Wang Yi: Diflomasiyyar Kasar Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankalin Da Ake Bukata A Duniya Mai Cike Da Rikici
Published: 7th, March 2025 GMT
Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu.
Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba.
Bayan haka kuma, Wang Yi, ya ce dabarar sanya shinge da kayyade fitar fasahohi, ba za iya dakushe ruhin kirkire-kirkire ba, kuma duk wanda yake raba gari ko kawo tsaiko ga tsarin samar da kayayyaki a duniya, kebanta kan shi yake yi. Wang Yi ya ce, bai kamata a yi amfani da kimiyya da fasaha a matsayin katangar karfe ba, kamata ya yi su zama arzikin da kowa zai amfana da shi.
Ya kara da cewa, a duk inda aka sanya shinge, an samu nasara, kuma a duk inda aka yi danniya, an kirkiro sabbin abubuwa.
Bugu da kari, yayin da ba a daina danne kasar Sin ba gaira ba dailili ba ta fuskar kirkire-kirkiren kimiyya ko samar da na’urar chip, hanyar da Sin ta dauka na zama mai karfi a bangaren kimiyya da fasaha na kara fadi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a BornoDa yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.
“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.
A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.