Gwamnati Na ɗaukar Matakai Don Rage Farashin Abinci Ta Hanyar Zuba Jari A Noma – Minista
Published: 12th, February 2025 GMT
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba.
“Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu yana da yawa, farashin sa yana sauka da kan sa.
Ministan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannin tsaro, inda ya ce a shekarar 2024 jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 8,000, sun kama mutum 11,600, tare da ƙwato makamai fiye da 10,000.
Ya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ake yi yana sa hanyoyi na ƙara zama lafiya.
Ya ƙara da cewa, “Ko da yake har yanzu muna da aiki a gaba, hanyoyin mu sun fara zama mafi aminci.
“Hanyar Abuja zuwa Kaduna, wadda aka fi sani da rashin tsaro, tana daga cikin misalan da ke nuna irin cigaban da muke samu.
“Kamar yadda na faɗa, har yanzu akwai aiki da yawa a gaba, kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba.
“Haka kuma, sama da mutum 8,000 da aka sace an kuɓutar da su cikin nasara.
“Za mu ci gaba da ƙoƙarin rage yawan waɗanda ake sacewa tare da bunƙasa nasarorin mu wajen hana laifuka, gano masu ma’aikatan su, da kuma hukunta su.”
Idris ya ƙara da cewa, bayan da Kotun Tarayya ta ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ’yan ta’adda, jami’an tsaro sun samu cikakken ikon amfani da ƙarfin da ya dace wajen murƙushe su.
Dangane da tattalin arziki, Ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa suna samar da ingantaccen sakamako, musamman cire tallafin fetur wanda ya hana asarar ɗaruruwan biliyoyin naira a kowace shekara.”
Ya jaddada cewa shigar da tsarin Electronic Foreign Exchange Matching System (EFEMS) a watan Disamba na 2023 ya inganta gaskiya a harkar canjin kuɗi, inda ya taimaka wajen warware bashin dalar Amurka da aka tara tun baya, da kuma dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari.
“Makon jiya, Naira ta kai matsayi mafi ƙarfi cikin watanni takwas a kasuwar canji ta hukuma, yayin da jarin da ƙasashen waje ke zubawa a Kasuwar Hannun Jari ta Nijeriya ya ƙaru daga kashi 4 a tsakiyar 2023 zuwa kashi 16 a ƙarshen 2024.”
Ministan ya kuma bayyana cewa a shekarar 2024, Nijeriya ta zama ƙasa mafi jan hankalin masu zuba jari a ɓangaren man fetur da iskar gas a nahiyar Afrika, inda aka samu sama da dala biliyan 5.
Idris ya bayyana shekarar 2025 a matsayin shekara ta cigaba da gina nasarorin da aka samu a cikin wa’adin farko na mulkin Tinubu.
Ya ce za a gudanar da tarukan ministoci a duk mako na tsawon watanni uku masu zuwa domin tattauna nasarorin da aka samu a fannoni daban-daban.
Ya ce: “A cikin watanni uku masu zuwa, yayin da muke gab da cika shekaru biyu na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za mu kawo ministoci zuwa wannan dandali a kowanne mako.
“Shekarar 2025 ita ce shekara ta ƙarfafa nasarorin da muka samu a cikin watanni 19 na farko na wannan gwamnati.
“Wannan zaman farko na 2025 dama ce ta tunatar da mu waɗannan nasarori da kuma tabbatar da irin cigaban da ake samu yayin da muke shirin shiga rabin wa’adin mulkin nan.”
কীওয়ার্ড: nasarorin da
এছাড়াও পড়ুন:
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi.
Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar.
Kowace kasa tana da cikakken iko da ’yancin zabar manufofi da matakan da ya dace da ita. Da Sin ta tsaya kai da fata cewa ba za ta ba da kai a yakin haraji da Amurka ta tayar ba, hakan ya sa Amurka yin karatun ta nutsu, kuma ta tuntubi bangaren Sin domin tattaunawa.
Wadannan misalai sun nuna mana cewa, akwai hanyoyi masu sauki da inganci na samun maslaha, kuma shawarwarin da Sin take gabatarwa, su ne suka dace da yanayin duniya a yanzu. Ba dole sai kowa ya samu abun da yake so ba, amma hawa teburin sulhu da tuntubar juna tana taka muhimmiyar rawa wajen warware sabani, da lalubo inda kowane bangare zai iya saki, domin a samu mafitar da za ta karbu ga kowa. Kuma irin wannan din, shi ne burin sabuwar Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar a baya bayan nan. Duniya ba ta bukatar mayar da hannu agogo baya ta hanyar tayar da rikice-rikice da danniya da nuna fin karfi, zamani ya sauya kuma dole salon tafiyar da harkoki ya sauya, domin dacewa da yanayin da ake ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp