Aminiya:
2025-09-18@03:45:43 GMT

An yi wa kashi 25 na matan Nijeriya kaciya

Published: 12th, February 2025 GMT

Masu fafutikar kare haƙƙin bil Adama da ƙwararru a fannin kiwon lafiya haɗi da fasihai a ɓangaren shari’a sun buƙaci a tsananta hukunci kan masu yi wa mata kaciya a Nijeriya.

Masu ruwa da tsakin sun yi kira da a ƙara wayar da kan al’umma domin ganin an daƙile kaciyar mata gaba ɗaya a ƙasar nan.

Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa

A yayin wani taro da aka gudanar kan kawo ƙarshen kaciyar mata a Nijeriya, Nora Agbakhamen, wanda ta assasa Pulse Narrative, ta ce fiye da mata miliyan 200 a faɗin duniya sun fuskanci wani nau’i na kaciya, lamarin da ya shafi kashi 25 cikin 100 na matan Nijeriya.

Agbakhamen ta ce duk da cewa dokokin ƙasa da ƙasa sun ayyyana kaciyar mata a matsayin wani nau’i na cin zarafi da keta haddi, har yanzu matsalar na ci gaba da ta’azzara a sakamakon rashin tsananta hukunci.

A cewarta, akwai buƙatar a haɗa kai da duk masu ruwa da tsaki musamman tare da ƙwararru a fannin kiwon domin wayar da kan al’umma wajen ganin an kawo ƙarshen wannan matsalar.

Mohammed Abubakar na Masarautar Chokalin Fika da ke Jihar Yobe, ya ce sarakunan gargajiya tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da wayar da kan al’ummominsu kan illolin da ke tattare da kaciyar mata.

Ya bayyana cewa Gwamnatin Yobe ta shimfiɗa dokoki masu tsanani kan masu yi wa mata kaciya domin ganin an shawo kan matsalar.

Yayin da yake bayyana rawar da sarakunan gargajiya suke takawa, ya buƙaci ƙarin haɗin gwiwa domin tunkarar wannan annoba ta hanyar wayar da kan al’umma da shimfiɗa dokoki masu tsanani.

Wata ma’aikaciyar jinya kuma mai fafutikar yaƙi da cin zarafin mata, Amina Waziri Abdullahi, ta bayyana kaciyar mata a matsayin wani nau’i na cin zarafi da yake da mummunan tasiri ga rayuwar mace.

Shi ma wani wani lauya kuma mai fafutikar kare haƙƙin mata, Kowoabi Takoni, ya buƙaci a sanya haddin da ya zarce Naira dubu 200 da a yanzu ake karɓa a wurin waɗanda aka kama da laifin.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: cin zarafi Kaciyar Mata kaciyar mata

এছাড়াও পড়ুন:

NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025

A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.

Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi
  • Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata