Aminiya:
2025-11-03@03:58:53 GMT

Malaman addini sun yi wa ’yan siyasa juyin mulki —Sule Lamiɗo

Published: 17th, February 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo, ya zargi malaman addini da neman ƙwace lamurran siyasar Najeriya daga hannun ’yan siyasa.

Sule Lamiɗo ya nuna damuwa bisa yadda malaman addini ke ƙara shiga harkokin siyasa, inda ya ce, a halin yanzu malaman suna yin tasiri sosai a yanayin tafiyar siyasa da kuma jefa ƙuri’a.

Ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, bisa rasuwar babban ɗansa a Jihar Kaduna.

A cikin bidiyon ta’aziyyar, an ji Sule Lamiɗo, yana cewa, malaman addini sun yi wa ’yan siyasa ƙwace, inda suke fitowa fili suna yi wa ’yan takara yaƙin neman zaɓe, tare da kiran mabiyansu su zaɓi wanda su suke goyon baya.

Tsohon Ministan Harkokin Wajen na Najeriya ya ce, “duk da ni’imar da Allah Ya yi musu na kasancewa malaman addini, amma yanzu sun koma yin kokawa da ’yan siyasa.

“Kamata ya yi malaman addini su zama iyaye masu shiryatar da al’umma, amma tunda mulki suke so, to mun ’yan siyasa za mu bar musu, mu koma gefe.”

Cikin shaguɓe ya ci gaba da cewa, “muna jira su fito su gaya mana wanda suke so mu zaɓa gwargwadon abin da suke so.” Sannan ya ce, “Idan har ana so a samu adalci da daidaito a Najeriya, to dole sai kowa ya tsaya a matsayinsa a cikin al’umma.”

Jigon Jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana cewa an wayi gari rikicin cikin gida da rarrabuwar kai sun dabaibaye ƙungiyoyin da ɗarikun addini, kamar yadda jam’iyyun siyasa ke fama da waɗannan matsaloli.

Daga nan sai ya ce muddin ba a samu haɗin kai ba, tsarin siyasar Najeriya ba zai taɓa rabuwa da rikici ba.

Tasirin malamai a siyasar Najeriya

A baya malaman addini sun yi tasiri matuƙa wajen sanya magoya bayansu su yi rajistar zaɓe.

Amma a zaɓen 2023, wanda ake wa kallon rarrabuwar kai ta dabaibaye fiye da kowanne, malaman sun zarce hakan, inda suka riƙa bayyana ’yan takarar da suke goyon bayan.

Lamarin ya kai ga wasu malaman suna fitowa a huɗubobinsu, suna  bayyana ɗan takarar da suke goyon baya a cikin ’yan takara.

Wasu malaman Musulunci sun rika shawarar mabiyansu da su kaɗa kuri’a bisa la’akari da addinin ’yan takara. A ɗaya ɓangaren kuma, malaman Kirista sun riƙa iƙirarin samun ilhama gane da ɗan takarar da zai lashe zaɓen na 2023. Sai dai kuma mafi yawan waɗannan iƙirarin ba su abbata da.

Dambarwar malaman addini

Ko a baya-bayan nan, taƙaddama ta ɓarke tsakanin malaman Musulunci kan taron Mahaddata Al-Ƙur’ani da aka shirya gudanarwa a Abuja ranar 22 ga watan nan na Fabrairu, 2025, inda ake sa ran tara Mahaddata da Masu Zayyana da makaranta Al-Kur’ani mutum 30,000.

An ɗage taron zuwa abin da hali ya yi damuwar da wasu malaman Musulunci suka nuna kan halascin taron da kuma zargin cewa yana da alaƙa da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Takarar Muslim-Muslim

Idan ba a manta ba dambarwar zaɓen Musulmi da Musulmi a lokacin takarar Shugaba Bola da mataimakinsa Kashim Shettima  ya tayar da ƙura a fagen siyasar Najeriya a kakar zaɓen 2023.

Amma dai ’yan takarar sun kai labari a zaɓen saboda gagarumar goyon bayan da wasu malamai suka ba shi, suka kuma kwaɗaita wa mabiyansu alherin da ke tattare da hakan.

Bambancin addini da kabilanci sun kuma yi tasiri a yankin Kudu maso Yamma a kakar zaɓen.

A yankin Arewa muƙarraban Tinubu sun nema kuma sun samu goyon bayan manyan malaman addini wajen tallata shi. Da alama kuma irin haka ta sake kunno Kai, duba da yadda manyan ’yan siyasa suka fara shirye-shiryen zaben 2027.

Sai dai kuma akwai alama tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi, ya far sauya taku, inda a wannan karon yake ƙara matsa ƙaimi domin samun gagarumar goyon baya a yankin Arewa, inda Musulmi suka fi rinjaye.

Ana ganin halartarsa tarukan buɗa-baki a lokacin azumin watan Ramadan da kuma shigarsa harkokin da suka shafa al’ummar da kuma bayar da gudunmawar kuɗaɗe a matsayin wani salo na zawarcin al’ummar yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Siyasa Takara siyasar Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano

Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.

 

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori November 1, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia Suluhu Hassan ta yi tazarce
  • Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari