Wani Sanatan Amurka Ya Taso Shugaban Kasar Tunusiya Gaba Da Tsarin Dimokaradiyyar Kasar
Published: 11th, February 2025 GMT
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar
Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya takunkumi har sai ta dawo kan tsarin dimokiradiyya.
Maganganun Wilson, wanda ya shahara da kare matakan muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma tsantsar kiyayya ga kungiyoyin gwagwarmaya da dukkan gwamnatocin Larabawa da na Musulunci da suka ki amincewa da Shirin daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ya fuskanci mayar da martani mai yawa a tsakanin ‘yan siyasar Tunisiya da masu fafutuka kare hakkokin dan Adama, wadanda suka soki kalamansa, ciki har da ‘yar majalisar dokokin Tunisiya, Fatima Al-Mas’di wacce ta bukaci ya nemi afuwar al’ummar Tunusiya.
Fatima ta jaddada cewa: Shugaban kasar Tunusiya yana wakiltar al’ummar kasarsa ne tare da cikakken wakilcin jama’a.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, manufar tana cike da shirin aiwatar da sauyin yanayi, wanda ke fassara kudirin siyasar gwamnati zuwa tsarin aiwatarwa a aikace.
Ya kuma yi tsokaci kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na samar da makamashi ta hasken rana da ababen more rayuwa.
Gwamnan ya nanata shirin gwamnatin sa na dasa itatuwa miliyan 5 a shekarar 2025 domin rage zaizaiyar kasa, da inganta iskan shaka, da inganta kyawawan birane.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO