HausaTv:
2025-08-01@05:01:57 GMT

China: Kokarin Amurka Ta Haddasa Sabani Tsakanin Moscow Da Beijin Ba Zai Yi Nasar Ba

Published: 27th, February 2025 GMT

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lin Jian ne ya jaddada cewa, alakar da take a tsakanin Rasha da China ba ta tasirantuwa da shiga tsakanin wani bangare na uku, sannan kuma ya ce, kokarin da Amurka take yi na haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu ba zai yi  nasara ba.

A wani taron manema labaru da kakakin ma’aikatar harkokin wajen na China ya gabatar, ya bayar da jawabi akan tambayar da aka yi masa akan maganar da ta fito daga bakin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio cewa; Rasha ta dogara ne China, kuma kasashen biyu za su iya hada kai su yi fada da Amurka.

Li Jian ya kuma ce; Ba tare da la’akari da sauye-sauyen da za su bijiro a fagen siyasar duniya ba, alakar kasashen China da Rasha za ta ci gaba da bunkasa sannu a hankali,don haka kokarin Amruka na haddasa sabani a tsakaninsu ba shi da ma’ana.

A baya kadan shugaban kasar china Xi Jin Ping ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladmir Puitn inda ya bayyana masa cewa, alakar kasashen biyu ba za ta tasirantu ba daga tsoma bakin bangare na kuku.

Ita kuwa fadar mulkin Rasha “Kremlin” ta sanar da cewa, alaka a tsakanin Rasha da China da siyasarsu ta waje suna taimakawa wajen samar da zaman lafiya a duniya, kuma ba a gina alakar tasu domin fada da wani bangare ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai

Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu.

A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci.

Haka nan kuma ya ce; Daga cikin manufofin da HKI ta Shata cewa za ta cimmawa a yayin yakin, shi ne samar da sauyi a cikin wannan yankin, shi ya sa da dama daga cikin hukumomin kasashen larabawa su ka fahimci cewa raunana Iran yana nufin raunana kasashensu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata
  • Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
  • Gidauniyar ‘Ya’yan Sarakunan Arewa Sun Marawa Sarkin Musulmi A Matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna
  • Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri 
  • Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu
  • Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya
  • Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Rasha Ta Mayar Da Martani Ga Shugaban Amurka Kan Gindaya Wa’adin Kawo Karshen Yakin Ukraine