Hamas ta yi tir da matakin Isra’ila na shirin takura masu ibada a masallacin Quds
Published: 26th, February 2025 GMT
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar Juma’a a harabar masallacin Al-Aqsa, tana mai cewa matakin wani lamari ne mai matukar hadari da ke da nufin tauye ‘yancin addini.
Hamas ta ce, umarnin ‘yan sandan Haramtacciyar Kasar Isra’ila cin zarafi ne ga dukkan ka’idoji, yarjejeniyoyin da kuma dokoki na kasa da kasa, sannan kuma hakan tsokana ce kai tsaye ga musulmi.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa, irin wadannan tsare-tsare ba za su yi tasiri wajen sauya asali da tarihin masallacin Al-Aqsa ba.
Bugu da kari kuma Hamas ta dora alhakin abin da hakan zai iya haifarwa a kan gwamnatin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayin kin musulunci.
Daga karshe kungiyar Hamas ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kasashen duniya da su dauki tsauraran matakai domin dakile wannan mataki na keta alfarmar masallacin Al-Aqsa, da kuma tabbatar da cewa al’ummar Palastinu na gudanar da ibadarsu cikin ‘yanci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza
A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.
Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.
A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat” mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.
A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.