Leadership News Hausa:
2025-04-30@23:24:51 GMT

Yadda Matasa Ke Kara Shiga Harkar Tsaface-tsaface

Published: 28th, February 2025 GMT

Yadda Matasa Ke Kara Shiga Harkar Tsaface-tsaface

A 2024, rundunar ‘yansanda ta Abuja, sun kama wani mai suna Nuhu Ezra, a yanikin Lugbe dauke da Kokon kan mutum da Kasuwansa, inda wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa, ya ci karo da Kokon kan mutum da Kasuwan ne, a yayin da yake yin farauta a cikin Dajin Kuje.

Kazalika, duk dai a 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar Ondo, sun cafke wani mai suna Yusuf Adenoyin, a yankin Isua, na karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas dauke da Kokon kan bil Adama guda takwas.

A Jihar Oyo ma, rundunar ‘yansanda ta jihar ta kama wasu mutane biyu a yankin Amuloko da ke garin Ibadan, bisa zargin samun dauke da danyen Kokon kan wata mata , da ba a san kowacce ba.

A 2023, mutane biyar kowannen su Kotu ta yankewa hukuncin zama gidan kaso na shekaru sha biyu, bayan sun amsa laifin na tuno Kokon kan bil Adama a Kabari, bisa umarnin Bokansu da ya yi masu alkawarin mayar da su masu kudi.

Duk dai a 2023, kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Neja DSP Wasiu Abiodun, a cikin sanarwar da ya fitar a jihar ya bayyana cewa, rundunar ta cafke wasu mutane biyar bisa zargin samun su dauke da Kokon kan mutum.

Ya ce, bayan rundunar ta bincike su, suka amsa cewa, wani Bokansu su ne, ya umarce su samo Kokon kan mutum don ya hada masu asiri su zama masu kudi, inda ya kara da cewa, sai dai Bokan ya arce.

Wannan rashin imanin na irin wadannan matasan har ya kai ga ya zama tamkar sana’a a tsakaninsu, musamman suna ganin ta hanyar ciro wasu sassan jikin ‘yan Adama ne, hanya mafi sauki a gare su, domin su zama masu arziki.

Lamarin na bakin ciki, sai kara zama ruwan dare yake yi a tsakanin wasu matasan kasar.

Wannan lamarin ya tuna mana da Clifford Orji fitaccen rikakken dan kungiyar asiri da ‘yansandan jihar Legas suka kama a ranar 3 na watan Fabirairun 1999. Orji, ya yi kaurin suna wajen sace mutane, musamman mata domin aikata ayyukan asiri.

Batun cire sassan jikin ‘yan Adama domin aikata asiri a kasar nan, kusan za a iya cewa, maimakon irin wannan dabbacin ya ragu, kusan za a iya cewa, karuwa ma yake kara yi a kasar, wanda za a iya danganta karuwar lamarin kan rashin daukar hukunci na doka kan lokaci, inda har a wani lokacin a kanga irin wanda ake zargin da aikata wannan ta’asar, suna ci gaba da yawon su a cikin alumma ba tare da an hukunta su, bisa doka ba

Dole ne a sauya irin wannan halin na rashin hukunta wadanda ake zargin domin mutane na bukatar sanin, shin yaushe ne, aka kama irin wadannan mutane da ake zargin su aikta wannan rashin imanin, shin an gurfanar da su a gaban Kuliya, domin yin haka ne kawai zai tabbatar da girmama dokar kasa da fito da mutatun kasar nan da kuma daidaita al’amura.

Akwai matukar bukatar wayar da kan matasa domin a sauya tunaninsu zuwa aikata dabi’u masu kyau, musamma domin a cire masu tunanin son yi arziki a cikin gaggawa, musamman ta hanyar kirkiro da shirye-shiryen wayar masu da kai, da kuma sanya shirye-shiryen a cikin manhajar karatun zamani don a rinka ilimanatar da su, kan illar son zama masu arziki, a cikin dare daya.

Kazalika, akwai gagarumar gudunmawar da Malaman addinai da Sarakunan Garjajiya za su bayar a matsayinsu na shugabannin alumma wajen ilimantarwa da fadakarwa, musamman a tsakanin matasa kan illar son yin arziki a dare daya.

Wannan zai iya faruwa ne kawai, idan shugabanin suma sun kasance masu hali na gari.

Bugu da kari dole ne gwamnati ta samar da ababen more rayuwa da samar da kyakyawan yanayi ga ‘yan kasar, musamman duba da yadda rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasan kasar ya zama ruwan dare a kasar.

Dole ne kuma gwamnatin ta rage ci gaba da fifita bangaren masu arziki kuma dole ta sani cewa, tsare-tsaren da ta fito da su da ke shafar rayuwar manyan mutane, haka suna shafar rayuwar matsakaitan alumomin kasar.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da ake zargin yansanda ta

এছাড়াও পড়ুন:

Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137

 

Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kar A Mika Wuya Ga “Damisar Takarda”
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
  • Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
  • Rashin tsaro: Gwamnan AbdulRahman Ya Gana Da Sarakuna Masu Daraja Ta Daya A Jihar Kwara 
  • Gwamna Namadi Ya Nada Aisha Mujaddadi Sabuwar Shugabar Hukumar InvestJigawa
  • Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Ci Gaba Da Killace Gaza Da Kashe Mutane, Laifi Ne Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba
  • Sama Da Masu Sayayya Daga Ketare 220,000 Ne Suka Halarci Bikin Baje Kolin Canton Karo Na 137
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA