Rasha Ta Kai Hari Mahaifar Shugaban Ukraine Zelensky
Published: 6th, March 2025 GMT
Jami’ai a Ukraine sun ce mutane huɗu sun mutu, 29 da suka jikkata, a wani harin makami mai Linzami da Rasha ta kai kan wani Otel a birnin Kryvyi Rih – Mahaifar shugaba Zelensky.
Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo masu sauran numfashi a ɓaraguzan gine-gine.
Wannan hari na zuwa ne sa’o’i bayan Amurka ta tabbatar da cewa ta daina musayar bayanan sirri da Ukraine — wanda haka zai kasance ƙalubale matuƙa ga Ukraine wajen iya daƙile hare-haren Rasha.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce masu aikin sa kai daga wata ƙungiyar bayar da agaji daga Amurka da Birtaniya na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a daren jiya.
Hakazalika, an kai wasu hare-haren birnin Odesa wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutum biyu da lalata manyan gine-gine biyu, kamar yadda gwamnan yankin, Oleh Kiper ya tabbatar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.
An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.
Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.
A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.
Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta tsananta kuma za a musu tiyata.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.
Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.
Daga Khadijah Aliyu