin nukiliya domin babu tabbas kan zargin. Da aka tambaye shi ko Iran na kera makamin nukiliya?...
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...
Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika dake Nijeriya ce ta shirya taron mai taken “Hada Hannu Wajen Zamanantar da Sin da Afrika da cimma shirye-shirye 10 na Hadin Gwiwa a Cikin Al’ummar Sin da Afrika mai Makoma ta Bai Daya a Ko da Yaushe.” Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali...
Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar ta NPA, kudin shigar da ta yi hasashen Tarawa daga na Naira biliyan 865.39, sun karu zuwa Naira biliyan 894.86. “ Wannan ya nuna yadda Hukumar ta NPA, ta mayar da hankali da kuma kara zage Damtse wajen ganin ta Tarawa Gwamnatin Tarayya kudaden shiga, masu yawa,” A cewar Dantsoho. Shugaban ya kuma bayyana cewa, kudaden shigar da Hukumar ke hasashen Tarawa a shekarar ta...
Duk ana dora alhakin yadda lamarin cinikin Bayi ya bunkasa kan wani mutum dan asalin kasar Birtaniyya da ake kira da suna,John Hawkins. Hawkins shi ne mutumin da ya kara daukaka, bunkasa,da zamanan har da lamarin cinikin Bayi”manufa anan yayi gyare- gyare daga yadda Turawan kasar Fotugal suka fara da barinsa,ya yi masa kwaskwarima,zuwa lamarin kasuwanci mai daraja”. Jiragen ruwa suna tasowa daga Kasar Birtaniya ko kuma Ingila da Bindigogi, Madubi,da kuma Giya,Jiragen na zuwa wani wurin da ake kira da suna inda ake daukar Bayi a kai su kasar ko kasashen da suka saye su, yanzu wurin ana kiransa da suna yankin Neja Delta inda daga can ne kuma za ‘a fara tafiya, har sai sun kai inda zasu...
A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali har zuwa dandalin yenci dake tsakiyar birnin na Tehran . Ana dauke da gawakin shahidan rufe da tutan Iran a cikin akwatuna. Daga cikin manya-manyan bakin da suka halarci tattakin har da shugaban kasa Dr Masoud Pezeshkiyan da kuma wasu ministocinsa . A ranar 13 ga watan Yuni ne HKI ta fara kaiwa kasar Iran yaki inda ta kashe mutane da dama daga daga ciki...

Jiniyoyin Gargadi Sun Tashi A HKI A Lokacinda Mayakan Ansarallah Suka Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kasar
An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada rahoton yawan barnan da makamai suka yi ba bayan shigowarsu haramtacciyar kasar. Yahudawan sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi a yankunan Beersheba, Dimona da kuma garuruwan da suke kewaye da su a safiyar yau Asabar. Majiyar sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun cilla makaman kan haramtacciyar kasar Isra’ila ne saboda ci gaba da kissan kiyashin da take a zirin gaza.

Indomie Ta Kaddamar da gangamin “Ingantaccen Abinci Domin Nasara” Don Daukaka Abinci Mai Gina Jiki da Murnar samun Nasara
Indomie , shahararriyar kampanin taliyar indomie a Najeriya, ta sanar da kaddamar da sabon gangamin ta mai taken Ingantaccen Abinci Domin Nasara. Wannan gangamin yana jaddada rawar da abinci mai gina jiki kamar Indomie ke takawa wajen ciyar da nasarar iyalai da Karin lafiyar su a Arewacin Najeriya. Shekaru da dama kenan da aka san taliyar Indomie da inganci, daɗi da arha a gidajen ‘yan Najeriya. Tallan talabijin na Ingantaccen Abinci Domin Nasara ya kapu Akan wannan manufa, inda ya ke nuna Indomie a matsayin abokin tafiya wajen cinma nasarar dukkan iyalai na faɗin ƙasa. Nasara Ta Hanyar Abinci Mai Gina Jiki An ƙaddamar da gangamin ne a ranar 6 ga Yuni, 2025, Munaso mu kara jaddada jajircewar Indomie wajen...
Tallan na talabijin ya bayar da labarin rayuwar Binta, ya kuma mayar da hankali akan irin tasirin da abinci mai kyau ya ke da shi wajen tallafawa iyali. Da labarin ya yi nisa, mun gano Binta tun daga ƙuruciya zuwa shigarta makarantar koyon aikin likitanci. Hakan ya nuna yadda abinci mai kyau da goyon bayan iyali ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cin nasara a rayuwa. Binta ta girma tare da cin abinci mai gina jiki ta hanyar cin taliyar Indomie tun da fari. Indomie tun da daɗewa tana da yaƙini kan cewa ciyarwa bai tsaya kawai ga jiki ba ne. Har da taimakawa wajen cikar buri da samar da makomar kowanne yaro zuwa mataki na gaba. Shi ya sa...
Hukumar samar da bunkasa da hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin ta gabatar da taron manema labarai a yau Juma’a, inda aka yi karin haske game da yadda Sin take baiwa kasashen Afirka tallafi da samun bunkasa tare da su cikin hadin gwiwa. An ce, ya zuwa yanzu, Sin tana taimakawa kasashen Afirka fiye da 21 a bangaren kimiyyar aikin gona, inda ta tura musu kwararrun aikin gona fiye da 200. Kazalika, bangarorin biyu suna hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan dake da nasaba da na’urorin wutar lantarki da horar da kwararru da habaka da karfinsu da sauran bangarori. Kana suna kaddamar da ayyukan samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ciki har da samar da...
Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da wasu biyar suna jinya bayan da wata babbar mota ƙirar tirela ta ƙwace ta kutsa cikin kasuwar Mile Six da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba. Shaidun gani da ido a wurin sun bayyana cewa, duk ƙoƙarin da direban motar ya yi na hana afkuwar lamarin ya ci tura. Ƙudan zuma ya tarwatsa ɗaliban da ke jarrabawar NECO ’Yan sanda sun kama ɓarayi 5, sun ƙwato kuɗi da makamai a Gombe Aƙalla motoci biyu ne suka yi mummunan lalacewa a lamarin. Jami’an Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da hukumar tsaro ta farin kaya sibil defens (NSCDC) da kuma rundunar ’yan sandan Najeriya (NPF) sun halarci wurin da jajantawa yankin...
“Wannan ya nuna dalibai, 96,838 zasu rubuta jarabawa a fadin Nijeriya gaba daya duk ta wannan shekarar ce, 2025,a cibiyoyin rubuta jarabawa,183,yayin da wasu kuma za su jira.” Hakanan ma Hukumar tace tana nan tana bankado cibiyoyin rubuta jarabawa da ake yin cuwa- cuwa, da kuma wadanda basu cancanta, ace n arubuta jarabawar a wuraren ba, saboda rashin ingancin abubuwan da ake amfani da su lokacin jarabawar. Akwai wuraren/ cibiyoyin rubuta jarabawa wadanda aka tantance hakan kuwa ya biyo baya binciken kwakwaf da aka yi lokacin da aka yi jarabawar ta gwaji, jarabawar ta sosai,da wadda aka sake rubutawa.Kamar yadda aka bayyana, kuma kamar yadda sakamakon bincike-binciken da aka yi, akwai cibiyoyin rubuta jarabawa,113 wadanda yanzu an dakatar da amfani...
Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno. Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira. Shugaban APC na ƙasa Ganduje ya yi murabus NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe Shaidun gani da ido sun ce, sun ga ɗalibai na barin litattafai da takalma da jakunkuna, har ma da kekunansu yayin da suke gudu daga makarantar. A cewar wani ɗalibin da ke jarabawar da ya nemi a sakaya sunansa ya...
“Yunwa da talauci ba wai abubuwa ne da suka shafi al’umma ba ne kawai, su ne ke haifar da rashin tsaro, laifuka, tashin hankali, da kuma wargajewar al’umma, wadannan al’amura suna haifar da mugun yanayi, talauci yana haifar da rashin tsaro da rashin tsaro, sannan kuma ya kara zurfafa talauci. “Wadannan yunkurin a bayyane suke ta hanyar kara tallafi ga shirye-shiryen samar da abinci, habaka karfin aiwatar da doka, da ababen more rayuwa don tallafawa samarwa da rarraba noma. “A ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ONSA, muna ci gaba da hada kai da ayyukan motsa jiki da marasa karfi a fadin rundunonin soja, jami’an leken asiri, hukumomin tsaro, da masu ruwa da tsaki na gwamnati da...
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa tattaunawar da suka yi da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kawo ƙarshen duk wata rigima da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara. A daren ranar Alhamis ne Shugaba Tinubu, ya jagoranci wani zaman sulhu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, tsakanin Wike da Gwamna Fubara da kuma wasu daga cikin ’yan majalisar Ribas da aka dakatar. NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin dokokin haraji Bayan ganawar, Wike ya yi magana da manema labarai, inda ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicinsa da Fubara. “Dukkaninmu mun amince mu yi aiki tare da Gwamna, kuma...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu. Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa wasu shaguna da ke a wata kasuwa, da ka mayar a matsayin wajen kwanan, ‘yan gudun hijira, wuta. Duk da kokarin da wasu matasa da kuma kokrin jami’an tsaro na dakile maharani, hakan ya faskare su, hatta wani daya daga cikin jami’in tsaro da aka tura wanzar da tsaro, ya rasa ransa. Duk a 2025, a watan Afiiru an kai hare-hare a Logo da Ukum,...
Daga ƙarshe dai Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sa hannu kan sababbin dokokin haraji guda hudu da a baya suka jawo cece-kuce da zazzafar muhawara a faɗin Najeriya. An dai sanya hannun ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja ranar Alhamis, inda shugaban ya ce dokokin za su bunkasa harkokin hada-hadar kudade da tattara haraji a kasar. NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya? Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya A kwanan nan ne dai Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da kudurorin su zama doka bayan tafka zazzafar muhawara a zaurukan majalisun guda biyu. Daga cikin waɗanda suka halarci bikin saka hannun akwai Shugaban...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...
Cristiano Ronaldo ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwatiraginsa da shekara biyu a ƙungiyar Al Nassr da ke buga gasar Saudi Pro League. Wannan dai na nufin kyaftin din na tawagar Portugal zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2027, lokacin da zai kai shekara 42 a duniya. Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun Islamiyya Al-Nassr ta bai wa Ronaldo kwantiragi mafi tsada a tarihin wasanni, inda ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fam miliyan 24.5 ($33.7m), lamarin da zai ba shi damar samun albashin da zai rika karbar sama da fam miliyan a duk kwana biyu. Ɗan wasan mai shekara 40 ya je Al Nassr ne a...
Babban malamin addinin Islama kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya cika shekaru 101 a duniya, a lissafin kalandar Musulunci. An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne a ranar 2 ga watan Muharram a shekara ta 1346 bayan hijira, inda a gobe Juma’a, 2 ga Muharram na shekarar 1447, yake cika shekaru 101 cif a ban kasa. Ƙarancin abinci: UNICEF ta tallafawa yara 600,000 a Borno, Yobe Gwamnatin Katsina ta amince da ƙidayar almajirai, makarantun Islamiyya Duk da cewa iyalai da almajiran Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi ba su yi wani biki don taya shi murnar cika shekara 100 a duniya, amma masoya da almajiran Shehin Malamin sun bayyana farin cikinsu da yi masa addu’o’i musamman a...
Adedeji ya ce har zuwa sa’o’i biyu kafin sanarwar, sunan hukumar shi ne FIRS, amma yanzu sunan ya koma NRS. Ya bayyana cewa sabuwar hukumar ba za ta tsaya kan tattara haraji kawai ba, domin yanzu tana damar tattara sauran kuɗaɗen shiga da ba na haraji ba. Hakazalika, za ta yi aiki cikin ’yanci tare da bin ƙa’idojin bayyanan aiki da bin diddigin nasarori. Ya ƙara da cewa sabuwar hukumar za ta mayar da hankali sosai wajen cimma nasarori, kuma za ta yi aiki da ƙwarewa kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya. Shi ma shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ko da kuwa doka na da kyau, idan ba a aiwatar...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar. Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar. Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa...
Yawan gawarwakin da aka tsinta bayan harin duk na mabiyansa ne. Ɗaya daga cikin su, Bashari Maniya, wanda tsohon ɗan bindiga ne da ya ce ya tuba kuma ya fara taimaka wa jami’an tsaro, shi ma ya mutu bayan motar da yake ciki ta faɗa rami mai zurfi. Manga ya bayyana cewa ba da bindiga aka kashe Maniya ba, saɓanin jita-jitar da ke yawo. “Sabuwar mota ce, kuma ba su san dajin sosai ba. Yayin da suke gudu a cikin daji, sai suka faɗa cikin wani rami mai zurfi. Motar ta kife, kuma an kasa ciro ta cikin sauƙi,” in ji shi. Ya ce lokacin da aka zo taimaka musu, an same su a cikin motar a sume. Motar ba...
Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin. Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya. Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai karkashin jagorancin wani fitaccen kasurgumin dan bindiga mai suna Babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine ne ya bayyana hakan a wani sharhi da aka wallafa a shafinsa na X, yana mai cewa, maharan sun kashe mazauna yankin da dama, tare da hana ayyukan noma, da kuma haddasa durkushewar ayyukan kasuwanci na yau da kullum a yankin. “Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga karkashin jagorancin babaro sun kwace iko da jagorancin karamar hukumar Kankara, jihar Katsina. An hana noma daga Marabar Kankara zuwa ‘Yantumaki, an kashe mutane da dama, an yi garkuwa da wasu, kiwon lafiya ya durkushe. Mazauna garin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce zai karɓi kowane irin muƙami da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi, amma ya ce a yanzu ba ya son a yi magana kan batun zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Yayin wata ganawa da manema labarai kan shirin sauraron ra’ayoyin jama’a da za a yi kan sauya kundin tsarin mulki, Barau ya ce, “Duk abin da Shugaba ya ce na yi, zan yi shi da yaƙini na gaske.” Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su Wannan na zuwa ne bayan ya shawarci wani rukuni da ke goyon bayan...

Gwamnan Jigawa Ya Kaddamar Da Rumbun Sauki Don Sayar Wa Ma’aikata Kayayyakin Abinci A Farashi Mai Rahusa A Sakkwato
Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Sin Ta Sha Alwashin Rarraba Fasahohinta Na Ainihi Da Dabarunta Na Kirkire-Kirkire Tare Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce, kasarsa a shirye take ta rarraba fasahohinta na ainihi, da dabarunta na kirkire-kirkire tare da sauran sassan kasa da kasa. Li Qiang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bude taron shekara-shekara, na sabbin jagorori karo na 16, wato dandalin tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos a takaice, wanda aka bude yau Laraba a birnin Tianjin na kasar Sin. Li ya kara da cewa, Sin na da karfin gwiwa, da ikon wanzar da ci gaban tattalin arzikinta, tana kuma kara kaimin zama kasa mai babban matsayin samun kudin shiga, yayin da ake kara daga matsayin sayayya bisa kyakkyawan yanayi a kasar, wadda ita ce ta biyu a girman kasuwar sayayya a...
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Borno (PPRO), Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, ta ce an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu jihohin da suka hada da Benuwe, Filato, da Borno, a ‘yan kwanakin nan sun samu tabarbarewar tsaro, lamarin da ya sa sojoji da sauran jami’an tsaro suka kara zage damtse wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da kalubalen tsaron ke kara ta’azzara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yaya girman neman fadadar kungiyar NATO yake? Alkaluma ne za su iya fayyacewa: Abun da aka kashe a duniya kan aikin soji a shekarar 2024 ya kai dala triliyan 2.72, inda kungiyar NATO ta dauki dala triliyan 1.5, wato kaso 55 na jimillar ta duniya. Duk da rashin daidaiton karfin soji tsakanin kasashen duniya, NATO na ci gaba da sanya mambobinta su kara abun da suke kashewa a bangaren tsaro zuwa kaso 5 na alkalumansu na GDP. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar ya nuna cewa, kaso 67.4 na wadanda suka bayar da amsa sun yi tir da yadda NATO ke gaggauta fadada karfinta na soji, suna gargadin hakan ka iya haifar da sabuwar takarar makamai da yin gagarumar...
Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja. Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli. Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga...
Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su. Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe. PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta An same su da laifin ɓoye bayanai, taimakawa wajen aikata laifi, satar yara da kuma safarar su. An sace yaran ne daga Kano, sannan aka sayar da su a garin Onitsha da ke Jihar Anambra. Shugaban tawagar, Paul Onwe, tuni aka yanke...
Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi. Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya. Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a...
Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi. Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya. Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya nesanta kansa daga wata kungiya da take fafutukar ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a 2027. Mai magana da yawun Sanatan, Isma’il Mudashir ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce a maimakon haka, kamata ya yi kungiyar ta fi mayar da hankali wajen mara wa Tinubu baya ya samu nasarar yunkurinsa na bunkasa Najeriya. A kwanan nan ne dai wata kungiya mai suna Zauren Matasan APC na Arewacin Najeriya (NNPYA) ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu ya dauki Sanatan a matsayin wanda za su yi takara tare. Gwamnatin Nijeriya ta yi wa Amurka martani kan barazanar tsaro a Abuja Mali...
Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet. “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki. “Amma abin ya ba mu...
Gwamnatin Nijeriya ta ce babu wata barazanar tsaro a babban birnin ƙasar, Abuja, inda ta yi kira ga mazauna birnin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana. Nijeriya ta musanta batun yiwuwar kai hari kan ’yan Amurka da suke zaune a kasar, sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani dangane da gargaɗin tsaro da Amurka ta aika zuwa ga ’yan ƙasarta da ke birnin Abuja. A sanarwar da Ministan Watsa Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce, “Gwamnatin Nijeriya ta samu labarin...
Shugaban Mali, Assimi Goita da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Wannan dai na cikin wasu yarjejeniyoyi da Mali da Rasha suka rattaba hannu waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki. Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Shugaba Vladimir Putin ya shaida wa shugaban kasar ta Afirka ta Yamma da ke ziyara cewa akwai wasu fannoni na musamman da za a iya ƙara haɗin kai. Putin ya karbi bakuncin Kanal Assimi Goita a fadar Kremlin, inda suka tattauna tsawon awanni biyu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati...
“Ina so in yi kira ga NNPYA da duk sauran kungiyoyi da daidaikun mutane da ke cikin wannan ikirari da su daina wannan kiran, a maimakon haka, su mayar da karfinsu wajen marawa Shugaba Tinubu baya a yunkurinsa na magance dimbin kalubalen da kasarmu ke fuskanta.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar ministocin harkokin waje ta kungiyar kasashen musulmi (OIC), ta gudanar da taronta na 51 daga ranar 21 zuwa 22 ga watan nan. Taron ya tabbatar da kokarin Sin na kare al’ummar musulmi tare da yaba wa ci gaban da aka samu na dangantaka tsakanin Sin da kasashen musulmi da kuma sa ran kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyar OIC da kasar Sin. Da yake tsokaci kan hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jian kun, ya ce a ’yan shekarun nan, Sin da kasashen musulmi da ma kungiyar OIC, sun ci gaba da zurfafa aminci a tsakaninsu da fadada hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban da karfafa musaya tsakanin al’ummominsu tare da samun kyawawan sakamako. Ya ce Sin za ta...
Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla. Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata. Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Trump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba. Ya ce: “Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar muku cewa ina fushi da abin da suka aikata.” Shugaba Trump ne mutum na...
Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki. Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga gobe Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yulin 2025. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai. Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanar wa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi. A ƙarshe sanarwar ta ce...
Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta tsare wasu tsofafin manyan jami’an Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) kan zargin badakalar kudade da yawansu ya kai Dala biliyan 7.2. Jami’an EFCC sun tsare tsohon Babban Jami’in Kudi na NNPCL, Umar Ajiya Isah da kuma tsohon Manajan-Daraktan Matatar Mai ta Warri, Jimoh Olasunkanmi, kan zargin almundahanar. Wani babban jami’in EFCC da ya nemi a boye sunansa ya ce hukumar ta tsare tsoffin manyan jami’an na NNPC ne kan zargin wadaka da kudaden gyaran matatun mai da ke Kaduna da Warri da kuma Fatakwal. Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske daga kakakin EFCC, Dele Oyewale, amma jami’in bai amsa duk kiraye-kirayen da aka yi masa da kuma rubutattun sakon...
Eze ya gode wa waɗanda suka kafa ADA saboda ƙoƙarinsu na ceton Nijeriya daga hannun shugabannin da ba sa bin tsarin dimokuraɗiyya. Ya ce sun nuna ƙwazo da ƙaunar ƙasa. Ya ce, “Kun nuna bajinta da kishin ƙasa ta hanyar ƙoƙarin ƙwato mulki daga hannun shugabannin da suka haddasa rikice-rikice, garkuwa da mutane, talauci, yunwa da kunya ga ƙasar nan.” Eze ya kuma yi addu’ar cewa Allah Ya taimaka musu su samu nasarar ceto Nijeriya daga hannun shugabanni marasa ƙwarewa da tausayi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...

Xi Jinping Zai Halarci Bikin Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan Da Yakin Kin Tafarkin Murdiya
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya bayyana cewa, shugaban kasar Xi Jinping, zai halarci bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin jinin harin sojojin Japan, da yakin kin tafarkin murdiya, da safiyar ranar 3 ga watan Satumban bana, tare da gabatar da jawabi. Kazalika a ranar, kasar Sin za ta gudanar da gagarumin bikin faretin soja a filin Tian’anmen dake nan Beijing, inda shugaba Xi zai duba faretin. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tawagar Likitocin Kasar Sin Sun Duba Marayu Marasa Lafiya Fiye Da 200 Kyauta A Zanzibar Ta Tanzaniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
2. Haɗin kai da shugabanni daga ko’ina 3. Rashin ta’asar da ya yi wa kowa Bayannan ƙuri’un INEC na 2023 daga jihohin Arewa maso Gabas sun nuna cewa Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u fiye da Tinubu a dukkan jihohin yankin. Ƙungiyar ta kammala da cewa: “Lokaci ya yi da Shugaba Tinubu ya kamata ya yi la’akari da wannan batu yayin shirye-shiryen zaɓen 2027.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani hari da Sojojin Amurka da Isra’ila suka kai kan wuraren Nukiliyar Iran ya kara tsoratar da kasuwar mai, wanda ke nuna cewa farashin na iya haura sama da $80 a kowace gangar mai. Masana sun yi hasashen cewa farashin fetur na iya haura sama da N1,000 a litar cikin ‘yan makonnin nan idan ba a dauki mataki ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu. Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023. A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara. Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya...
Rikicin Isra’ila da Iran ya kara dagula tabarbarewar harkokin man fetur da iskar gas a cikin fargabar barkewar rikicin Gabas ta Tsakiya wacce ta kasance jigo wajen hada-hadar man fetur da iskar gas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan 258.5. Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa. A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu. Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka...
Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila. Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”. Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani...
Gonar ta ‘AA Dibine Agro’, ta kasance a yankin Pasali Karshi da ke cikin karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa. Kazalika, kudirin shi ne; nomawa da kuma samar da isasshen Filanten din da za a rika kai wa har zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin sayar da shi. A cewar tasa, abin da gonar ke son cimma shi ne, taimaka wa fannin aikin noma na tarayyar kasar nan, wanda hakan zai kuma kara tallafawa wajen kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa tare da samar da wadataccen abinci. Sai dai, ya bayyana cewa; rashin kudaden da za a yi amfani da su wajen cimma wannan manufa, su ne babban cikas. Gonar, wadda aka samar da ita a zagayen Katangu,...
Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...

Babban Al’amari Ne A Samu Ƴar Shekara 6 Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli
Ya kara da cewa wannan sauka ita ce karo na hudu wanda aka yi walimar dalibai 45, maza da mata, inda mafi kankanta daliba ita ce mai shekaru shida da rabi da makarantar ta yaye jimlar dalibai 90 kenan tun daga 2018 zuwa wannan shekara 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Kano Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar. Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran Sanarwar ta ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma’a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce “gwamnan zai kashe naira biliyan 2.” “Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Domin saukaka wannan tsari ga masu biyan haraji da kuma kara yawan karbar harajin a cikin irin wannan mawuyacin lokaci, hukumar ta amince da tsawaita ayyukan ofisoshin harajin zuwa karshen mako na watan Yunin 2025,” in ji umarnin da shugabannin uku suka sanya wa hannu, in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da biyan ƙarin albashin Naira 5,000 ga ma’aikatan ƙananan hukumomi da Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomi (LGEA). Ƙarin albashin zai fara aiki ne daga albashin watan Yuni na shekarar 2025 Wata sanarwa da Jibrin Yusuf ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Ahmed Abdullahi, ta ce cimma matsayar ne a wani taro na musamman da aka gudanar a ranar Talata. Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikata tare da wakilan ƙungiyoyin kwadago da wasu manyan jami’an gwamnati. Najeriya ta tura sojoji domin samar da zaman lafiya a Gambia Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa taron Kungiyar OIC a Turkiyya Ta ce an amince da ƙatin Naira 5,000 ga ma’aikatan har sai an kammala aikin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An yi wa wasu matafiya ɗaurin aure 12 kisan gilla bayan wasu mutane sun kai musu hari a yankin Mangu ta Jihar Filato sun kai musu hari. Rahotanni sun bayyana cewa mutum 11 daga cikin matafiya suna samun kulawa a asibiti, bayan raunukan da suka samu a harin da aka kai musu a yankin Ƙaramar Hukumar Mangu a ranar Juma’a. Aminiya ta samu labarin cewar an kai wa matafiya hari ne da misalin ƙarfe 8 na dare, a lokacin da su mutum 31, ciki har da mata da ƙananan yara, a cikin wata bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya. Ayarin ’yan daurin auren da aka kai wa harin sun fito ne daga yankin Basawa da ke Zariya a...
Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako. Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu, da tunanin jama’a, da kuma a matakin aiki. Yanzu ‘yan Nijeriya za su iya tabbatar da cewa manyan hanyoyin mu sun fi samun tsaro ƙwarai idan aka kwatanta da ‘yan shekarun baya.” Ya lissafa nasarorin da rundunonin sojin Nijeriya suka samu a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da yankin Arewa-maso-gabas da gaɓar teku. “Daga nasarar ragargaza sansanonin Boko Haram da ISWAP...
Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv. Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500. Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci. Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran. Makamin ya faɗo...

Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa
Mai bai wa Gwamna Uba Sani shawara kan harkokin kwadago, Adamu Samaila ne ya shaida wa wakilinmu cewa; nan bad a jimawa ba gwamnati za ta karbi rahotan tantance ma’aikatan da kuma yadda za a daidata albashin nasu. Samaila ya kara da cewa, “A mako mai zuwa ne za mu gana da wanda yake kula da aikin tantancewar, domin samun sakamakon rahoton albashin ma’aikatan.” Zamfara: Ba A Aiwatar Da Biyan Dari Bisa Dari Ba A Jihar Zamfara, gwamnati ba ta aiwatar da fara biyan sabon mafi karancin albashin ga ma’aikatanta ba. Guda daga cikin manyan jami’an gwamnatin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa; mafi karancin albashin, zai fi mayar da hankali ne a kan ma’aikatan...
Kazalika, a cewar jami’in, Sin na kara bude kofarta ga ketare bisa matsayin koli, da shigo da jari cikin kasar a bangaren sana’o’in samar da kayayyaki, kana da yafe dukkannin harajin kwastam ga kasashen Afirka mafiya fama da karancin ci gaba da suka kulla dangantakar diplomasiyya da ita. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum mai suna Alexander Peter bisa zarginsa da kashe mahaifiyarsa mai suna Madam Atiny Peter mai shekara 71 da adda. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ikot Inyang da ke ƙaramar hukumar Oruk Anam a Jihar Akwa Ibom. Yin sulhu da ’yan bindiga dabara ce ba gazawa ba — Gwamnatin Sakkwato Katolika ta horar da shugabannin al’umma da na addini kan zaman lafiya Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Baba Mohammed Azare ne ya tabbatar da kamen a yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, a hedikwatar ’yan sanda da ke Ikot Akpan Abia, a Uyo. Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin Alexander ne a ranar...
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana tsarin a matsayin wani kwakkwaran taswirar zamani da za a sa a gaba tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin an aiwatar da shi sosai. Ya ci gaba da cewa, “A yau mun samu wani gagarumin ci gaba a tafiyarmu ta haɗin gwiwa a jihar Zamfara ta hanyar inganta fasahar zamani, ƙirƙire-ƙirƙire, da hanyoyin samun bayanai da fasahar sadarwa. “Tsarin Ilimin Fasahar Zamani nna Zamfara wani tsari ne da zai amfani buƙatun al’umma na dogon lokaci don samar wa mutanenmu ƙarfin aiki da haɓaka ƙwarewarsu a cikin duniyar fasahar zamani. “Kamar yadda muka sani, ilimin fasahar zamani yana da muhimmanci don samar da ayyukan yi da samar da ingantacciyar tsarin...
A yau Jumma’a, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2025, an kafa sabbin kamfanoni na kasashen waje guda 24,018 a babban yankin kasar Sin, wanda ya nuna an samu karuwarsu da kashi 10.4 bisa dari a mizanin shekara-shekara. Daga watan Janairu zuwa Mayu, ainihin jimillar jarin waje na kai-tsaye, watau FDI da aka yi amfani da shi a masana’antun fasahohin kasar Sin ta kai yuan biliyan 109.04, inda jarin na FDI ya karu da kashi 146 cikin 100 a fannin hada-hadar kasuwanci ta shafin intanet, da kashi 74.9 cikin 100 a fannin kera kayayayakin jiragen sama, da kashi 59.2 bisa 100 a fannin samar da sinadaran harhada magunguna, da kuma karin...