Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura
Published: 27th, February 2025 GMT
Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya koma gidansa da ke Jihar Kaduna da zama, bayan shafe shekara biyu a Daura, tun bayan barinsa mulki a watan Mayun 2023.
Buhari, ya zaɓi yin rayuwa mai sauƙi bayan kammala wa’adin mulkinsa ba tare da shiga harkokin siyasa ba.
Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aikiYa samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da manyan jami’an gwamnati zuwa Kaduna.
Daga cikin tawagar da suka yi masa rakiya akwai Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, mataimakan gwamnan Jihar Katsina, Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, wasu tsofaffin ministoci, da wasu daga cikin hadimansa.
A lokacin da yake barin Katsina, jama’a da yawa sun taru don yi wa Buhari fatan alheri.
Daga cikin manyan da suka yi masa rakiya akwai Malam Mamman Daura, Musa Halilu (Dujiman Adamawa), da Bashir Ahmad.
Komawa Kaduna na nufin wani sabon mataki a rayuwarsa bayan shafe shekara biyu a Daura.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Buhari Daura Rakiya
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.
Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.
A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.
Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.
Abdullahi Jalaluddeen