An Nada Obasanjo Mai Shiga Tsakani A Rikicin Congo
Published: 26th, February 2025 GMT
An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo.
Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo inda yaki ya kazanta a gabashin ƙasar.
Shugabanin kasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi nadin a wani yunƙuri na kawo karshen yaƙin basasa a gabashin Congo, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da hukumomi na gwamnatin tsakiya.
Da yammacin jiya Litinin, suka fitar da sanarwar cewa sun nada tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo a matsayin wadanda za su taimaka wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar sulhu.
“An bukaci dukkan bangarorin su mutunta tsagaita wutar da aka ayyana a taron EAC da SADC, kuma an yi kira ga M23 da kuma sauran bangarorin su dakatar da kutsawa cikin gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo tare da mutunta tsagaita wuta,” in ji kungiyoyin a wata sanarwar da suka fitar.
Har yanzu kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU sun gaza shawo kan rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongon wanda ya laƙume rayukan fararen hula da dama.
Yaki a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 7,000 a wannan shekarar, kamar yadda Firaiministar kasar Judith Suminwa Tuluka ta shaida wa kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta.
A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025.
Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai.
Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin biyan fansho.
Ya kara da cewa, wannan yunkuri ya yi daidai da kudirin jihar gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki, tare da bai wa ‘yan fansho dama su gyara duk wani bayanin da bai cika ba a takardunsu.
Shi ma da ya ke jawabi, Akanta Janar na Jihar, Alhaji Abdullahi S.G. Shehu, ya jaddada cewa aikin tantancewar zai bai wa ‘yan fansho damar sabunta bayanansu da suka bace ko suka canza a takardunsu.
Saboda haka, ya bukaci dukkan ‘yan fansho daga ma’aikatun gwamnati, sassan hukumomi, kananan hukumomi da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi da su halarci tantancewar a ranar da aka tsara kamar yadda yake cikin jadawalin aikin.
A jawabinsa, Shugaban kungiyar kananan hukumomi ALGON ta Jihar Jigawa, Farfesa Salim Abdurrahman, ya tabbatar da cikakken goyon baya daga shugabannin kananan hukumomi 27 domin cimma burin aikin.
Shugaban na ALGON wanda shugaban karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani ya wakilta, ya bukaci ‘yan fanshon da su ba da cikakken haɗin kai don samun nasarar shirin.
Shi ma Shugaban hukumar, Dr. Bilyaminu Shitu Aminu, ya bukaci ‘yan fansho daga sassa daban-daban da su ba da hadin kai domin cimma burin da aka sanya, tare da jaddada cewa su ziyarci sakatariyar kananan hukumominsu domin a tantance su.
Shugaban Kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jihar Jigawa, Alhaji Umar Sani Babura, ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta bada cikakken goyon baya domin nasarar wannan shiri.
Dukkan ‘yan fansho daga Ma’aikatun Gwamnati, Kananan Hukumomi, da Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi da ke cikin tsarin fanshon, ya zama wajibi su halarci wannan tantancewa a ranakun da aka tsara a jadawalin aikin.
Usman Muhammad Zaria