Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano
Published: 18th, February 2025 GMT
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al’umma ta Jihar Kano mai suna ‘Kano State Security Neighborhood Watch.’
Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne tare da wasu ƙarin dokokin guda biyu, waɗanda suka haɗa da dokar gyara hukumar sufuri ta jihar da kuma wadda ta kafa cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar ta ce gwamnan ya amince da dokokin ne a zaman majalisar zartarwar jihar na 25 da ya gudana a fadar gwamnatin jihar.
Hakan na zuwa ne bayan dokar samar da rundunar tsaron ta bi matakan da suka kamata a majalisar dokokin jihar.
Kano dai na fama da matsaloli irin na rikice-rikicen dabanci da ƙwacen waya, lamarin da ya yi sanadiyar ajalin mutane da dama.
Me Abba ya ce?A jawabinsa bayan rarraba hannu dokokin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin an samu ribar dimokuraɗiyya da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya kuma jaddada cewa gwamnati ta tsaya tsayin daka a ƙoƙarinta na ɓullo tare da aiwatar da manufofi da tsare-tsare da nufin inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.
Gwamna Yusuf ya bayyana jin daɗinsa dangane da irin goyon baya da haɗin kai da jama’a ke ba su, inda ya buƙaci da su ci gaba da gudanar da ayyukansu domin cimma manufofin gwamnatin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kano State Security Neighborhood Watch Rundunar Tsaron Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA