Ku tona asirin ’yan tsubbu —Sarkin Ilori ga malaman addini
Published: 17th, February 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya buƙaci a riƙa tona asirin malaman tsubbu a duk inda suke.
Sarkin wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, ya buƙaci malaman Musulunci da su riƙa fallasa duk masu fakewa da rigar malumta suna ayyukan tsubbu.
Basaraken ya buƙaci malaman addini da “su tsaftace harkar tasu, tare da tona asirin ɓata-garin cikinsu ga jami’an tsaro kafin miyagun su kai ga aikata munanan ayyukansu ko halaka jama’a.
Ya yi wannan kira ne bayan kisan gillar da wani mai iƙirarin malumta mai suna Abdurrahman Bello, ya yi wa wata ɗaliba ’yar ajin ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ake Ilori, mai suna Hafsah Lawal.
A cikin sanarwar da basaraken ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Abdulazeez Arowona, a ranar Lahadi, ta umarci “malaman addini musamman limaman masallatan da ke Masarautar Ilori da ma faɗin Jihar Kwara, da su karkatar da huɗubobinsu kan inganta tarbiyya da kuma muhimmancin kare ran ɗan Adam, ba tare da la’akari da addini ko ƙabilanci ba.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan tsubbu Sarkin Ilori Sulu Gambari
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar
Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp