MDD Ta Yi Gargadi Akan Tsanantar Yunwa A Kasar Sudan
Published: 27th, February 2025 GMT
A jiya Laraba ne dai Hukumar da take kula da harkokin jin kai dake karkashin MDD ( OCHA) ta bayyana cewa; Kusan shekaru biyu na yakin da ake yi a Sudan ya kara tsananta, kuma a halin yanzu yunwa wani abu ne da ya zama dahir ana ganinta a kasa a Sudan.
Babbar daraktan gudanar da ayyukan hukumar agajin ta MDD Edem Wosornu ta fadawa kwamitin tsaron MDD cewa; Da akwai mutane miliyan 12 da aka tarwasta daga gidajensu, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3.
Haka nan kuma ta kara da cewa; Tsarin kiwon lafiya na kasar ya durkushe baki daya, da akwai miliyoyin kananan yara da su ka daina karatu, wasu kuma an ci zarafinsu.”
Bugu da kari, saboda fadan da ake ci gaba da yi, an dakatar da kai kayan agaji zuwa sansanin ‘yan hijira mafi girma na Zamzam, alhali suna da bukatuwa da agajin.
A ranar Litinin da ta gabata ne dai kungiyar likitoci ba tare da iyaka ba ( Médecins Sans Frontières ) ta nuna rashin jin dadinta da yadda rashin tsaro ya tilasata ta dakata da ayyukanta a sansanin Zamzam.
Jakadan Sudan A MDD Al-Harith Idriss ya ce, kasarsa a shirye take ta samar da yanayin da zai bayar da damar ci gaba da gudanar da ayyukan agaji a kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wakilin Gidan Talabijin Na Al-Alam Ya Bayyana Yadda Shi Da Iyalansa Suka Rayu Kwanaki Biyu Babu Abinci A Gaza
Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba.
Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.”
Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar Juma’a mutanen Gaza sun yi ta yawo a kasuwanni, tituna, da unguwanni ba tare da samun kilo guda na gari ba.