Ban fitar da ran lashe Premier League na bana ba — Arteta
Published: 2nd, March 2025 GMT
Mikel Arteta ya ce, Arsenal ce za ta lashe kofin Premier League na kakar bana, ba kamar yadda ake hasashen Liverpool ba.
A ranar Laraba Gunners, wadda take da tazarar maki 11 tsakaninta da Liverpool za ta fafata da Nottingham Forest a wasan mako na 27 a Premier League.
Ta ina Kungiyar Hizbullah ke samun kuɗaɗenta? An kama ɓarayin waya a KanoA ranar Lahadin makon da ya gabata, Liverpool ta yi nasara a kan Manchester City da 2-0 a Etihad, bayan Arsenal ta yi rashin nasara 1-0 ranar Asabar a Emirates ta hannun West Ham.
Bayan wasan na West Ham Mikel Arteta ya zargi ‘yan wasan da rashin sa ƙwazo a fafatawar, bayan Gunners shafe kaka 21 rabon ta da kofin Premier League.
Kociyan ɗan kasar Sifaniya ya kara da cewa, ‘‘Damar ɗaukar babban kofin tamaula na Ingila na bana ba a hannuna yake ba.’’
To sai dai a shirin da Arsenal ke yi na karawa da Forest a ranar Laraba, Arteta ya ce, ba zai taɓa fitar da ran lashe kofin Premier na kakar bana ba.
Arsenal wadda take sa ran ɗaukar Premier na kakar bana ta gamu da koma-baya, saboda wasu ’yan wasanta da ke jinya.
Kai Havertz da Gabriel Jesus za su ci gaba da jinya har bayan kakar bana, ana sa ran Bukayo Saka zai koma taka leda a cikin watan Maris.
Rabon da Saka ya buga wa Arsenal tamaula tun cikin Disamba, shi kuwa Gabriel Martinelli na ci gaba da jinya.
Kyaftin Odegaard ya yi jinyar da bai buga wasa 12 ba tun farkon fara wasannin bana, inda kuma aka dakatar da wasu ’yan wasan Gunners.
’Yan wasa biyar na Arsenal aka bai wa jan kati a wasa 26 a Premier League kawo yanzu.
Arsernal ta daɗe tana biye da Liverpool a teburin Premier League, wanda tuni Gunners ta kai zagaye na biyu a Champions League, amma an yi waje da ita a FA da Carabao Cup.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arsenal Mikel Arteta
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani.
Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa.
Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.