Aminiya:
2025-11-03@03:53:40 GMT

Ƙin yin sulhu da ’yan bindiga na haifar da alheri – Gwamnan Zamfara

Published: 6th, March 2025 GMT

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ce matsayarsa na ƙin amincewa a yi sulhu da ’yan bindiga na taimakawa wajen dawo da zaman lafiya a jihar.

Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake karɓi baƙuncin Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Bala Abubakar.

An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Sheikh Hassan Jingir a Jos

Air Marshal Abubakar, ya ziyarci jihar domin yin ta’aziyya harin bam da rundunar sojin sama ta kai wa wasu mutane bisa kuskure.

Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta canza matsayarta ba game da ƙin sasanci da miyagun mutane.

“Muna shaida wa kowa cewa ba za mu zauna da ’yan bindiga ba,” in ji shi.

“Hanyar da muka ɗauka tana haifar da sakamako mai kyau, kuma muna ganin zaman lafiya yana samuwa a Zamfara.”

Gwamnan ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro ke hanzarin amsa kiran gaggawa a jihar.

“Ina gode wa Hafsan Sojin Sama saboda matakin gaggawa da ya ɗauka. Kafin wannan ziyarar, ya aike da manyan jami’ai domin jajanta mana.

“Wannan yana nuna ƙwazo da jajircewarsu wajen kare lafiyar mutanenmu,” in ji shi.

Hakazalika, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana gina sabon filin jirgin sama a Zamfara, kuma ya buƙaci a gina wajen ajiye jiragen rundunar sojin sama a ciki don ɗaukar matakan gaggawa kan matsalolin tsaro.

“Muna gina filin jirgin sama a Zamfara. Da zarar an kammala, muna fatan samun wajen ajiye jiragen sojin sama a cikinsa domin hanzarta ɗaukar matakan tsaro,” a cewarsa.

Air Marshal Hassan Abubakar ya gode wa gwamnan bisa yadda ya fahimci cewar harin da sojin rundunar suka kai ba da gangan ba ne.

Ya bayyana cewa sojojin sun kai hari ne bisa bayanan sirri kan ayyukan ’yan bindiga, amma daga baya aka gano cewa wasu ’yan sa-kai sun rasa rayukansu a dalilin harin.

Ya tabbatar wa mutanen Zamfara cewa rundunar sojin sama za ta ci gaba da inganta ayyukanta domin kauce wa irin wannan kuskure a nan gaba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamna Lawal Sakamako Mai Kyau Zamfara yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m