Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan wanda a Ondo
Published: 17th, February 2025 GMT
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo.
Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu.
An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a AbiyaAna zargin al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, amma ba a samu cikakken bayani ba sai zuwa ranar Lahadi.
Wani mazaunin Ifon, wani gari da ke iyaka da Jihar Edo, ya shaida wa Aminiya cewa mutuwar matashin ta sa al’umma da abokansa yin bore.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun a ranar masoya.
Samun labarin mutuwar matashin ke da wuya, sai matasan suka ɗunguma zuwa ofishin ’yan sanda..
Ya ce ’yan sandan sun kasa shawo kan masu boren da suka mamaye ofishin, inda suka banka masa wuta a fusace.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin.
Ta kuma ƙara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar, Wilfred Afolabi, na kan hanyarsa ta zuwa Ifon domin ta tabbatar da zaman lafiya da kuma hana sake aukuwar wani tashin hankali.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
Wasu mutum shida sun shiga hannun ’yan sanda kan zargin satar zinari da kuɗinta ya haura Naira miliyan 109.5 a Jihar Kebbi.
Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda a jihar Kebbi na tuhumar su da sace sarkoƙin zinare guda biyar sauran kayan zinare daga wani gida a garin Ka’oje, Ƙaramar Hukumar Bagudo.
Sauran sun haɗa da zobba huɗu da munduwar hannu tara, da nauyinsu ya kai gram 782.7 — dukkansu mallakar ’ya’ya da ’yan uwar mai gidan.
Wanda ake tuhuma ya amsa laifiBayan samun koken, jami’an suka kama Ibrahim Abubakar Ka’oje, jami’i a Hukumar Gyaran Hali ta Kasa, wanda a yayin bincike, ya amsa laifin.
’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhuYa bayyana cewa ya sayar da kayan ga wasu mutane biyu, dukkansu daga Sakkwato, tare da wasu mutum biyu a Jihar Kebbi.
An kuma gano wanda ya taimaka masa wajen sayar da wasu daga cikin kayan, inda ya karɓi naira miliyan 2.5 a matsayin lada.
Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa har yanzu tana neman sauran da suka gudu, bisa zargin taimakawa wajen sayar da kayan sata.
Ana zargin an sayi filaye biyu a Birnin Kebbi da kuɗin da aka samu daga sayar da kayan.
Abubuwan da aka ƙwatoKayan da aka ƙwato sun haɗa da munduwar hannu biyu, babur ɗin Haouje, da kuma wayoyin iPhone 16, Samsung Galaxy Ultra da Samsung Flip.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya jinjina wa jajircewar jami’ansa bisa wannan nasara.
Ya kuma yi kira gare su da su ci gaba da aiki tukuru domin cafke sauran da ake nema da kuma ƙwato dukkan kayan da suka rage.