Kare Tsaron Kasa Ko Yunkurin Dankwafe Ci Gaban Duniya?
Published: 11th, February 2025 GMT
Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci gaba, kuma al’umma sun kasance cikin walwala.
এছাড়াও পড়ুন:
Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.
Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai EU ta zartas da matakan mayar da martani kan Amurka a zagaye na farko. Firaministan kasar Japan Ishiba Shigeru kuma ya bayyana a fili cewa, bai shirya mika wuya don cimma yarjejeniya kan harajin kwastam cikin hanzari ba.
Yanayin rudani da Amurka ke ciki cikin kwanaki 100 da suka gabata ya ilmantar da jama’a cewa, babu wanda zai yi danniya bisa ganin dama. Kuma babu wanda zai hana dunkulewar tattalin arzikin duniya. Hadin gwiwa mai kunshe da kowa da samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare, ita ce hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp