Iran da Saudiyya sun jaddada wajabcin kara karfafa dangantakasu
Published: 8th, March 2025 GMT
Ministocin harkokin wajen Iran da Saudiyya sun tabbatar da aniyar kaasashensu na ci gaba da kara azama domin bunkasa alakoki a tsakaninsu a dukkanin bangarori.
Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Saudiyya Faisal bin Farhan suka yi ne a wannan Juma’a a gefen taron gaggawa karo na 20 na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Jeddah.
A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan matsayin dangantakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma masarautar Saudiyya, tare da jaddada aniyar kasashen biyu na ci gaba da fadada hadin gwiwa tsakaninsu.
Bangarorin biyu sun kuma yi nazari kan halin da ake ciki a kan batutuwa daban-daban da suka shafi yankin, da ma sauran batutuwa na kasa da kasa, tare da jaddada wajibcin yin hadin gwiwa a tsakanin dukkanin kasashen musulmi wajen tinkarar kalubale dangane da batun Palastinu da Isra’ila ta mamaye, da kuma hana aiwatar da makarkashiyar da ake shiryawa da nufin share batun Palastinu, ta hanyar tilastawa al’ummar Gaza yin gudun hijira daga yankinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba.
Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.”
Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar Juma’a mutanen Gaza sun yi ta yawo a kasuwanni, tituna, da unguwanni ba tare da samun kilo guda na gari ba.