Al’ummar Gundumar Kano Ta Arewa Sun Dara Bayan Kwashe Shekaru 10 Ba Ruwan Sha
Published: 17th, February 2025 GMT
An samar da ruwan sha a yankunan Danbatta, da Makoda da Minjibir dake gundumar Kano ta Arewa bayan kwashe kimanin shekaru goma.
Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka a wani rangadin da ya kai kananan hukumomin uku domin tantance yadda ake samar da ruwan sha ga al’umma.
Umar Doguwa ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu sosai wajen samar da ruwan sha a dukkan lungu da sako na jihar Kano.
Ya ce an gyara kananan cibiyoyin samar da ruwan sha a yankunan inda ake samar da ruwa babu kakkautawa.
Kwamishinan ya ce yanzu haka ana samun ruwan sha a kauyukan kunya, da Kilawa da ,wailare duk a karamar hukumar Minjibir yayin da ake kokarin ganin an samar da ruwan sha na karamar hukumar Danbatta.
“Abin takaici ne matuka, duk wadannan kauyukan sun shafe sama da shekaru takwas babu ruwa, duk da cewa suna da cibiyoyin samar da ruwan“.
Ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike a wadannan kauyukan domin tabbatar da cewa an gyara dukkan bututun da a halin yanzu wasu sun yi tsatsa da sauran matsaloli sakamakon rashin amfani da su na tsawon shekaru.
Doguwa ya kara da cewa, hakan na nuni da kokarin gwamna Abba Kabir Yusuf na farfado da samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar.
Umar Haruna Doguwa ya ci gaba da cewa gwamnati ba za ta ragawa duk wanda aka samu yana karkatar da ruwan da aka tanadar don sha da amfanin gida ba zuwa gonaki don noman rani.
Abdullahi Jalaluddeen
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ruwan Sha samar da ruwan sha ruwan sha a
এছাড়াও পড়ুন:
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi.
Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar.
Kowace kasa tana da cikakken iko da ’yancin zabar manufofi da matakan da ya dace da ita. Da Sin ta tsaya kai da fata cewa ba za ta ba da kai a yakin haraji da Amurka ta tayar ba, hakan ya sa Amurka yin karatun ta nutsu, kuma ta tuntubi bangaren Sin domin tattaunawa.
Wadannan misalai sun nuna mana cewa, akwai hanyoyi masu sauki da inganci na samun maslaha, kuma shawarwarin da Sin take gabatarwa, su ne suka dace da yanayin duniya a yanzu. Ba dole sai kowa ya samu abun da yake so ba, amma hawa teburin sulhu da tuntubar juna tana taka muhimmiyar rawa wajen warware sabani, da lalubo inda kowane bangare zai iya saki, domin a samu mafitar da za ta karbu ga kowa. Kuma irin wannan din, shi ne burin sabuwar Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar a baya bayan nan. Duniya ba ta bukatar mayar da hannu agogo baya ta hanyar tayar da rikice-rikice da danniya da nuna fin karfi, zamani ya sauya kuma dole salon tafiyar da harkoki ya sauya, domin dacewa da yanayin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp