Masar Za Ta Bayyana Shirin Sake Gina Gaza A Yayin Taron Larabawa
Published: 3rd, March 2025 GMT
Babban jami’in diplomasiyyar kasar Masar ya sanar da cewa; Shirin da kasarsa take da shi na sake gina Gaza, abu ne mai yiyuwa a aikace, kuma za a aiwatar da shi ba tare da an kori mutane su bar Gaza ba.
Badr Abdul’adhy, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da fira ministan gwmanatin kwarya-kwaryar Falasdinu gabanin yin taron kasashen larabawa a birnin alkahira.
Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya ce; “Hanya daya tilo ta kawo karshen yawan fadace-fadace, shi ne a cusa wa Falasdinawa fatan jin cewa,abinda suke mafarki da shi mai yiyuwa ne a aikace,wanda shi ne kafa ‘yantacciyar kasarsu.”
Haka nan kuma ya ce; Shirin da Masar take da shi na sake gina Gaza, mai yiyuwa ne a aikace, kuma cikin wani matsakaicin zango na lokaci, bai kuma bukatar a ce sai mutane sun bar kasarsu.”
Wannan shirin na Masar dai ya zo ne bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce za a kori Falasdinawa su miliyan biyu daga Gaza saboda sake ginata da kuma yin wasu manyan gine-gine na kasuwanci.
Kalaman na shugaban kasar Amurka sun fuskanci mayar da martani mai tsanani daga Falasdinawa, kasashen Larabawa, da kuma wasu kasashen turai.
A nashi gefen, Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ya bayyana fatansa na samun cikakken goyon bayan kasashen larabawa domin aiwatar da shirin na kasar Masar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam
A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki da ake aikatawa a Gaza.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada wajibcin tunkarar muggan manufofin yahudawan sahayoniyya na tilastawa al’ummar Gaza da yammacin kogin Jordan yin hijira daga muhallinsu, yana mai bayyana halin ko in kula da kasashen duniya suke nun awa kan wadannan laifuka a matsayin abin mamaki da damuwa.
Araghchi ya kuma yi wa takwaransa na Masar bayani kan ci gaban tattaunawar Iran da Amurka kan Shirin makamashin nukiliya na zaman lafiya da ake takaddama a kai tsawon shekaru.