HausaTv:
2025-07-31@10:19:51 GMT

Sharhin Bayan Labarai :Traump Yana Bawa Iran Zabi Nukliya Ko Yaki

Published: 11th, February 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta.

///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda ta fermata da yaki.

A maganarsa dai shugaban yana son nuna diblomasiyya da kuma lallashi ne ga kasar Amurka ta amince da yarjeniya wacce zata daina mu’amala da sinadarin Uranium kwata-kwata, a sannan zata zauna lafiya da Amurka, amma kuma ra rusa diblomasiyyarsa da, kara takuarawa Iran da sabbin takunkuman tattalin arziki, da kuma baranar kara wasu takunkuman tattalin arziki, ko kuma idan duk wadannan sun kasa shawo kan iran ta zai bude wuta a kan cibiyoyin nukliyar kasar ta Iran ne.

Wannan matsayin da shugaban kasar Iran ya bayyana ba matsayi ne na diblomasiyya ba, sai dai barazana ce, na cewa JMI bata da zabi inda banda wanda Amurka ta bada, wato ko ki yarda ki tadakar da shirin na nukliya kwata-kwata!, ki daina mu’amala da makashin nukliya, ko kuma mu farmaki da yaki. Dole ne ta zama daya daga cikin zabin da Amurka ta bata.

Sai dai bayan wannan furushin na shugaba Trump. Iran ta shigar da korafin a gaban kwamitin tsaro na MDD. Inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar kan al-amuran sharia da kuma kasa da kasa, Kazem Gharibabadi , ya bada sanarwan cewa JMI zata shigar da korafi a gaban kwamitin tsaro na MDD. Kan cewa gwamnatin Amurka ta yi barazanar fermata da yaki.

Yaze wannan barazanar ta sabawa dokokin kasa da kasa, wace ta bawa ko wace kasa yencin kai da kuma zabin abubuwan da zata yi da wadanda basa son yin.

Shugaban Trump dai ya dade yana wannan barazanar kafin ya shiga fadar white house karo na biyu, sannan wannan ba shine karon farko da yake wannan barazanar ba. Sai dai a wannan karon ya fito karara ya bayyana shi.

Kafin haka dai su jami’an gwamnatin JMI sun yi ta sabani a tsakaninsu kan ya zauna da Amurka ne don a zauna lafiya da ita ko kuma me za’a yi?.

Amma a makon da ya gabata wato a ranar larabann da ta gabata Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya fito fili ya bayyana matsayin JMI kan wannan al-amarin wanda kuma shi ne, Iran ba zata shiga tattauna da da Amurka tare da dalilai, kwarara.

Na farko shi wannan Trump din shi ne ya fidda Amurka daga yarjenioyar JCPOA tsakanin Iran da manya manyan kasashen duniya shida. Bayan tattaunawa na shekaru kimani 2. Sannan sauran suka saba wa alkawalin da suka dawkawwa Iran a JCPOA.

Wani tattanawa kuma za’a yi da shi. Bayan da takunkuman tattalin arzikinsa suna dabaibaye da kasar Iran. Don haka ya kammala da cewa mai hankali, da kuma wanda yake son mutuncinsa, har ‘iala yau wanda baya son daukar kaskasci ba zai amince da hakan ba, Don haka Iran ba zata yi tattaunawa da wani da cikin wadannan kasashen yamma ba.

Wannan ya sa dukkan mutanen kasar Iran yan siyasa da sauran mutane suka dawo kan ra’ayin jagoran.

Don haka a halin yanzu sai mu jira mu gani me Trump zai yi bayan wannan matsaya mai karfai .

Banda haka jagoram ya bayyana cewa idan Amurka ta yi barazana , zasu yi mata barazana idan ka kawowa Iramn hari zata rama.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa

Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa kyale HKI wanda kasashen duniya suka yi ne, ya ke bawa HKI karfin giwan ci gaba da abinda take yi a gaza.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin kasar ta Iran yana fadar haka a taron shuwagabannin majalisun dokokin wanda ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Geneva.

Wannan dai shi ne taron shuwagabannin majalusun dokoki na duniya karo na 6 wanda MDD take daukar nauyinta.

Dangane da hare-haren da HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran a cikin watan Yunin da ya gabata kuma ,Qalibof ya bayyana cewa manufarsu it ce lalata shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, kwata-kwata. Alhali hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA tana sanya iado a kan ayyukan sarrafa uranium da kasar take yi.

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa hare-haren kwanaki 12 wanda wadan nan kasashe biyu wadanda basa son zaman lafiya a Iran sun kai mutane kimani 1100 ga shahada. Sannan sun sanya shirin nukliyar kasar Iran cikin hatsari, wanda ya tilasta mana daukar matakai don kare shi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025  Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025  Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka July 30, 2025 Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu July 30, 2025 Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu July 30, 2025 MDD Zata Aiwatar Da Hanyar Warware Rikicin Falasdinawa Da Yahudawan Sahayoniyya July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa
  • Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
  • Shugabannin Arewa Sun Tattauna Sabon Hanyar Ci Gaba – Minista Uba Maigari Ya Yaba
  • Manjo Janar Musawi: Ko Kadan Ba Mu Yarda Da Amurka Ba
  • Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba  Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta
  • Hamas: HKI Da Amurka Sun Janye Daga Tattaunawa Ne Don Sake Damarar Yaki
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan
  • Shugaban Kasar Masar Ya Roki Trump Ya Kawo Karshen Yaki A Gaza