Kwanan nan, aka wallafa littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1 a kasar Sin, wanda kwalejin nazarin tarihi da adabi na kwamitin kolin JKS ya tace.

Littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1, ya kunshi muhimman ayyuka kuma na asali na rubutun Xi Jinping kan raya tattalin arziki daga watan Nuwamban 2012 zuwa Disamban 2024.

An tsara shi bisa tsarin lokaci, kuma ya kunshi rubuce rubuce guda 74 da suka hada da rahotanni, jawabai, laccoci, umarni da sauransu.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri 

Ruwan sama mai ƙarfi da ya sauka da safiyar ranar Laraba a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, ya haddasa ambaliya.

Ruwan wanda ya fara sauka tun da misalin ƙarfe 5 na Asuba, ya cika tituna da gidaje musamman a unguwannin Dala, Bulunkutu, titin Damboa, filin Polo, da Federal Low Cost.

Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu

Ambaliyar ta haifar da cikas a rayuwar jama’a, inda ruwa ya lalata dukiyoyi mutane masu tarin yawa.

Mutane da dama dun fice daga gidajensu domin neman mafaka, musamman waɗanda gidajensu ruwa ya mamaye.

Hakazalika, wasu tituna sun shafe sakamakon mamakon ruwan, lamarin da ya hana mutane fita ko komawa gidajensu da kuma yin ayyukansu na yau da kullum.

Wasu daga cikin mazauna garin sun ce ambaliyar ta tsananta ne saboda magudanan ruwa sun cika da shara irin su robobi, datti da tarkacen kayan gini.

Hakan ya hana ruwa tafiya yadda ya kamata.

Wani da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce mafi yawan magudanan ruwan Maiduguri ba sa aiki yadda ya kamata saboda sun toshe da shara.

Ya ƙara da cewa rashin kula da tsaftar muhalli ne ya haddasa irin wannan matsala.

A halin yanzu, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara sanya ido, ta tsaurara dokokin muhalli, da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin tsaftar gari.

Har ila yau, akwai buƙatar a gyara magudanan ruwa domin gujewa irin wannan ambaliya a nan gaba.

Masana sun gargaɗi jama’a cewa ana sa ran samum mamakon ruwan sama a makonni masu zuwa.

Amma an buƙaci jama’a su ɗauki matakan kariya da kuma haɗa kai da hukumomi domin shawo kan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu
  • Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu
  • NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
  • Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF
  • Kwamitin Kolin JKS Ya Shirya Taron Bita Tare Da Wadanda Ba ’Yan Jam’iyyar Ba 
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri 
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya