Kungiyoyi 70 Na Amurka Sun Bukaci Trump Ya Yi Watsi Da Shirinsa Kan Gaza
Published: 15th, February 2025 GMT
Kungiyoyin kare hakkin fararen hula da kungiyoyin fafutuka sama da 70 ne suka bukaci shugaban Amurka Donald Trump da ya yi watsi da shirinsa na kwace iko da yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kaura zuwa kasashe makwabta.
Wasikar da aka aike wa Donald Trump ta bayyana matukar damuwar kungiyoyin da suka sanya hannu kan shirin korar Falasdinawa kusan miliyan biyu daga kasarsu ta asali.
Wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun yi kira ga gwamnatin Amurka mai ci da ta karfafa yunkurin diflomasiyya a baya da ya kai ga tsagaita bude wuta a Gaza, maimakon aiwatar da manufofin da za su kawo cikas ga yankin yammacin Asiya.
A cikin wasikar da suka fitar sun ce matakin na Amurka kan Gaza na iya haifar da martani mai karfi daga kasashen Larabawa da na musulmi, da jawo sojojin Amurka cikin sabbin yake-yake marasa iyaka, wanda hakan zai haifar da karin rikici a yankin.”
Wasikar ta bukaci Trump da ya yi aiki da abokan huldar yankin don sake gina Gaza ba tare da korar mazaunanta ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa
Ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce fiye da sojojin kasar 20,000 ne suka ji rauni tun farkon yakin da aka fara a Gaza a watan Oktoba 2023, inda fiye da rabinsu ke fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, ciki har da ciwon damuwa.
A cewar sashen bayar da shawarwari na ma’aikatar, kusan kashi 56 cikin 100 na wadanda suka ji rauni sun kamu da wasu matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ke nuna irin tasirin matsalar kwakwalwa da wannan rikici ke haifarwa.
Ma’aikatar ta kara da cewa kusan kashi 45 cikin 100 na wadanda suka ji rauni suna fama da raunuka a jiki, yayin da kashi 20 cikin 100 na sojojin ke fama da matsalolin kwakwalwa da na jiki a lokaci guda.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Iran Ta Bayyana Shirinta Na Halartar Taron Shekara-Shekara Na Hukumar Makamashin Nukiliya September 14, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Bayyana Rashin Halarta Tawagarta A Kada Kuri’a Kan Batun Falasdinu September 14, 2025 Tsananin Masifar Da Falasdinawa Ke Ciki A Gaza Saboda Hare-Haren Gwamnatin Mamayar Isra’ila September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci