’Yan Najeriya 52,000 za su sauke farali a 2025
Published: 13th, February 2025 GMT
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025.
Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar.
An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a RibasTa ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025.
Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya.
Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, bayan tuntuɓar shugabannin hukumar a jihohi da wakilin fadar shugaban ƙasa.
Shugaban ya tabbatar da ƙulla yarjejeniya da waɗanda za su kasance masu hidima tun da wuri don guje wa fuskantar tsaiko.
Wannan matakin yana da muhimmanci saboda ana sa ran fara aikin samar da biza ga maniyyata daga ranar 19 ga watan Fabrairu.
Shugaban NAHCON ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, bisa goyon baya da taimakon da yake bai wa hukumar.
Ya ce hukumar za ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa maniyyata sun samu damar yin Hajji cikin sauki da kwanciyar hankali.
Ya kuma buƙaci su ci gaba da bibiyar kafofin sadarwa na NAHCON don samun sabbin bayanai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farfesa Pakistan Kasar Saudiyya tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasu
Allah Ya yi wa Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Muslunci a Najeriya, Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah, rasuwa.
Babban Mufti na ƙasar Yarbawa, Sheikh Daood Imran Molaasan, ne ya sanar da rasuwar Sheikh Abdul Rasheed Hadiyatullah a cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a kai a daren Litinin.
Sai dai bai bayar da cikakken bayani game da inda Sheikh Hadiyatullah ya rasu ko kuma lokacin da hakan ya faru ba.
Sheikh Molaasan ya bayyana cewa rasuwar marigayi Sheikh Hadiyatullah ta bar giɓi mai wuyar cikewa a shugabancin Musulunci na ƙasar.
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya“An haife shi a garin Iwo a Jihar Osun kuma an san shi da dabi’u Musulunci. Sheikh Hadiyatullah ya kasance fitaccen malamin Musulunci kuma masanin shari’a, wanda an san shi da ƙoƙarinsa na neman a aiwatar da Shari’a Musulunci a tsarin mulkin Najeriya, tattaunawa tsakanin addinai, da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin Najeriya masu bambancin addini.
“Ya yi aiki a matsayin Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci na tsawon shekaru, inda ya jagorance ta a lokutan ƙalubalen zamantakewa da ci gaba.
“Sheikh Hadiyatullah ya fara karatun addinin Musulunci a wurin malaman gida kafin ya ci gaba da karatunsa a ƙasashen waje.
“Ya samu girmamawa a faɗin Najeriya da ma wajenta saboda zurfin ilminsa a fannin fiƙihun Musulunci da kuma salon shugabancinsa mai nutsuwa da tsayin daka kan akida,” kamar yadda Molaasan ya bayyana.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta wa Sheikh Hadiyatullah ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.