Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon
Published: 16th, February 2025 GMT
An kammala aikin gina wani jirgin ruwa sabon kira mai bambaro saman ruwa, da samarwa, da adanawa, da saukewa wato FPSO a takaice, wanda ke da na’urar rike iskar carbon da wurin adanawa, a Shanghai, a cewar Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin.
Jirgin dai shi ne irinsa na farko a duniya kuma ana shirin isar da shi a karshen watan Fabrairu, a cewar jaridar.
Jirgin na FPSO mai tsayin mita 333 da fadin mita 60, yana iya samar da danyen mai har ganga 120,000 a kowace rana. Kana yana iya aiki na musamman wajen rike iskar carbon dioxide da aka samar yayin kewayawa da ayyukan samar da mai. Bugu da kari, yana amfani da makamashin zafi daga iskar gas don samar da wutar lantarki, tare da cimma manufofi biyu na kare muhalli da tsimin makamashi, a cewar rahoton. (Mohammed Yahaya)
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun hada da kamfanonin kasuwanci guda biyar, hudu da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, daya kuma a kasar Turkiyya, wadanda suka sayar da albarkatun man fetur na kasar Iran ga kasashe uku, da kuma wasu kamfanonin jigilar kayayyaki guda biyu.
A cikin sanarwar da sakataren harkokin wajen kasar ta Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce “Matukar dai Iran na son samar da kudaden shiga na man fetur da sinadarai don samar da kudaden gudanar da ayyukanta na tabarbarewar zaman lafiya, da kungiyoyin da ya bayyana da na ta’addanci to Amurka za ta dauki matakin laftawa Iran da dukkan kawayenta alhakin kaucewa takunkumi.”
Matakin na zuwa ne jim kadan bayan Iran ta sanar da cewa za a sake gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa da gwamnatin shugaba Donald Trump a birnin Rome a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a karkashin jagorancin kasra Oman.