Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara
Published: 7th, March 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a aiwatar da matakan da suka wajaba na cimma nasarar tsare-tsare masu inganci, na bunkasa rundunar sojin kasar Sin na shekaru 5, wato tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.
Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar zartarwa ta rundunar sojin kasar Sin, kuma sakataren kwamitin kolin JKS, ya yi wannan kira ne a Juma’ar nan, yayin da yake halartar taron rukuni na tawagar rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin PLA, da rundunar ‘yan sandan kasar, a wani bangare na taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA