An ce, tsakanin shekarar 2000 zuwa 2023, kasar Sin ta samar da rance da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 43 ga kasashen Afirka, don su raya bangaren samar da wutar lantarki. Kana a shekarun nan, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da dimbin ayyukan samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka, kamarsu madatsar ruwa ta Souapiti ta kasar Guinea, da madatsar ruwa ta Djibloho dake kasar Guinea Bissau, da dai sauransu.

Gaba daya an gudanar da ayyukan a kasashe da yankuna fiye da 40 na nahiyar, wadanda suka kara samar da wutar lantarki na kilowatt miliyan 120, da karin layin wutar lantarki mai tsawon kilomita dubu 66. Har ila yau, kasar Sin ta sanar da shirin gina wasu manyan ayyukan samar da wutar lantarki ta hanya mai tsbta guda 30 a nahiyar Afirka, cikin shekaru 3 masu zuwa, a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara.

Na biyu shi ne, fasahohin Sin a fannin zamanantarwar bangaren samar da wutar latarki suna da amfani ga kasashen Afirka a kokarinsu na raya kasa.

Kasar Sin ta kafa tsarin samar da wutar lantarki mai tsabta mafi girma a duniya, inda fitattun fasahohi da ta samu suka zamo masu rahusa kuma suka dace da yanayin da kasashen Afirka ke ciki. Kana kamfanonin kasar da suke taka muhimmiyar rawa a duniya a fannin sauya salon samar da makamashi mai tsabta, su ma za su iya taimaka wa kasashen Afirka kafa masana’antun hada injunan samar da wutar lantarki.

Na uku shi ne, Sin da Afirka sun cimma matsaya daya a fannin zamanantar da kasa ta hanya mai tsabta. A wajen taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bara, Sin da Afirka sun daddale yarjeniyoyi a bangarorin kara yin amfani da makamashi da ake sabuntawa a Afirka, da karfafa hadin gwiwar bangarorin samar da sabbin makamashi, da kara kaimi ga zamanantarwar tsarin kula da aikin makamashi na Afirka, da dai sauransu, wadanda suka nuna ra’ayi daya da kasashen Afirka da Sin suka samu a fannin manufar raya kasa. Hakan ya zo daidai da maganar da Cliff Mboya, masani dake aiki a cibiyar nazarin huldar Afirka da Sin ta kasar Ghana, ya fada, wato “Kasar Sin na kokarin daidaita manufofinta don neman dacewa da Ajandar shekarar 2063 da kungiyar kasashen Afirka AU ta gabatar”. (Bello Wang)

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: samar da wutar lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba

Sai dai don neman cimma burinta na “sake mayar da kasar Amurka zakaran gwajin dafi”, kasar Amurka ta sha daukar matakai na dakile ci gaban kasar Sin, ciki har da katse huldar tattalin arziki da ita da ma sanya takunkumai ga kamfanoninta masu ci gaban kimiyya da sauransu, duk da hakan, kasar Sin ta kiyaye bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata, har ma karuwar tattalin arzikinta ta kai kaso 5.2% a cikin watanni tara na farkon bana, lamarin da ya shaida inganci da juriya na tattalin arzikin kasar. A kwanan nan, kasar Sin ta zartas da shawarwarin da aka gabatar game da tsara shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma bisa ga shawarwarin, za a tsara shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15 na kasar. Cikin sama da shekaru 70 da suka wuce, kasar Sin ta yi ta kokarin aiwatar da shirye-shiryen ba tare da kasala ba, ba don neman kalubalantar wata ko maye gurbinta ba, amma don mai da hankali a kan raya kanta da kuma bayar da damammaki na samun ci gaba ga sauran kasashen duniya.

 

Ganawar da aka yi a wannan karo ta kasance ta farko a tsakanin shugabannin kasashen biyu tun bayan da shugaba Trump ya sake hawa karagar mulkin kasar Amurka. Kafin wannan kuma, shugabannin biyu sun taba tattaunawa da juna ta wayar tarho har sau uku, don nuna alkiblar bunkasar huldar kasashensu. Tun bayan watan Mayun da ya gabata, bisa daidaiton da shugabannin biyu suka cimma, tawagogin kasashen biyu sun gudanar da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya har sau biyar. A sabon zagayen shawarwarin da aka gudanar a baya bayan nan a birnin Kuala Lumpur, sassan biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan tattalin arziki da ciniki da ke janyo hankulansu duka, tare da cimma matsaya daya a kan matakan da za a dauka. Lallai ta hanyar yin shawarwari da juna cikin daidaito, sassan biyu sun kai ga karfafa fahimtar juna da amincewa da juna, hakan kuma ya shaida cewa, yin shawarwari da juna ya fi yin gaba da juna, kuma Sin da Amurka suna iya raya kansu tare da tabbatar da ci gabansu na bai daya.

 

Kasancewarsu kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, alhakin da ke rataya a wuyan Sin da Amurka ne su gano hanyar da ta dace ta cudanya da juna. Kasashen biyu za su iya karfafa ginshikin huldarsu da samar da kyakkyawan yanayi na bunkasa kansu, tare da samar da karin tabbas da kwarin gwiwa ga duniya, muddin sun tabbatar da daidaiton da shugabanninsu suka cimma, kuma suka yi hangen nesa tare da nacewa ga yin shawarwari da juna wajen daidaita sabaninsu, da kuma inganta hadin gwiwarsu da mu’amala da juna a kai a kai.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayinmu Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu October 17, 2025 Ra'ayinmu Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai October 10, 2025 Ra'ayinmu Matsalar Ciwon Kwakwalwa A Gidajen Yarin Kasar Nan September 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Zakzaki: Yakin Sudan Yana Kare Maslahar Kasashen Yamma ne Kawai
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai