Gwamnatin Zamfara Na Biyan Ma’aikatan Bogi N193.6m Duk Wata
Published: 13th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Zamfara ta bankaɗo ma’aikatan bogi 2,363 da ke karɓar jimillar N193,642,097.19 a kowane wata bayan gudanar da tantancewar ma’aikatan gwamnati.
Gwamna Dauda Lawal ya kafa kwamitin tantance ma’aikata a watan Agustan bara don tabbatar da biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000. Kakakin gwamnan, Sulaiman Idris, ya bayyana cewa binciken ya nuna akwai ƙananan yara 220 da ke karɓar albashi a matsayin ma’aikatan gwamnati.
Rahoton kwamitin ya tabbatar da cewa an tantance ma’aikata 27,109, yayin da 2,363 suka kasance ma’aikatan bogi, 1,082 sun dace su yin ritaya, 395 na aikin kwantiragi, 261 ba su cikin jerin ma’aikata, 213 suna hutun karatu, 220 ƙanana ne, sannan 67 suna aiki a wasu wurare. Binciken ya kuma gano cewa ma’aikata 75 sun samu aiki ba bisa ƙa’ida ba, kuma dukkansu ƙanana ne a lokacin da aka ɗauke su aiki.
Kwamitin ya bada shawarar dakatar da ma’aikata 207 da ba a tantance ba, waɗanda ake biyansu N16,370,645.90 a kowane wata. Haka nan, an gano ma’aikata 12 a cikin jerin masu albashi amma ba su cikin bayanan ma’aikata, inda suke karɓar N726,594 a kowane wata. Gwamnati ta ce za ta ci gaba da wannan tantancewa don tabbatar da gaskiya da rikon amana, musamman duba da fara biyan mafi ƙarancin albashi daga watan Maris.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Da Stellar Steel, Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Habaka Karafan Cikin Gida
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa October 31, 2025
Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025