Gwamnatin Kwara Ta Kaddamar Da Kwas Ga Dalibai Makarantun 50
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da shirin horas da makarantun firamare da kananan makarantun gwamnati 50 a fadin jihar domin su iya amfani da fasahar ziyyana shafin internet.
Da yake gabatar da shirin a madadin Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a Makarantar Sakandare ta Bishop’s Smith Junior Ilorin, babban mai ba gwamna shawara na musamman, Alhaji Sa’adu Salau, ya ce shirin na dijital ya kasance don ƙarfafa fannin ilimi.
A cewarsa shirin ya shafi sama da dalibai 150 a kowace makarantu 50 na gwamnati a matakin gwaji.
Ya ce idan aka kafa harsashin tsarin zamani, yaran jihar Kwara ba za su koma baya a tsakanin takwarorinsu na duniya ba.”
Gwamna AbdulRazaq yace sauran makarantun gwamnati da za su ci gajiyar wannan karimcin a babban birnin kasar sun hada da makarantar Sarauniya Elizabeth, Makarantar Grammar Ilorin, da kuma makarantar firamare ta Sheikh Alimi.
A nasa bangaren, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kwara kan harkokin dijital da kirkire-kirkire, Ishola Kayode, ya ce manufar shirin shi ne tabbatar da cewa daliban makarantun gwamnati ba su koma baya ba a duniyar dijital.
Ya ce daliban za su zama masu ilimin zamani, inda ya ce za su iya magance matsalolin da ke addabar al’ummarsu.
Ya ce za a fadada shirin bayan tantance bayanan da aka yi.
A nata jawabin shugabar makarantar Bishop’s Smith College (Junior Session), Mrs Akanbi Janet Ayoola, ta ce aikin na daya daga cikin mafi kyawun shawarar da gwamnatin jihar ta dauka a zamanin da fasahar sadarwa da fasahar kere-kere suka zama abin bukata na rayuwa.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Na Ci Gaba Da Kyautata Rayuwar Al’umma Ta Amfani Da Hidimomin Dijital Da Na Kirkirarriyar Basira
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp