An ga watan Ramadan a Najeriya — Sarkin Musulmi
Published: 28th, February 2025 GMT
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Juma’a, wanda hakan ke nufin ranar Asabar, 1 ga watan Maris, ita ce daya ga watan Ramadan 1446 Hijira a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmi, ya karanta a fadarsa, ya bayyana cewa an samu sahihan bayanai daga kwamitocin ganin wata da shugabannin addinin Musulunci a sassa daban-daban na kasar nan.
a dalilin haka, ya ayyana fara azumin watan Ramadan daga safiyar Asabar.
Haka nan, hukumomin Saudiyya ma sun tabbatar da ganin watan, inda suka ayyana Asabar a matsayin daya ga watan Ramadan a kasar.
Kira Ga Musulmi
Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi riko da ibada, addu’a da taimakon marasa galihu a wannan wata mai alfarma.
“Yana da matukar muhimmanci a cikin wannan wata mu kasance masu sadaukarwa, taimakon mabukata da kuma yawaita addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban kasa,” in ji shi.
Ya kuma bukaci masu hali da su tallafa wa talakawa da gajiyayyu, musamman da abinci da sauran kayayyakin bukatu domin saukaka musu azumi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ga watan Ramadan Sarkin Musulmi
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya.
(Hoto: Onyekachukwu Obi).